Skip to content
Part 14 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Shiru na ji har na fito kitchen din. Na jawo tebur na jera kayan abincin na saci kallon shi, ya dafe kanshi da hannayensa, tabe baki na yi na yi wa Momi sallama na wuce. Da daddare ma kasa zama nayi a falon dan yana nan. Kwance nake kan gado idanuwana suna kallon sama daddadan kamshin da ban iya manta mamallakinsa ya daki hancina, lumshe idona na yi ya zauna saitin kafafuwana kara rufe idanuwa nayi gabana na fat fat.

“Na zo ban hakuri ne Shuhaina.” Muryar sa ta ratsa dodon kunnena, karo kuma na farko da na ji ya ambaci sunana gabana ya tsananta bugawa. “Ki yi hakuri ki yafe min nasan na zalunce ki na kware ki tsawon zamana da ke ban kyauta maki ba, ashe har ciki na tafi na bar ki da shi ki ka yi wahalar shi ke kadai ki ka yi ta haihuwa ki ka dora ta reno, kika dandani zafin rashinta ke kadai ki yafe min.”

Maida hawayen da na ji sun taho min na yi gami da kara kudundunewa. Ya dade yana magiya amma bai samu na ce ko uffan ba. Da safe da ya shigo ya ce ma Momi yana son tafiya da ni bikin Khausar, ta ce ” Idan ta amince sai ku yi ta tafiya da zai fita ya yafito Husna tashi tayi ta bi bayan shi, can sai ga ta ta dawo tana daga min rafa na yan dari biyu na ce, “Iye wa ya baki kudi? ta dan murmusa “Lanbar wayar ki kadai na bayar aka bani.” dai na murmushin da nake na yi na tabe fuska na mike tsam na shige daki, kamar jira ake aka kira wayata bakuwar lamba ce na daga hade da sallama ya amsa “Ranki ya dade roko nake ki zo muje gidan mu ki amshi tsarabar ki.”

Jarumta nayi sosai wurin ce ma shi “Ba sai na je ba ranar da ka samu lokaci ka kawo.” Rage murya ya yi “Haba my baby ki daure mu je.” Ba tare da na amsa ba na kashe wayar, ba’a dauki dogon lokaci ba ya kuma kira kamar in share shi sai na amsa. Rokona yake da magiya in fito yana mota ganina kawai yake son yi. Na ce ma shi to. Kashe wayar nayi gaba daya na haye gado barci kuma ya yi awon gaba da ni. Da daddare ma yana gidan dan haka ban fito falon ba, rike nake da littafin hausa ina karantawa turo kofar dakin aka yi abinda ya sani kai idona kofar, Ahmad ne wanda ya sha kwalliya ta kananan kaya yana ta zabga kamshi, kujerar dressing mirror ya jawo ya zauna.

“Shuhainata kenan ba ko gaisuwa? kara rufe fuskata na yi da littafin ni sai yake bani mamaki kamar ba Ahmad din da na sani ba da wanda ban ishe shi sauraro ba, wata zuciyar ta ce ya gama tsula tsiyar shi yanzu lokacin ki ne. Wayar shi ya ciro magana na ji yana yi, Abakar ya yi sallama kofar dakin da jakunkuna a hannun shi gaban shi ya ajiye, yaron na juyawa ya maida kofa ya rufe, ya fara bude jaka. “Gimbiya tsarabar ki ce na rasa abinda zan sawo maki dan ban san komai naki ba abu daya dai na rike ke din ma’abociyar kamshi ce, dan duk sa’adda na shiga dakin ki zuciyata ta kan nutsu da daddadan kamshin da ke fita a ciki, dan haka na sawo maki turaruka da kayan shafa.”

Turo min ita ya yi ya kuma turo min sauran guda biyu babba da karama. Yau ma haka ya gaji da magiyar in furta ma shi ko kalma daya ne ya gaji ya tafi. Husna ce ta bude jakunkunan ta farko rantsatstsun takalma ne hade da jakunkunan su, sai ta biyu cunkus take da kayan kwalliya da turaruka masu matukar tsada, sai yar karamar sarkoki ne da yan kunnayen su wa’anda ba sai an gaya maka taadi me yawa aka yi wa naira kafin a mallake su. Bayan mun kwanta ma text din shi suka yi ta shigowa yana fada min halin da ya fada na tsananin kaunata, na karshe shi ne yake shaida min zai shigo da safe mu je wajen tela ya gwada ni dunkunan da zan sa a wurin bikin Abdullahi yau ya sayi kayan. Da ya zo kuma nayi mirsisi na ki zuwa gwada dinkin, sai Husna ce ta dauki rigata ta ba shi. A daren bai zo ba sai nayi tunanin ya yi fushi ne, tara da rabi sai ga kiran shi wai ga shi a bakin get in fito mu shirya tafiya wurin bikin, text na tura ma shi ba za ni ba na koma na cigaba da kallona. Da safe bayan mun yi sallar asuba mun yi marajaa komawa nayi na kwanta sai dai na ji Husna na bubbuga ni cikin barci nake tambayar ta meye?

