Da sunan Allah mai rahma mai jinkai
Kwashe tuwo nake a cikin kicin. Idona duk ya yi ja saboda hayaƙi, dan gidan yawa ne, kowa ya hura murhun sa. Amma duk da haka hankalina na can wurin sauraron hirar da Baba Ladi da Baba Gambo suke yi, waɗanda ke ƙarƙashin baranda daga yamma.
Yayin da mahaifiyata Fatima wacce muke kira Innarmu mu ƴaƴanta, take daga na ta kofar ɗakin, itama a ƙarƙashin baranda, amma ita a ɓangaren gabas take, kenan suna kallon juna, wanda na tabbatar itama tana sauraren su.
Suna tattaunawa ne kan bikin wata yarinya a makwabtanmu, na irin mahaukatan saitin da aka danƙara mata, da kayan kicin ɗin da aka yi mata sai da aka maido ma uwar da saura. Gara kuwa da aka soma loda ta sai da aka cika store har ma ya yi kaɗan. Baba Ladi kenan take faɗawa Baba Gambo, Baba Gambo tayi tsaki cikin nuna damuwa.
“Ai wallahi kallo ya bar ni, duk wannan mayataccen tarin ne da ya sani gaba shi ya hanani zuwa dankin nan, amma in Allah ya yarda da ni za’a ranar bikin in je in kashe kwarkwatar ido.”
Tsam Innarmu tayi ta shige ɗaki, nima na kammala kwashe tuwon cikin wata babbar cooler na kai ɗaki na komo na ɗauke tukunyar miyar na aje a kofar ɗakinmu.
A ɗaki na samu Innarmu tana zaune kan ƙaramin gadonta na katako ta dora kanta jikin gadonta, ganin har na zauna bata ɗago ba ballantana tayi min sannu da sanya albarkar da ta saba a duk sanda aka yi mata abinda ya faranta mata, na san abinda ke damunta dan haka sai na ƙara matsawa kusa da ita
“Innarmu,” Na kira sunanta.
Firgigit ta yi alamar tayi nisa cikin tunani.
“Me ya same ki? ” Na tambaye ta shiru tayi na cigaba. “Innarmu kwanan nan, kin tsangwami kanki, tun randa su Baba Ramu suke hirar auren Jamilar Alh Babajo har suke cewa wasu sai dai aukin tara ƴaƴa mata, amma ba a da zuciyar da za a huce takaicin kai masu kayan ɗaki. Tun daga nan kika rasa walwalarki. Na sani auren Anty Ummu kike tunani, wanda ko shi mijin naga ai yasan halin da muke ciki, har kuma ɗakin nan ya zo ya ce kar ki damu kanki, abinda Allah ya hore shi za’a kai mata, kuma arzikin bawa ai yana goshin sa Malamin mu ma ce mana yayi duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa sai ki ga abinda ba’a zata ba, ƙofofin Allah ai yawa gare su.”
Zuba min ido tayi ganin yarinya ƴar shekara sha biyar ce da wannan zurfin tunanin, duba na tayi sosai sannan ta ce duk na sani Shuhaina abinda ke damuna duka yau saura kwana ashirin da hudu bikin nan ga gonar mahaifinku wacce kuka ci gado na ce a sata a kasuwa amma dillalan sun ƙi mata sayen daraja, kuɗin su ɗan yi auki, dan nufina a raba kuɗin biyu ayi mata hidima da rabi rabin sai a adana maki a banki tunda ke ma idan muna da rai kwana nawa ne?”
Jin ban amsa ba yasa ta gane kunya nake ji ta cigaba “Wannan yarinyar jiya da ta zo har kuka tayi dan mijin nata shi ma sai jiya aka sako shi na yarinyar da ya bige a hanyar kafancan, dubu goma ta kawo tana kuka wai yaci ace ita ce komai a bikin kannenta amma ji abinda ta kawo, da kyar na taushe ta na nuna mata komai nufi ne na Allah, ga matsalar mutanen gidan nan abu bai samunka a tausaya maka sai dai ayi tayi da kai.”
