Oh! Na ce cikin raina, Allah sarkin dadi in ji barawon zuma, cikin satin da ya gabata, idan an ce zan tsinci kaina cikin farin cikin da na samu kaina yanzu zan ce ah ah, amma da yake Allah babu ruwan shi baya dawwama ka a bakin ciki haka kishiyar shi. Sai ga shi wuni guda ya jefani cikin dadin da nake ji tun da na ke duniya ban taba tsintar kaina cikin sa ba. Motsin Momi da na ji ya katse min tunani, na ce "Innarmu, zan ba." Na shiga yi mata godiya.
Da daddare na je nayi ma. . .