Ta ce “Ba yau za ku tafi ba kika koma kika kwanta? Maida kaina na yi “Sai in ki barci dan yau zamu tafi.” Ban san iya lokacin da na dauka a kwance ba sai dai na ji an yaye bargon da na lullube saurin bude idona na yi tunanina Husna ce, Ahmad ne zaune gefena ya zura min ido saurin kankame jikina nayi saboda rigar barcin da ke jikina ba wata ta kirki ba ce, dan miskilallen murmushi ya saki tare da nuna kamar be san me nayi ba.

“Barcin ya isa haka ki tashi mu wuce.” Dan tura baki nayi na ce, “Ba za ni ba.” Ya ce “Kina so in shigo cikin bargon kenan?” Zumbur na yi na duro na fada bathroom sai da na sa key sai na fara wanka muryar shi na ji jikin kofa “Ga kaya nan ki zabi wanda za ki sa yanzu.” Daga ciki na ce, “Ni fa in ba da Husna ba ba in da za ni.” Ya ce “In hakan kika fi so sai ayi hakan.” Na kara cewa, “Idan ba ka tafi ba ba zan fito ba.” Ya ce “Na tafi” Sai da na tabbatar da tafiyar shi na fito na fara shafa mai ina kallon kayan da ya zube bisa fado, na shiga duba su na rasa wadda zan zaba dan duk sun hade daga karshe na hakura da wata shadda readymade doguwar riga ce ta amsan ba kadan ba na zabi cikin sarkokin da ya kawo min na zabi jaka da takalmi ina daura dankwali ya shigo ta madubi na hango shi yana min kallon kasa kasa, bude jakar da ya kawo min ya yi ya ciro turare yana fesa min ni dai kaina yana kasa ya koma ya kwashe sauran kayan da ke zube a kan gadon ya maida cikin jakar ya rufe ya yi waje da jakar.

Na sami Momi zaune na gaishe ta ta amsa tana cewa “Har an shirya kuma ba’a karya ba?” Ladi cikin masu aikin ta ta fito da tire ta ajiye gabana tea na hada na sha sama sama, Husna ta fito ta sha kwalliya itama ba magana Momi tayi mana fatar dawowa lafiya, muka fito muna taku a hankali, nesa na hangi motar Ahmad yana zaune cikinta yana shan waya, bayan motar muka zauna mu biyu waiwayowa kawai ya yi ya dube ta ta yi saurin fita ta bar motar, bayan ya dawo kusa da ni, “Haba gimbiya ta dawo gaba mana” shiru nayi ina duban fuskar shi da ke nuna damuwa karara, “Dan Allah ki rika min magana wannan shirun ba karamin azabtar da ni kike ba, gara ki rika min magana ko da ba kalmomi masu dadi za ki gaya min ba.”

Yana rufe bakin shi wayar shi ta soma kara a hands free yasa ta muryar me kiran ta fito, “Kai malam mun fa gaji da jiranka ya ce “Ina gaban gimbiya sai ta gama shiryawa.” Ya ce “Yana da kyau amma ka kara minti ashirin sai dai ku taho kai da gimbiyar.”

