Bismillahir Rahmanir Rahim
Na kusan ficewa sai naji motsi a bayana, wanda yasa ni jin faɗuwar gaba. “Barka da safiya Haj. Muryar Baba mai gadi ta ratsa dodon kunnena, cikin karfin hali na waiwaya muka haɗa ido, ” Barka dai Baba” na ƙara sauri dan in samu in fice, “Lafiya Haj da sassafe kuma a ƙafa? Na haɗiyi yawu, “Makaranta zani Baba ana neman mu ne.”
Na ciro Kuɗi na miƙa mashi ban kuma tsaya sauraron addu’o’in da yake kwarara min ba nayi waje, a ƙafa na fice unguwar kafin na samu abin hawa inda zan shiga motar Malumfashi na nemi ya kaini, babu ta can, sai dai zuwa Katsina, ita na hau, gabana na ta faɗuwa. a yayin da suke haɗa kudaden fasinja. Bayan wani ɗan jira aka gama haɗa kuɗin mota, direba ya ɗau hanya.
Mota tana ta shara gudu a titi ina kallon bishiyoyi, kukan da wayata ta ɗauka yasa ni saurin buɗe jakata na zaro ta Husna ce, ban ɗaga ba illa sakon text na tura mata na kashe wayar gaba daya. Cikin yardar Allah mun isa lafiya, a kwanar ABU na sauka, mashin na haye zuwa gida ina sauka na shige ciki, ina yin sallama mutanen gidan suka yo kaina da oyoyo har ɗakin mu. Ni dai ido kawai nake wurgawa in ga ta inda zan ga Innarmu ina cikin gaishe su ta fito daga uwar dakanta ashe mura take fama da ita, sai da ta ga kowa ya kama gabanshi ta tsareni da idanuwanta ina kokarin gaisheta bata kula ba.
“lafiya wannan tafiya ta ki? Dan murmushi na kakaro “lafiya lau” tayi ta fama dani ta ji wani abu game da tafiyar na kafe na ce lafiya lau. ta gaji ta ce “Shi kenan in ma dai wani abun ne ubannin naki suna nan, ko kowa ya kyaleki Baban Asiya ba zai dauki shegantaka ba (Baba ya’u).” Na ce “Bare ma innarmu ba komai” muna nan zaune Aminu dan wurin Baba sani ya aiko Innarmu ta san mashi miya shi Innarsu miyar karkashi tayi baya shanta.”
Ta ce ” Ka ce mashi kaza tayi kwanci kan murhun nawa.” Yaron ya juya, wani tausayi na ji ya kamani ina can cikin daula uwata na nan sai ta zauna bata dora abinci ba? Na ce “Innarmu ina Yusuf? Ta ce “Yana makaranta”. Na ce ” Yahya fa? ya daina bude shagon ne? Ta ce ” Ya kwana biyu baya jin dadi, a rufe shagon yake.” Na marairaice “kuma sai ku zauna ba ku ci abinci ba ina Salma? ta ce tana “Makaranta.”
Mikewa nayi na kira Aminu Kudade masu kauri na ciro na mika mashi lissafin kayan abinci na mashi ya tafi. Na zauna ina kallon dakinmu fes yake ta malala hadadden carpet dinta da na saya mata a saudiya da labulayya. Bayan Aminu ya dawo ya jide kayan abincin buhu daya na shinkafa na ce ya je da shi ya rabawa mutanen gidan, da tinkiya da nasa aka sawo aka gyara na ce ya raba masu kowace tayi miya. Jallof din couse couse na dora wanda na sawa hanta da kayan lanbu dan shi ne zai dahu cikin sauri na gama na adana shi a warmers na kai daki, a kofar dakinmu nayi girkin sai wani kifi irin kifin ruwan nan ne da direba ya tsaya a hanya na saya, na wanke shi sai na tsane shi zuwa yamma in dafa. Innarmu ta ce “Da kin cire wannan kayan kin samu wasu.”
Na ce “To” “Ni dai hankalina ya ki kwanciya da wannan tafiya taki, koma me ya faru da kin gaya min ya zan yi hakuri zan yi in ta fadin Alhamdulillahi alaa kullu halin, dama mu masu yaya mata ai bamu rufe kofa sai dai mu saya idan aka koro maka ka ce shigo.” Da naga hankalinta ya daga kwarai sai na gaya mata, fada tayi min sosai ta ce duk halaccin da uwarshi ta nuna maki bata cancanci wannan sakamakon daga gare ki ba. Komawa wuri daya nayi ina mata kuka, sai da ta gaji da fadan ta ce “Ki tashi akwai sauran kayanki da ban bayar ba ki canza” wata bulawus na saka na daura zane sai da nayi sallah Salma ta dawo, tayi ta tsalle da murnar ganina.
