Skip to content
Part 13 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Aunty kubra tana ta fadin rashin jin dadin ta na rashin dawowar Ahmad su hadu, dan rabon ta da kasar tun rasuwar Anty Amina. Ta tafi da kwana biyu ranar ta kama litinin, na gama shirina tsaf cikin kyakykyawar shiga ta abaya kalar ta milk color, gaban ta caccabe da kwalliya, mayafi me kyau na yane jikina da shi, Takalmina flat ina rike da handbag na fito.

Husna da Farhan na samu dan Farhan ya ce sai biyu yake da lactuce Abakar an tafi da su shi da yaran Haj Asmau Anty Amarya. Dan duban su na yi, “Barkanku da hutawa.” A tare suka juyo suka dube ni Husna ta ce “Banda ban yi wanka ba ai da tare muka fita na wuce salon.” Na ce “Ki bari idan na dawo sai mu je. Kai ta daga Farhan ya ce Anty Shuhaina daga kuma samun Anty Husna sai aka wancakalar dani.”

Kallon mamaki nake mishi, “Kai kam akwai daukar dumar magaji da nishi, yaushe aka yi hakan? Husna ta ce ” Kyale shi hala ni din kishiyar ka ce? Na ce ” To yi hakuri tashi mu tafi in za ka.” Ya kada kai “Yi tafiyar ki kallo nake.” Na yi wa Momi
sallama sai na bar gidan. Ko da na isa sai na samu kaina ban san yin komai kasala duk ta rufe ni, sai ina jin faduwar gaba. a daddafe na kare zaman na taho hanyar gida ina ta sake saken ina isa kwanciya kawai zan yi. Na yi sallama kofar Momi na sa kai, abin da na gani ba karamin sani kaduwa ya yi ba, take gabana ya soma bugawa ya amsa sallamar da na yi yana zaune yana cin abinci a dinning ya kara wani irin kyau da gogewa sai annuri ke fitar mishi, na bayyanar yana cikin jin dadi kananan kaya ne a jikin shi da suka yi matukar amsar shi daga idon da nayi a karo na biyu dan in kara tabbatar da shi din nake gani hada ido muka yi ya zare glass din shi ya dube ni, na yi saurin wucewa ciki a dakin wurgar da komai na yi na fada gado rub da ciki na kwanta, sai na samu kaina ina tuna abubuwan da suka shude, tun dawowar Anty daga zuwa rasuwar ta. CANJIN da aka samu na BA ZATA wato aurena da Ahmad da irin zaman da na yi da shi har zuwa tsallake nin da ya yi ya tafi ya bar ni da dan tayin da bai ko san da shi ba, har haihuwata rasuwar yarinyar zuwa yau. Komai na ji ya dawo min sabo wani irin bakin ciki ya lullubeni. Sai na samu kaina ina malalar da hawaye masu zafi. Ban san iya lokacin da na dauka a haka ba sai dai muryar Abakar na ji yana fada min Momi ta ce ya zo ya gani na dawo.” Na ce, Eh ya ce “Ta ce ki fito a ci abinci.” Kai na daga ma shi na tashi zaune ganin ya juya na mike na shiga bathroom wanke fuskata nayi na fito na mutststsuka mai da hoda sai na fito na same su a falon. Momi na yi wa sannu da gida, duk yadda na so daurewa in ci abincin ya ki wuce min ganin Ahmad ya lalata komai sai juice na yi ta banka ma cikina ina lura da Momi hankalinta na kaina, ko da ba ta ce min komai ba.