Daga can ya ce. “kuna iya tafiya” Sannan ya kashe wayar ya koma lallashina in dawo gaba sai da na gama mishi yanga sai na koma ta waya ya kira Husna. Cikin tawagar abokan su muka yi tafiyar Ahmad ke jan motar shi Abdullahi na gefen shi muna baya ni da Husna Yamma likis muka isa, gidan babba ne amma ba masaka tsinke ko ina jama’a ne, rawa ake cashewa. Khausar suka yi ma waya ta ce ta fita amma za ta yi waya a zo a yi mana jagora zuwa ciki daki guda aka bamu hatta da abinci an shirya mana salla muka fara yi sannan muka ci abinci, Mun kammala muka kishingida har Husna tayi barci ni kaina cikin gajiyar nake, san ganin Khausar ya hana ni yin barcin da karfi aka turo kofar “Ina Shuhainar nima cikin jin dadi na tashi zaune na tare ta, hannuna ta kama ta rike yanda na ga ta koma ya sani rike baki, na zuba mata ido a sanin da nayi mata ita din doguwa ce mara jiki sai na ga mata ta ajiye hips da cikar kirki, hure idona ta yi, “Malama kallon fa lafiya? “Ke kin fa bani mamaki kin ga yanda kika koma?”

Ta kada ido “To ba dole ba, aure wasa ne? Na rike baki “Aure? ai ba ki tare ba? Ta yarfe hannu “Ba dai an daura ba? ai nan daf nake da juyewa.” Sai da na ji faduwar gaba jin zancen ta” Ban gane juyewa ba? kina nufin ciki gare ki? Cire wai ana kai ni ban wuce three month.” Kama baki nayi “Ke yanzu Allah ya sanya Alheri za’a ce ko Allah ya raba lafiya?” Kafada ta noke “Duk wanda aka ce ai fata ne” Na jinjina kai “Ashe yayana yasan abinda ya taka shi yasa ya daina wannan giringidishin.”

Ta ce “Da farko bai samu hadin kaina ba sai da ya dage.” “To da ya ji maganar cikin me ya ce?. Me kuwa zai ce dadi hakan ya ma shi Wai hakan ya sa Abba na ya ba shi matar shi.” Na ce “Ko da yake da gaskiyar shi yayan nawa ya zama tuzuru, ina zai iya jira? Ahmad shekarar shi nawa da aure? ko da yake na farko auren gata aka yi ma shi.” Ta rike baki “Wai me Ahmad din ya ba ki dawowar shi kike zaro zance haka? dan ni dai Shuhainar da na sani idan an sa mata hannu a baki ba za ta ciza ba.”

Muka yi dariya ta ce “Yanzu ma Abba na da kyar ya yarda yasa ranar tarewar shi bai san rabuwa da ni, sai da Momi ta ce ka ba shi matar shi in dai ba so kake a haife mana a gida ba.”

Na ce, “Shi daddy bai san yar ta gaji da zama da su ba.” Dariyar muka sake yi daga karshe tashi muka yi ta kaimu muka gaisa da mahaifiyarta. Karfe tara na dare kowa ya gama shiri dan halartar liyafar da abokan ango suka shirya mishi, na hade tsaf cikin wando da riga na wanda ya yi min cif rigar daga sama zuwa ciki ta kama ni sai aka bude ta daga kasa tsawonta iya gwiwa dan haka ta fidda surata, gyalen me yala yala ne wanda zugar Husna na bi na yafa shi in banda haka rufe jikina zan yi sanin zunubin da zan kwasa, wai so take in kara ruda yayanta da na ce mata akwai maza a wurin ba kyau ta ce, “Yau ne kadai ta ma roki Allah ya yafe mana dan ta san hada ita za’a raba zunubin daga ita ta matsa min.”

Dariyar maganar ta nayi. Na ce “Dama wani malamin mu ya ce mace ce in za tayi magana sai ka ji ta ce Allah na tuba memakon tun da ta tuba tayi shiru to maganar da za tayi wadda zata janyo mata zunubin ce.” Sarkar da nayi amfani da ita me kama wuya ce takalmina me tsini ne da jakar shi Husna na tsaye rike da turare tana fesa min na rike hannunta “Bar ni haka in ji da wannan zunubin.”

Ta ce “Duk da yaya Ahmad yake dan’uwana da nake so da girmamawa ya bata min rai kwarai da abinda ya maki dan kin san ciwon ya mace na ya mace ne, kuma ko ni aka yi wa abinda ya yi maki ba zai ji dadi ba.” Ban lalubi amsar bata ba aka kira wayata Ahmad yake gaya min ya so ya zo ya tafi da ni to amma dole ya kasance a wurin dan ganin tsaruwar wajen, amma ya turo a dauke mu, idan mun gama shiryawa. An fara shirye shiryen da za’a yi muna kallon wajen zaune muke ni da Husna muna kallon juna mun sa tebur tsakiya. Ina son kallon ango da amarya amma idon da Ahmad ya tsare ni da shi ya hanani sakewa ya sha duk da uban kwalliyar da ya sha yana daga gefen angon daga hagu amarya na a zama kowannen su ka duba ba’a maganar irin kyan da ya yi, abokan angon yan boko ne masu murza naira. Yammatan amarya masu ji da kan su ne ko wacce ka duba sai shan kamshi take, fira muke kasa kasa tare da kallon abinda ke gudana a wurin, maza biyu suka tsaya kanmu da san yi mana magana Husna ta ce matan aure ne na ukun ne ya fi naci dan da kyar ta samu ya wuce na ce,