Na idar da sallar la’asar ina buga miyar kukar da nayi wadda nasa aka sawo min kaza da ita nayi sanwar dan haka ban bata lokaci ba na dora farfesun kifina wanda na sawa attarugu da albasa da kayan kamshi da alayyahu, ina zaune gaban rishon a kofar dakinmu ya dauko dahuwa dan kamshin shi kawai ke tashi. Ina ji mutanen gidan na ta gaisuwa alamar an yi baki, ina juyawa wa zan gani, Ahmad ne.
Ban kara mashi kallo na biyu ba na maida idona kan rishon gabana yana gama gaisawa da mutanen gidan ya tako kai tsaye zuwa kofar dakinmu, kallo ya kare min sai ya sa kai ya shige dakin. Ina jinsu shi da Innarmu yana gaisheta da suka kare waje ta fito, an kwashi kusan minti bakwai ban shiga dakin ba sai da Innarmu ta rika yo min dakuwa daga inda take zaune, na tashi na shiga kai tsaye da niyyar dauko inda zan zuba kifina. Na dauko na fito zan yi waje naji an rike hannuna ido biyu muka yi sai na sunkuyar da kaina dan sosai idanuwanshi ke min tasiri ban cika juriyar hada ido da shi ba. Kallo yake kare min ni kuma ina kiciniyar kwace hannuna, ” Yi hakuri yammatana na gane kuskuren da nayi shi na biyo in gyara, duk wanda ya dace in nemi afuwarsa kan abinda nayi maki zan yi hakan, kin hakura? Ya tanbayan yana leka idanuwana.”
Ko tashin hankalin da na shiga yau kadai da aka ce min ba a ganki ba kika rike a matsayin ramuwar abinda na maki ya isheki.” Jin ya sassauta rikon da ya yi min nayi saurin kwace hannuna nayi waje na juye kifin na cire na mutan gida na shigo da namu daki. Wuri na samu nesa da shi nayi tagumi, ya ce “Ba a yi dani ba girkin da aka yin?” Na tashi na kwaso su duka na ajiye gabanshi na hado da cokula da plate na koma inda na tashi, farfesun kifin ya zuba yana ci kallona yake “Banda ban ga su Baba ba da yanzu muka wuce.” Cikin dakewa na ce “Ni ba za ni ba.”
Haka muka dauki lokaci yana kokarin shawo kaina amma abu ya faskara har aka fara kiraye kirayen sallar magrib ya mike tsam dan tafiya masallaci, ni ma alwalar nayi na fara sallah. Har aka idar da sallar isha’i ban kara jin duriyar Ahmad ba, sai dai na ji bakin salma ta gan shi waje yana gaida Babannina. Asiya yar baba ya’u ita ce ta shigo ta ce Babansu na kirana.” After dress na dora saman wasu skintight guntaye da na saka sai na daura zane sama dan garin akwai zafi. Na same shi zaune yana cin tuwo, cikin girmamawa na gaisheshi.
Ya ce “Yanzu muka gaisa da mijin naki a waje shi ne da na shigo ladi ke ce min tafiyar daban daban kuka yi ta ke kin zo da rana shi kuma da yamma, shi ne na ce da kyar ba wata shegantakar kika shirya ba, lafiya? Na ce “lafiya lau” Ya ce “Mijin naki ya bamu hakuri ya kuma roki san tafiya da ke gobe idan Allah ya kaimu, yana so ya koma ya je wurin aikinsa.” Kuka na fara,
“Ni daga zuwa in bi shi gobe? Dama shi mutum ne me saurin hasala nan da nan ya taso min, ” Idan ba ki bi shi kun tafi ba sai ki gaya min uwar da za ki dauka nan din? Kin ga Shuhaina ki fita idona in ba haka ba ina ganin sai na shige ki, sannan za ki nutsu ki gane abin da ake nufi, yanzu gaisheni kawai ya yi ga kudin da ya bani nan ko kirga su ban yi ba, yan dubu dubu ne ga su nan lodi guda, yar banzar yarinya arziki na kiranki tsiya na hanaki. Nan ya yi ta balbalin fadansa ina sauraro har na shiga kuka, sai da ya kare ya ce in wuce in ba shi wuri. Haka na shige dakinmu ina kuka, Innarmu ganin kukan da nake ta fita ta bar min dakin, ina cikin kukana naji muryar Ahmad a kaina, tsugunawa ya yi daidai kaina yana tambayata abinda aka yi min, nayi banza da shi. Da na gaji da lallashin da yake min na ce, “Dama ka je ka gaya masu dan ba zan bi ka ko ina ba.” Kasake ya yi sannan ya mike ki yi hakuri ki same ni mota sai mu warware matsalar.”
