A maƙalar da ta gabata mun kawo muku yadda ake samar da ganɗoki a labari inda muka yi bayani kuma muka kawo misalan irin yadda ake samar da ganɗokin, wato zaƙuwa da son jin cigaban labari. A maƙala yau, za mu tattauna ne a kan yadda ake samar da baɗoki.
Kamar yadda na faɗa tun a waccan maƙalar, baɗoki kishiyar ganɗoki ne. A ganɗoki murna da zaƙuwa makaranci yake yi ya ji abin da zai faru a gaba, amma a baɗoki fargabar da tsoron abin da zai iya faruwar ne suke fusgar manazarcin labarin. Za mu fi fahimtar darasin idan aka bayar da misali, don haka zan sake buɗewa da wani misalin a cikin labarina Kukan Jini.
Kukan Jini
A cikin jerin irin ni’imtattun ranakun nan ne kyawawa da ke ƙayace da ni’imar daddaɗar iska mai kaɗawa haɗe da wani irin ƙamshin ƙasa mai daɗi, da yake ba a daɗe da fara yayyafi ba aka ɗauke. Sai dai duk da haka garin akwai alamar hadarin da ke nuni da za’a iya yin ruwa a kowanne lokaci.
Yamma ta fara yi wajen misalin ƙarfe huɗu da rabi zuwa biyar, har na fara harhaɗa kayana da niyyar na rufe shagon nawa na tafi gida, don kuwa na san tunda har hadarin nan ya taso ba zai bar mutane su sake da garin ba. Ba lallai ba ne ma a ƙara yin ciniki, duba da yadda jama’a sai ficewa suke yi daga cikin kasuwar cikin sauri-sauri, kowa ƙoƙari yake yi ya isa gida kada ruwan nan ya tare shi a waje.
A daidai lokacin ne kuma ta shigo mini cikin rumfar shago da gudu-gudu cikin alamar ruɗu da firgici kamar wata wacce ta ga mutuwa, haka kuma cikin ƙarfin hali ba tare da jiran komai ko neman izinina ba ta shige can cikin shagon tana magana mai gauraye da haki.
“Malam don Allah ka rufa mini asiri ka taimaka mini.” Tuni kuma ta samu bayan wata ƙatuwar akwati cikin tarin akwatunan sayarwar da ke shagon ta ɓuya ba tare da jiran abin da zan ce ba.
Gabaɗaya sai ta ba ni mamaki ta kuma ɗaure mini kai, lokaci guda kuma zuciyata ta fara ɗarsa mini lallai ba ta da gaskiya, don haka ne na buɗi baki zan yi mata magana amma ganin taron wasu ƙartin da suka ci burki a ƙofar shagon nawa suna wani haki da waige-waige ya hana ni, don kuwa zuciyata tana raya mini ita suka biyo, kuma ga dukkan alamu idan har suka kama ta ba za ta ji da daɗi ba. To amma kuma me zai sa su biyo ta? Don kuwa kwata-kwata ba ta yi mini kama da mara gaskiya ba.
Daga inda nake a tsaye ina iya jin muryar ɗaya cikin su yana tambayar mutum biyun da suka riga shi zuwa wurin.
“Ina ta yi? Kun gan ta kuwa?” Wanda aka tambaya ɗin ya ba shi amsa.
“Wallahi ba mu gan ta ba, amma na tabbata wani shagon ta shiga a nan. Don haka yana da kyau mu duba sosai.” Ƙarƙare kalaman nasa sai ya sa na ji gabana yana faɗuwa sai ka ce wanda shi za’a kama, ni da ko laifin da ta yi musu ma ban sani ba. Na yi saurin mayar da fitilun idanuwana cikin shagon, watak’ila kuma hakan yana da nasaba da son ƙara gani ko ta samu kyakkyawar maɓoya inda ba za a gan ta ba kada ta jaza mini masifa.
Aikuwa ina juyawa muka yi ido biyu da ragowar gefen gyalenta da bai gama ɓuya ba, na san duk wanda ya nufo shagon tun daga nesa zai iya hango ta. Don haka ne na sake juyawa wajen ƙartin don ganin ko sun wuce, sanadin da ya sa na ji gabana ya sake faɗuwa sakamakon gani da na yi biyu cikin su sun nufo shagon nawa gabaɗaya.
Irin yadda ɓarawon da ya bi hanyar da ba ta ɓullewa yake yin mutuwar tsaye, haka ni ma na sanƙare cikin rarraba ido kamar ɗan dokar da aka ba wa cin hanci a cikin mutane. Wanda ya fara yi mini magana wani garjeje ne baƙi firgita maza, cikin wata irin murya ta shi mara daɗi kamar an daki hujajjiyar ganka.
“Malam ba ka ga wata ‘yar iskar yarinya ba da wani farin gyale a jikinta, mun biyo ta kuma muna kyautata zaton wani shagon ta shigo a nan ta ɓuyar mana.” Ya ƙare zancen yana mai gwararo mini jajayen idanuwan shi masu kama da na soja a filin daga…”
A lokacin da mai karatu ya zo ƙarshen wannan shafi, cike da fargaba ko tunanin “Anya kuwa ƙartin ba za su ga yarinyar ba tunda dai ta bar gefen gyalenta a waje? Ko kuwa ba za su gan ta ba? Idan sun gan ta to me za su yi mata kenan da suka biyo ta da gudu haka? Shin me ma ta yi musu?” Zai buɗe shafin gaba ne zuciyarsa cike da tarin irin waɗannan tambayoyi na fargaba, waɗanda suke gauraye da sanya zumuɗin jin amsarsu a gaba, to ire-iren wannan salon shi ake kira Baɗoki. A daidai wannan gaɓar kuma muka kawo ƙarshen dabarun gina farkon labari, sai dai kuma kafin mu tafi zuwa gaɓa ta gaba wato dabarun gina doron labari (tsakiya), akwai wasu muhimman gaɓoɓi da muka tsallake waɗanda suke da buƙatar mu yi musu komayya. Ku karanta a wannan maƙala ta gaba.