Da na gaji da zaman mikewa na yi na koma na yi alwala na yi sallah na dade a duk sujjadar da na yi ina neman agajin ubangiji kan kar ya kara maimaita min irin zaman da nayi da Ahmad na rashin yanci da ganin wulakanci. Dan ni dai yanzu na san bani da wani yanci da zan ce bana auren shi in dai ba shi na samu ya ce ba ya yi ba. Har dare ban kara jin motsin shi ba, ba kuma ji wanda naji ya yi maganar shi. Husna dama ban same ta ba sai yamma sosai ta dawo, Sai da aka kirani cin abinci ta lura bani da walwala, Ta dubi Farhan da ke gefenta,

“Wai make damun Antyn namu ne? Tun da na dawo nake ganinta gata nan dai.” Ya noke kafada “Ban san me ke damunta ba, amma kina da labarin dawowar yaya Ahmad a yau?” Ta ce “Abakar ya gaya min sai dai ban gan shi ba.” Ya kada kai “Yana falon Abba sun taram mashi, ni anya na taba ganin Abba yana irin fadan da na ga yana wa yaya Ahmad yau?” Momi dai kwalla kawai take abinda ya kara tada hankalin yaya Ahmad, idan ka dube shi Allah sai ya baka tausayi.” A natse take kallon shi jin ya kai aya ta ce sarkin tsurku, kai wa ya yi kiranka har ka gani?”

Ya bude ido, “Ah ah ba tsurku naje ba Habu direba ya bani key na kai.” ” Sai kuma ka tsaya ganin abinda bai shafeka ba? Bai kara magana ba kujerar shi ya tura baya sai ya mike ya bar wurin. Wayata ta dau tsuwwa na mika hannu na dauko Anty Amarya ce.

Ta ce, “Shuhaina ki zo falon Alh yanzu.” Gabana na ji ya buga, na ce “To” sai na mike doguwar hijabi ta na zura na ce ma Husna ina zuwa ta daga min kai na wuce kamar wacce kwai ya fashe mawa a ciki. Cikin sassanyar murya na yi sallama kusada anty na rabe a kasa Abba ke kan doguwar kujera Haj. Babba na zaune gefensa, Momi na zaune kan kujera me zaman mutum daya Ahmad da na duba sau daya kan shi kasa yake sai zufa yake fitarwa. Ko ni da ake mashi hukuncin domina zuciyata ta risuna. Abba ya ci gaba da magana gargadi yake mashi me zafi da gindaya mashi sharudda a kaina. Daga bisani ya sallami kowa ya rage daga ni sai Ahmad, nasiha ya koma yana ma shi cikin lafazi me taushi. Hankalina ya dawo wajen yana cewa “Ba zaka gane alherin da nake nema maka ba. Shi aure a gida na kwarai ribar shi ba ce, matukar ka rike wannan, to in sha Allah za ka ga cin nasara a rayuwar ka. Ni aka ba na kuma karbar maka ba tare da wani tunani ko shakku ba, duk wanda ya samu mace ta kwarai ya samu rabin addini sai ya nemi rabin, Ina maka kwadayin samun alheri irin wanda na samu na auren matar kwarai irin mahaifiyar ka, ba kai ba ma duk wanda ya sanni ya san ina girmama al’amarinta, bana wasa da duk abinda ya shafe ta, saboda tsatsaon da ta fito gida ne na mutanen kwarai haka gidan da ka dauko wannan yarinya, yar’uwarta har Allah ya amshi abun shi ka taba ganin abun ashsha a tare da ita?”