“Ai kin ga irinta” Muna cikin haka ango da amarya suka shiga tsakiyar fili. Wurin ya rincabe da jama’a ana masu liki naso zuwa ganin yawan mutanen yasa na saurara, Husna ta ce in bari su yi sauki sai mu je da suka ragu na mike ita kuma tana amsa waya, na ratsa mutane na soma likin kamar jira maza suka rufe ni da liki, gabana na ji yana harbawa na yi wuri wuri ina neman in da zan bi in sulale ina cikin haka ban san yanda aka yi ba sai dai na ji an finciki hannuna ja na ake da karfin tsiya, ban fahimci wanda ke min wannan aikin ba sai da muka fito harabar wurin da ake ajiye motoci wata mota ya bude ya tura ni ciki ya shigo ya zauna kusa da ni, ba sai na fadi irin razanar da na yi ba a takaice ji nayi kamar in saki fitsari a zaune ya dube ni da idanuwan shi da suka canza kala dan bacin rai,

“Ke kin ga dacewar abinda kika yi? wannan shigar ita ce ta dace da matar da ke da igiyar aure a kanta ta fito haka?” Gaba daya hall din kallon ki ake kin san irin zunubin da kika kwasar ma kan ki? Ya finciki yalolon gyalen da na yafa ya murde shi a hannun shi na yi maza na kare kirjina da hannuna biyu, kwafa ya yi me bayyanar da takaicin shi “Bayan kin gama nuna ma kattin banza. Kuka na shiga yi mashi ya ce “Yanzu dai kin gama Fatin bikin ma ban da na Abdullahi ne da gida na wuce da ke dan ba dan iskan da zai kuma ganin ki na ki ki hau high table dan kar a gan ki ashe ban tsira ba, dawo gaba in maida ki gida na ki motsi na ce gyalena.”

Ya ce “Wato ni kadai kike jin kunya sauran duka yan iskan da suka gani ba ki jin kunyar su?” Mantawa ya yi da ni ya danna kira’ar Abba zaria sautin ya rika ratsa cikin motar, kwankwasa glass din motar da ake yasa ya tada kai ya sauke glass, “Lafiya” ya ce da matashin da ke tsaye, tsayuwa ya gyara “Wannan gimbiyar ta bayan motar ka na biyo, dan Allah ina son magana da ita.” “Yi hakuri malam ka kama gabanka matar aure ce.”

Yar dariya ya yi “Nima mijin aure ne, ka dube ta fa ai ba alamar hakan a tare da ita.” Tsaki me karfi Ahmad ya ja ya juyo ya dube ni, “Kin ga abinda nake gaya maki ko.” Sannan ya juya wurin mutumin sa’ar ka daya ita ta yi shigar da ta kira ka amma ba dan haka ba, yayi kwafa “Idan an ce ga me irin fasalinta ba za ka yi marmarin kallo ba.”

Daga haka ya finciki motar ni da ban shirya ma hakan ba har ina hantsilawa muna isa “Sauka kawai ya ce min ganin ba fuskar tambayar gyalena na fita na soma tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa kuma jikina ya bani ni yake kallo dan ban ji tashin motar shi ba.

Tana shigewa cikin gidan ya shafi dan lub lub din sajen shi gaskiya Allah ya yi halitta a nan yaso ya yi wa kan shi sakiyar da ba ruwa yana tuna yanda take tafiya komai nata na girgiza ko ta ina ta cika, ashe ba banza take faman lullube lullube a hijabi ba ta san abinda take boyewa. Har mamakin kanshi ya rika ji tun da ta shigo hall din ya rasa sukuni gani yake kowa a wurin ita kadai yake kallo, wanda ya san Amina tana yawan sa gyale shi ne ma lullubinta amma bai taba damun shi ba.

<< Canjin Bazata 13Canjin Bazata 15 >>

1 thought on “Canjin Bazata 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×