Shiru na ji har na fito kitchen din. Na jawo tebur na jera kayan abincin na saci kallon shi, ya dafe kanshi da hannayensa, tabe baki na yi na yi wa Momi sallama na wuce. Da daddare ma kasa zama nayi a falon dan yana nan. Kwance nake kan gado idanuwana suna kallon sama daddadan kamshin da ban iya manta mamallakinsa ya daki hancina, lumshe idona na yi ya zauna saitin kafafuwana kara rufe idanuwa nayi gabana na fat fat.
"Na zo ban hakuri ne Shuhaina." Muryar sa ta ratsa dodon kunnena, karo kuma na farko da na ji ya. . .
Dakyau!