Na ce “Ki yi hakuri Innarmu wannan kuma sha’anin yawa ne.”
Yusuf wanda ya dade tsaye a bakin kofa yana sauraronsu ya ƙaraso ya zauna yana cewa; “Haba Innarmu a yanda na sanki da juriya da tawakkali me zai sa ki tada hankalinki kina raunana zuciyarki abu ya ya yi ta damunki ban jin dadin ganinki a yan kwanakin nan kina cikin kunci, nima zubi nake ba’a bani kwasata ba, nayi niyyar sai dai in je in ce ma yayarmu ta fito mu je mu sawo ma Ummu kaya,
a yan kwanakin nan duk aikin karfin da na samu hadawa nake da shi kafin in je wurin aikin walda ta har taɓa ka lashe nake karɓa na mashin.”
Ya sa hannu a aljihu ya fiddo Kuɗi ya ba Innarmu.
“Wannan na ƴan ayyukan da nake yi ne, su na zubin idan aka bani sai mu san abin yi ina son ganin walwalarki Innarmu ki aurar da Ummunki ki kai mata komai kamar sauran yaya.”
Dan murmushi ta yi.
Allah ya yi maku albarka dukkanku.”
Yusuf ya ce “Yawwa Innarmu.”
Ta ce. “Ga uwata itama shiru ko duriyarta an rabu da ji.
Ya ce; “Kai na mance Innarmu in faɗa maki jiya da daddare ta kira ni har ta nemi in kawo maki wayar na ce mata dare ya yi nisa har nake faɗa mata bikin Ummu ta ce mijinta ya kammala karatun shi dama ita yake jira ta karasa nata, sannan tana ganin kafin ma bikin za su dawo.’
Wani tsalle nayi na jin dadi wanda har sai da Yusuf ya dube ni.
“Ke fa Malama lafiya? Meye haka?
Na ce “Yaya Yusuf murna ce fa rabon da in ga Anty Amina tun Ina shekara goma koma zan gane ta?.
Ya harare ni kar ma ki gane ta tunda sanda ta tafi ke ɗin jaririya ce.”
Dariya nayi.
Innarmu kuwa ba ka cewa ta ji dadin labarin da aka bata, na san ta hadiye murnar ta ne a cikin ta, dan ita ɗin me bar ma Allah komai ce.
Yusuf ya dube ni.
“Me kika dafa mana ne? “
Bai ko sauke numfashi ba, na ce; “Tuwon shinkafa miyar kubewa danya.”
Bata fuska ya yi.
“Yanzu da ranar nan?
Na ce, “To komai na mu ya kare ita kenan shinkafar ta rage, kuɗin cefanen da ka bayar kuma na sawo kubewa ɗanya da kayan miya.”
Ciro kuɗi ya yi a cikin aljihun shi.
“Amshi ki sawo taliya ki dafa mana da yamma. Akwai wani aikin ginin da muka yi ranar lahadi mutumin bai biya ni ba idan ya bani sai in sawo kayan abincin.”
Ba mu ankara ba sai dai muka ga Innarmu tana share hawaye. Mun san bai wuce mahaifinmu ta tuna ba, sai muka yi tsit! Sai da ta natsa.
Yusuf ya ce, “Ina Ummun ne?”
Na ce “Tana gidan Hajiya, aikowa tayi kiranta.”
Ya ce “Zubo min tuwon nan in ci in kama kaina.”
Sai da na zuba masa sannan na dawo na zauna.
Matar Baba Auwalu tayi sallama ta shigo, Baba Auwalun abokan wasa suke da babana. Ta zauna dai dai Yusuf na cewa,
“Gaskiya randa kika yi aure kika tafi za mu yi kewar girkin nan naki me dadi ga shi tafiyarki tana nufin innarmu ce za ta ci gaba da girki wanda ni bana son tana wahala.”
Matar Baba Auwalu Gwoggo saratu ta ce,
“To kai kuma sanda za ta tafi ai surukarmu tana shirin isowa ko?”
