Ƙagaggun labarai na ɗaya daga cikin rukunin adabin Hausawa na zamani, da masana adabin Hausa suka bayyana shi da “zube”, wanda shi ne na farko a cikin rukunin, kafin waƙa da wasan kwaikwayo su zo (Yahaya da wasu, 1992).
Shi ƙagaggen labari cike yake da zantukan hira da nishaɗi, wanda ba da gaske ya taɓa faruwa ba, saboda ana samar da shi ne kawai don nishaɗantarwa (Mukhtar, 2002).
To amma dangane da tarihin samuwar ƙagaggun labarai na Hausa kuwa, yana da muhimmanci a fahinci mene ne rubutun zube, domin fahintar ma’anar ita ce ginshiƙin samar da tarihin samuwar rubutun zuben.
Ma’anar rubutun zube
Masana Adabin Hausa da al’adun Hausawa da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ra’ayinsu dangane da abin da suka fahimta game da ma’anar zube.
Dangane da haka ne Magaji (1982) a wata takarda da ya gabatar mai suna ‘Tasirin adabin baka a cikin Ƙagaggun labarai’, inda yake cewa, “Zube rubutun labari ne da mawallafi ya shirya da kah, sannan ya rubuta shi a zube”.
Mukhtar (1985) shi kuma a cikin wata ƙasida mai suna ‘Yanayin Ƙagaggun labarai na Hausa’ ya ce “Zube wani irin zance ne wanda ake faɗansa da baka ko kuma a rubuce wanda yake bayyana yiwuwar wata al’amari, wanda zai iya faruwa a zahiri, amma bai faru ba, ko kuma ba zai taɓa faruwa ba”.
Mukhtar (2002) kuma cewa ya yi “Zube na nufin rubutun da ba waƙa ba, ba kuma wasan kwaikwayo ba. Idan an ce Zube ana nufin tsagwaron rubutu ne kai tsaye wanda aka yi shi cikin shafi ko shafuka da sakin tayi daban-daban, a rubuce ko a maganance, wato ta hanyar magana.”
Shi kuma Sheihin Malamin nan Ibrahim Yaro Yahya, a wata ƙasida mai take ‘Ƙagaggun labaran Hausa” ya ce “Zube ƙagaggun labarai ne wanda ake shiryawa a kan waɗansu sharruɗa don bai wa jama’a abin samun hira da nishaɗi”.
Shi kuma ‘Yar Adu’a (1996) a gudumawarsa da ya bayar kan ma’anar zube, cewa ya yi “Zube labari ne da a kan shirya cikin hikima da fasaha kuma a gudanar da shi don nuna ƙwarewa, wanda ya ƙunshi nuni da shiryawa ga wani abu na alkhairi ko kuma na sharri ko yakan iya zama na gaske ko na ƙarya”.
To idan aka dubi waɗannan bayanai dangane da ma’anar zube zamu fahinci cewa shi zube labari ne da aka shirya shi da kah kuma a zube don samun abin hira.
Tarihin samuwar rubutun zube na Hausa
Dangane da tarihin samuwar ƙagaggun labarai a Hausa, Mukhtar, (2002) cewa ya yi zube na Hausa ya samo asali ne ta hanyoyi guda biyu:
- Ta hanyar addini wato rubutun zube ta hanyar Ajami, wato hanyar rubuta Hausa cikin haruffa na Larabci
- Ta hanyar rubutun boko, wato ta amfani ba baƙaƙen abacada
Rubutun Ajami
Wannan hanya Hausawa ne suka ƙirƙiro abarsu tun asali ta hanyar rubuta sunaye na gargajiya a jikin fahami. Ta irin wannan hanya kuma manya-manyan malamai da manyan sarakuna sukan rubuta wasiƙu a tsakaninsu. Amma dangane da samun ƙagaggun labarai ciki, bincike ya nuna cewa an fi samun rubuce-rubucen Ajami na zube a cikin hanyar rubutun Magaribi, wato ba a faye samun rubutun Ajami da yawa a cikin rubutu na sharkiyya ba.
Irin rubuce-rubucen da aka samu cikin ajami tun wajen karni na 17 su ne irin rubuce-rubucen Malam Abdullahi Suka Kano da Wali Ɗanmasani a cikin Birnin Katsina da Malam Muhammadu na Birnin Gwari da dai sauransu. Amma dangane da ilmin Arabiya da samuwar Musulunci wannan tun wajen ƙarni na 9 ne, domin akwai alaƙa tsakanin ƙasashen Hausa da na Larabawa tun a wannan ƙarni. Har kwanan gobe Malaman zaure na ƙasar Hausa idan za su yi rubutu na zube a cikin rubutun Ajami suke ƙaddamar da shi. Haka kuma akwai jaridu da akan buga a cikin ajami kamar su: Albishir da Alfijir. Da sauransu.
Samuwar rubutun boko
Rubutun boko yana ɗaya daga cikin ire-iren rubutu na duniya da aka rattaba tsare-tsarensu, da wuraren da ake sarrafa su.