Sai da ya ji Abba ya yi shiru sannan ya ce, “Na yi kuskure babba Abba, ban duba irin gatan da kuka yi min ba, amma wallahi tun ban dawo ba nadama ta shige ni na shiga bakin cikin abinda na yi ina neman gafararku Abba, tuni nake rokon Allah ya yafe min.” Abba ya shiga shi mana albarka ya kara mana nasiha kafin ya sallame mu. Ahmad bedroom din Momi ya wuce ya dade yana bata hakuri kafin ya fito ya tafi. Da safe da muka tashi, da shi muka tashi duk rokon da ya yi mata ganin bata tanka ma shi ba ya fita limamin da ke jan sallah a masallacin cikin gidan shi kuma ke koya wa yaran gidan karatun addini. Shi ya dauko wa Momi yana fara bata hakuri ta ce, ita ba ita ya yi ma wa ba matar shi zai nema gafara.Ya ce duk da haka ita ma suna neman afuwar ta ta ce ta yafe. Tun da na tashi yau ma haka nan nake raina babu dadi, har Husna ta gaji da bi na da ido, ta ce “Wai Anty Shuhaina har yanzu ba ki hakura ba? Ko ba ki gamsu da karbar yancin da su Abba suka yi maki ba?” Na share hawayen da suka taho min, na ce, “Ba ki fahimce ni ba Husna amma Abba da Momi bani da abin ce masu sai Allah ya yi masu sakayya da mafificin alherin sa, ya karbi rayuwar su cikin imani. Dan tun randa aka daura min aure da Ahmad ba wanda ya nuna min ni ma ya ce me daraja, ba wanda ya dubi rashin adalcin da Ahmad ya yi min, Mahaifiyata tana jin zafin halin da na shiga amma halinta na kawaici da kauda kai da hakuri yasa bata taba cewa komai ba, waanda ya dace su nema min yancin babannina ba su ce komai ba, sai Abba da Momi suka tsaya kai da fata, Sai dai abinda ke sanyaya min jiki yake sani jin tsoro.”

Sai na yi shiru ina share hawaye ta ce, “Ina jin ki”. Na ce “Duk da ba wani uban shekaru gare ni ba na san ba karamin shiga garari bane a ce miji baya san ka sai iyayen shi ne ke san ka ina hange wa kaina wannan matsalar.” Na lura itama jikinta ya yi sanyi ta dan dafani “In sha Allah Allah zai so ki kuma biyayya ki ka yi Allah ba zai wofintar da lamarin ki ba.” Na ce “Na gode Husna Allah ya shige mana gaba.” Ta ce “Amin” sai ta miko min mug wanda ta cika da kunun gyada “To shanye wannan ko fa karyawa ba ki yi ba.” Ta turo min flate din chips da kwai Na kafa kai ina sha tana kara jan hankalina ta hanyar bani labarai “Ke ai Anty ko dan kyakykyawar surar da aka yi maki namiji ya soki ko bai shiryawa yin hakan ba, ballantana ma kina da kyan hali, kin ganni ni ba me sakewa da mutane ba ce, mu’amalar ki tasa dole na kasa share ki muke muamala me dadi, ko momin mu abinda ya ja mata samun matsayi me girma a zuciyar Abbanmu kenan.” Na yi saurin kallonta tare da yarda da abinda ta ce, a zuciyata, dan shima Abban na ji ya fada da kan shi. Ta ce “Yes Abban mu tare suka yi karatun jami’a da Mama (Haj Babba) school mate din shi ce, har suka gama tare suna soyayya, tana yar masu mulki yana dan talakawa duk da kyawun sakamakon da ya fito da shi, bai samu wani babban aiki ba yana karamin ma’aikaci ita kuma yar masu da shi kuma jinin sarauta, kina dai kallon sai a wuni a kwana ba ki ji in da tayi magana ba, in ba ta kama ba, Yan’uwan shi tun suna shaawar zuwa gidan shi har suka daina. Mahaifiyar shi kanta ta zo gidan shi sai dai ta nema wa kanta matsuguni, wannan ma ya rage kimar ta a zuciyar shi daga randa mahaifiyar shi ta ce ta sallama zuwa gidan shi hakan yasa ma shi sha’awar kara aure, amma kuma yana gudun a kara maimaita yar gidan jiya. Kusa da gidan su akwai wani kamilallen malami ko shi ya kan je daukar karatu wurin shi zamanin da yake jami’a da kuma ya fara aiki yana taimaka mashi da addu’a. Yana yawan ganin yaran malamin har dai ya roki ya ba shi daya daga ciki. Ya ce wane ina yaba hankalin ka kuma halayenka halaye ne da ko wane uban kwarai zai so hada zuria da kai, sai dai wani hanzari ba gudu ba ya ta babba a yanzu kwata kwata shekarunta 12 yanzu ta kammala karatun primary din ta. Abba ya ce Allah ya gafarta malam in dai za’a bani ina so,” Ya ce” To abinda za’a yi ka turo malam Ahmad din muyi magana a kawo sadaki rana ita yau in sha Allahu zan daura maku aure da Hadiza a kai maka matar ka.”