Sosa kanshi ya yi.
“Ai ni Gwoggo ko zan yi aure sai na aurar da salma.”
Baki ta rike.
“Salmar me shekara goma za ka tsaya jira?”
Ya ce “To idan ban kauda ta ba, abin ne na talaka sai a hankali”.
Ta yi murmushi.
“To Yusuf ubangiji ya rufa asiri, ya cigaba da ba ka wuyan daukar nauyin mahaifiyarka da yan’uwanka,
ya ba ka mata ta gari wacce za ta rika kara maka kwarin gwiwa ta soka kai da yan’uwanka.”
Sosa keyar shi yake har ya fice.
Innarmu ma duk da daɗin da addu’ar tayi mata a fuskarta ba ta ce komai ba.
*****
Da safe misalin karfe bakwai da rabi, kari muke da kokon dana dama mana.
Kasantuwar yau ɗin lahadi ne babu makarantar Boko duk dai (Exam) muke an kusa hutu da yake je ka ka dawo nake yi a (Government Day senior secondary school malumfashi) Ina aji hudu ss 1 bamu da islamiya yaron me makarantar ya rasu.
Daga kofar dakinmu aka yi sallama. Baba sani ne kanen mahaifinmu, shi ma cikin gidan yake zaune.
Ya shigo bayan an amsa masa sallamar.
Kan kafet din dake malale a dakin ya yi nufin zama kasantuwar ba kujera, amma tuni na dauko masa pillow a uwar ɗaka ya ce;
“A’a malama shuhaina ba’aje makarantar bane?”
Na ce “Eh”
Na ba shi labarin abinda ya hanani muka gaishe shi, suka gaisa da Innarmu, Ya dubi Innarmu.
“Zuwa na yi inji na ki shirye shiryen game da bikin nan, dan abin na ta matsowa.”
Ta ce “Dama maganar gonar nan ce da na gaya maka, kuma har yanzun dai ba’a samu masu sayenta ba da daraja.”
Dafe kansa ya yi ya yi shiru na dan wani lokaci. Kafin ya dago.
“Allah ya rufa mana asiri ya raba mu da babu.”
Ta ce “Amin Ta gyara zama.
“Ba na so a sai da gonar nan amma tun da nake ta bige bigen in ga nawa zan samu in hada da sadakinta Wallahi da ƙyar na kulla dubu ashirin.”
Ya fiddo su ya miƙa mata, ta sa hannu ta amsa tare da godiya me yawa. Wasu ya kuma fiddowa wannan sadakinta ne da na jin magana da suka kawo, na so barin su wajena ko zan samu in kulla in yi mata saitin kamar kowace ya, amma abin ya faskara. Su kuma sauran yan’uwana Ina yi masu magana, to Auwalu ne dai ya bani dubu biyar.”
Ya miko ta ita ma ya karasa maganar tare da damuwa me yawa akan fuskar shi.
Ta ce “Babu komai Baban yara ai kana iya kokarinka Ina laifin wanda ya tsaya maka akan al’amarinka? Koma bai baka komai ba, adduata agareka ita ce Ubangiji ya saka maka da mafificin alheri, ya ba ka ladan zumunci ya raya zuriarka yasa masu albarka.
Wannan yarinyar ma ta kawo dubu goma shekaranjiya.
Ya ce Wai Azima?
Ta daga kai,
Ya ce Allah ya saka mata da alheri.
Ta cigaba Inna ma ta aiko in je jiya,
buhun shinkafa biyu da buhun gero da na masara ta nuna min, da fridge ta ce inji danta ita kuma ta bani dubu talatin.”
Ya yi murmushi “Ma sha Allahu, in sha Allah asiri zai rufu.”
Itama murmushin ta taya shi
Yusuf ma adashi yake yi shi yake jira a ba shi sai su tafi da yayar ta su su sawo kayan dakin, to ba ka aje komai ba duk dan abinda ka samu ciki ke cinyewa”
Dan murmushi ya kara yi ya yi addua ya fita.