Rubutun boko baƙaƙe ne da wasula a jere, waɗanda suka samo asali daga rubutun Latin. Kusan duk mutane ƙasashen turai kamar Ingila da Faranshi da Jamus da Portugal da sauransu, irin wannan hanyar rubutun suke sarrafawa a cikin dukkan makarantunsu da littattafansu da harkokinsu na sadarwa (Yahya, 1988:72)
Samun labarai na wanzuwar wata sabuwar duniya a bangaren Afirika ya sa Turawa musammam na Portigal da na Jamus da na Faranshi da na Ingila sun tashi tsaye wajen nemo gano yanayin ciki da wajen Afirika. A cikin tafiye-tafiyen nasu wasunsu sun ziyarci garuruwan ƙasashen Hausa kamar su Kano da Sakkwato, sun kuma rubuta labarin rayuwar mutanensu.
To amma dangane da tarihin samuwarsa kuma Mukhtar, (2002) ke cewa
“Rubutun boko bai jima da zuwa ƙasar Hausa ba in aka kwatanta shi da rubutun ajami. Kafin a fara rubutu da Hausar boko a ƙasar Hausa, sai da aka daɗe ana amfani da ita a ƙasashen Turai. Amma mutumin da ake jin ya fara amfani da ita shi ne wani Baturen ƙasar Jamus mai suna James Frederick Schon wanda ya zo ƙasar Saliyo aikin Mishan a 1840. ya yi tunani ya kuma ƙirƙiro cewa ya kamata ya yi amfani da haruffan Latiniyya ya rubuta lafazin Hausa:
Inda yake cewa cikin waƙa kamar haka:
“na riya waɗannan ƙa’idojin rubutu
a raina ne, bayan na yi shekaru ina
lura da abubuwa. Saboda haka na
yi amanna da dacewarsu”
(Schon, 1862).
Bayan da Schon ya yi niyyar amfani da haruffan Latiniyya ya rubuta Hausa, sai wani Bature mai suna Lepsius, ya ba shi shawarwari a kan yadda zai kyautata rubutun. An kuma sami Turawa waɗanda suka biyo irin wannan hanyar rubutu ta J.F. Schon kamar:
- Prietzer a (1904),
- Mischlich a (1906)
- Westermann a (1911) da sauran waɗanda suka biyo baya.
Mukhtar (2002) ya ƙara da cewa, bayan wannan hanyar kuma “wata hanyar rubutu cikin boko da aka fito da ita, ita ce wadda Robinson (1896) ya fito da ita, kodayake Robinson shi ma Latinanci ya yi amfani da shi, sai dai shi ya ɗauki tsarin Ajami ne wajen sarrafa baƙaƙen da babu su a wasu harsuna. Misali /ɓ/ da /ƙ/ da /ɗ/ da sauransu, a hanyar rubutu ta Robinson waɗannan haruffan ɗigo ake musu a ƙasa irin na Ajami maimakon Ianƙwasa. Wato sai a rubuta su kamar baka:- b k d ba tare da tanƙwasa ba.
A lokaci na farko da hukuma ta tsoma baki a kan rubutun zube shi ne lokacin mulkin mallaka a nan Nijeriya inda Hanns Vischer wanda ake ƙira Ɗan Hausa ya tsara ƙa’idojin yadda za a yi amfani da Hausar boko a (1910) sai dai shi ma ya yi amfani ne da hanyar Robinson inda yake sa ɗigo a ƙarƙashin harafi mai alhamza.
Wata hanyar rubutun zube kuma ita ce wadda Bargery (I934) ya yi amfani da ita; shi kuma waƙafi ya dinga sa wa hamzatattun haruffa a maimakon ɗigo. Kamar baka:-
‘b k’ ‘d
Hukumar Fassara ta Jihar Arewa ita ce ta fara ba da shawara a (1938) cewa ya kamata duk hamzatattun baƙaƙe a dinga lanƙwasa su maimakon ɗigo ko waƙafi. (Yahaya, 1988).
To, tun lokacin da Ɗan Hausa ya yi wannan ƙoƙari ba a sake samun wani yunƙuri ba domin kyautata rubutun na Hausa sai a shekara ta 1955, lokacin da aka kafa ‘Hausa Language Board”, wato Hukumar Harshen Hausa, Sarkin Daura Muhammad Bashar ya nuna wa wannan hukumar gatanci. Ita wannan hukuma ta yi gyare-gyare a littafi mai suna Rules of Hausa spelling, sannan, a ciki ta ba da shawarar cewa lamirin lokaci da kuma lamirin mutum kowanensu yana cin gashin kansa ne wato yana zaman kalma guda ne.
Ba burin wannan makala ba ne ta ci gaba da kawo bayanai a kan yadda ake rubutun Hausa ba, amma kuma zai yi kyau a san yadda aka fara rubutun, don shi ne jigon samuwar ƙagaggun littattafai na Hausa. Don haka a karanta wannan makala inda muka kawo muku bayanin irin gudumawar da Turawan farko suka bayar wajen rubutun littattafan Hausa, musamman rubutun da suka shafi ka’idijin Hausa wanda bayan su ne aka soma samun kagaggun rubutu na zube.