Godiya ya shiga yi, an daura auren kamar yanda Malam ya ce daki ya gyara a gidan su aka saka ta, lokacin yana aiki a sokoto Allah ya yi ta me kazar kazar kwata kwata bata da kasala, duk da karancin shekarunta ita take aiwatar da komai na gidan sai dai abinda ya gagareta sai surukar ta ta yi dan tun tana hana ta har ta gaji ta kyaleta. Idan ya tafi sokoto daga bauci sai ya yi wata amma ita ko a jikinta harkar gabanta kawai take yi Allah da ikon sa tana cikin shekara ta biyu ta samu cikin Anty kubra wadda tsakaninta da yaya Ahmad wata ashirin ne da biyu, tana da karamin cikin yaya Ahmad Allah ya karbi ran mahaifin shi. Sai gidan ya zama daga ita sai mahaifiyar shi sai kanan shi saurayi, ta yaye Ahmad ba jimawa maman tashi ma ta rasu. To anan fa ne hankalinta ya tashi ta gudu gidan su ta ce bata kara zama gidan. Dole ya yanke komawa da ita sokoto yana kaita kuma makaranta ya jefata dan ya lura tana da hazaka tana kuma san karatun a zamanta Bauci ta kan tsare kanen shi ka koya min karatu ka ga ni primary kadai na yi, wasa wasa ta samu karatu dan haka ss1 aka saka ta, Yayan ta kuma ya nemi me kula da su. Dan a lokacin ya samu cigaba har motar kan shi ya mallaka, dawowar ta dangin shi suka dawo da zuwa, dan dangi ne da shi masu tarin yawa, duk wanda ya zo tana makaranta sai dai ta dawo ta iske shi tsakar gida daki za ta kai mutum ta ba shi abinci, dam ma bata kara haihuwa ba, su yaran mama kyamar yan kauye suke Momi ce me zuwa mama bata zuwa kauye.” Da haka ta kare sakandire din ta ta cigaba har ta samu Diploma a fannin girke girke duk dan ta burge cikin mijin ta, idan yan’uwan shi sun zo iya abinda take da shi zata zage tayi masu hidima da shi wanda kuma duk ya kawo kukan shi bata samun kwanciyar hankali sai ta ga ya yi masu, wannan ma ya kara mata matsayi me girma wajen Abba. A kaduna ya auri Anty Amarya ita ma diyar masu da shi ce digiri ne da ita a lokacin shi ma kuma sannan ya kama kasa da su ake damawa a gwamnatin tarayya. Tsakani na da yaya Ahmad shekaru goma ne cif! daga ni sai farhan sai auta Abakar. Mama yaranta shida, Yaya Kabir babba sai mata hudu sai autanta Sudais, Anty Amarya yaranta biyar Rufaida ce babba sai Najib sai Ummi sai yan biyun ta mata. Dubana tayi ina fata kin fahimci dalilin ba ki wannan dogon labarin da abinda nake so ki fahimta? Gyada mata kai na yi dana duba flate din gabana sai na ga na ci sama da rabi ji na yi na dan samu nutsuwa Dan haka mikewa nayi in shirya in wuce wurin computer. Ina zuwa falon Momi na samu da Ahmad sha’anin da da uwa fira suke, hoton Amina karama a hannun shi. Na gaida Momi zan wuce ta ce, “Idan ba ki makara ba samo ma shi abin kari.” Da “To” Na amsa na wuce kitchen.

Ji na yi yana fadin, “Da dai ace cikin da Mina ta tafi da shi ta haife shi sai in ce diya ta ce da mina ta haifan min dan tsananin kamar su. Ko dan ban gani ba na san murmushi Momi ta yi, “wannan ma wata Minar taka ce da Shuhaina ta haifa maka.”

<< Canjin Bazata 12Canjin Bazata 14 >>

1 thought on “Canjin Bazata 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×