Na umarci kanwata Salma da ta kwashe kayan da muka yi kalaci ta je ta wanke, ni kuma na kama gyara dakin
Cikin lokaci kankani na gyare shi,
dama ba wani tarkace mai yawa a cikin shi.
Falonmu kafet ne dan ubansu me tsada,
wanda Hajiya kanwar kakarmu,
wadda
ta haifi innarmu ta bata da yake ya hadu da masu tsafta kullun cikin tsaftace shi muke
Sai keken dinki da innarmu ke yi shi ɗin ma hajiyar ce ta saya mata,
Sai labulayyarmu masu kyau, su ma hjy ce ta bamu.
Uwardaka gado ne me rumfa sai fameka karami.
Na kunna turaren tsinke.
Zuwa lokacin Yusuf ya dade da fita wurin aikin shi na walda,
Anty ummu ko in ce Amarya kwance take kan karamin gadonmu tayi shiru kome take tunani oho!
Ita innarmu azkar take wanda indai zaka same ta ita kaɗai to baka rabata da hakan,
Ni ma wanka nayi na kwashi kayan wankin innarmu
na fita tsakar gida,
inda mutanen gidan ke ta harkokinsu na yau da kullun.
Wani abin tashin hankalin shi ne, har bikin ya rage saura kwana goma ba’a ba Yusuf adashin sa ba
wanda duk da taurin ransa fidda ƙwalla ya rika yi gaban innarmu.
Ga shi duk tarin yawan mutanen gidanmu dubu goma suka haɗo
Wai gudummawarsu kenan
Dakin kishiyar innarmu waɗanda muke uba daya da su,
Dubu goma mahaifiyar su ta bada ta ce ga na su.
Wanda a dakin na su ma mutum ɗaya ma za ta iya gama komai.
Zuwa lokacin matan gidan suna ta ma innarmu tunin yanzu fa ana saura sati guda ake zuwa danki.
A son Innarmu aje da kuɗin da ke hannu a sawo abinda ya samu,
A cewar ta sandar da ke hannunka ai da ita kake kai jifa,
ba ka da gashin wance ba ka cewa sai ka yi kitson wance.
Amma Yusuf ya kafe.
Sai ana saura kwana takwas innarmu ta nuna matukar bacin ranta
sannan ya hakura da niyyar washegari asabar yayarmu za ta zo sai su tafi su sawo abinda ya samu.
Wayewar garin asabar ko ni ban je makaranta ba, Ina jiran ganin tafiyar su.
Yusuf tuni ya shirya yayarmu kawai yake jira takwas da rabi tayi sallama.
Na ce, “Kai yayarmu kin yi sauri, “
Ta ce “Bayan ma sai da na shirya yara na tura su islamiya, na ce idan an tashi su nufi wajen gwoggo (surukarta). Ɓallo dan da ke bayanta nayi.
Yusuf ya ɓata rai.
“Yanzu zama za ki yi, in don ta ni ai da yanzu Ina birni.”
Kallon shi tayi daidai tana zama.
“Ai duk saurinka dai, ka bari in gaida uwata ko?”
Ta shiga gaishe ta tana amsawa cikin nutsuwa.
Nima na gaishe ta Yusuf ma ya gaisheta.
Ta tanbayi Salma da ummu. Innarmu ce ta bata amsa salma na gidan inna can ta kwana ummu ta fita yanzu kasuwa ta nufa wai zata sawo kayan dinki.
Ta idasa maganar tana miƙewa.
“Bari ka gani in yi ƙoƙarin idasa ma mutane ɗinkunansu.”
Yayarmu ta ce Allah kuwa innarmu kafin a fara biki.”
Hayaniyar da muka ji tsakar gidan ya dauka ne yasa mu saurarawa, bamu fahimci meke faruwa ba.
Yusuf ya tashi ya leƙa da sauri ya juyo.
“Wallahi innarmu ga Amina nan.”
A guje yayarmu Azima ta fice.
Madalla. Allah ya ƙara basira.
#haimanraees