Na ce “Babu inda zan same ka.” Kallona kawai ya yi yasa kai ya wuce bayan ya fadi “Ina jiranki.” Ina nan wurin sai ga aiken shi yana jirana, na kori yaron. Ai kuwa Baban ne ya fito da kanshi kan in fice har saida ya dauke ni da wani gigitaccen mari, dan haka a guje na fice wajen, sai da nayi waige waige kafin na hango motar tashi nesa kadan da kofar gidan mu, har ya bude min kofar, ban da zabi sai kawai na shiga, ina shiga nasa kuka me cin rai ya jawoni zuwa jikinsa.
“Yi shiru, bana san kukan nan.” Na ce “So nake ka sauwake min auren ka ka auri zabin ka wadda kake so.” Amsa ya bani da cewa “Ai bani da wani zabi da ya wuce ke, saki kuwa tsakaninmu babu shi ina ganin ko za a daura min bakin bindiga ba zan iya furta shi a gare ki ba, zan dauki kowane irin bori da za ki yi min, babban burina ki huce ki so ni kamar yanda zuciyata ta hanani sakat saboda kaunar ki, tun ban dawo ba aka jarabci zuciyata da san ki, ina kuma dawowa nayi arba da ke zuciyata ta dada sukurkucewa, na rasa duk wata jarumta a kanki, sanki nake da dukkan zuciyata, ki yafe min laifin da nayi maki ko so kike in duka a gabanki dan ki fi gane irin nadamar da nayi? Saurin cewa “Ah ah” nayi tare da kokarin kwace kaina ya kara matseni “Dan Allah ka barni Innarmu taso rufe dakinta.” “Ki bini masaukina ki bar Mama ta rufe kofarta.” Ya fadi yana kara mannani a jikinshi,. Nayi saurin cewa “A’a” Ya ce “To in kina son in kyaleki sai kin ce kin hakura”. Na ce “Ya wuce.” Ya ce “Yawwa” yana kallona ina maida after dress dina da ya cire min. Na kauda kai, “Ba fa ka ci abinci ba?” Ya ce “To ya na iya? Tuwo nayi za ka ci Ban cin abinci me nauyi da daddare amma daga babyna tayi zan ci je ki kawo min sai in tafi da shi. Na shiga na zubo na kawo mashi, Ya sallameni ya wuce. A daren da tunani kala kala na kwana.
Da safe ina ganin Baba ya’u ya shigo dakinmu na baro dakin na wuce dakin Gwoggo Rakiya na haye gadonta nayi kwanciyata, ita kuma tana ta kokarin fara tuyar waina dan dama tun sanin da nayi mata ita din kwararriya ce wajen waina da tana ta saidawa sai ta bari sai idan an bata aiki, yau ma gidan wani attajiri da ke kusa damu ake biki. Kallona tayi ” Hala shigar Baban Asiya ya koro ki? Na daga mata kai “Jiya fa har marina ya yi.” Dan girgiza kai tayi “Ai yaya ba shi da dama jiya tunda aka ba shi kudin nan ya rasa inda zai sa kanshi, ko ni ya shigo dakin nan ya fi a kirga yana banbami, kin samu arziki za ki sa kafa ki shure, kuma gaskiyarsa, dan jiya gidan nan ba wanda bai shaida zuwan yaron nan ba, ya cika mu da abun arziki, Fatima kuwa ai sai Allah.
Nasan so take ta ji abinda aka ba Innarmu sai na ki gaya mata. Nan ta fice ta barn. Kamshin turarensa ya fara cika hancina kafin ya bayyana cikin dakin, ya yi kyau matuka cikin dakakkiyar shadda sai maski take, annuri kawai ke fita a fuskarsa, shi ya nema wa kanshi wurin zama, ina zaunen na ce a hankali “Ina kwana? Ya amsa yana dan murmushi, sama da kasa yake dubana “Wai a tafiyar da nayi ta shekara guda kika sauya? Waccan Shuhainar da na sani kullun cikin rufe jikinta take, amma wannan da ko wane irin kaya zama take ya kama rigar jikina yana lekawa hala daga ita ba ki sa komai a kasa ba ina kokarin kwace rigata aka yi sallama a kofa ya yi saurin sakina dan wajen Baba sani ne ya ce Gwoggo Rakiya na kirana na same ta kitchen inda take Suya kwanonin zuba abinci babba da karama masu kyau ta nuna min waina ce da miya wai in kaiwa Ahmad, bude ido nayi Baba ba aiki aka ba ki ba? Ita ma idan ta bude min “Idan aiki aka bani fa? Can gidan ma na aika na ce su bani miya surukina ne ya zo, ki duba miyar ta yi kyau ai ina ganin zai ci.
Na dauka na wuce dakinta me tsabtar tsiya Dan tsananin tsaftar gwoggo Rakiya ko bayi za ta bata yarda butarta ta taba kasar bayin. Ya ci fiye da yanda na za ta dan miyar ta sha tantakwashi da manshanu sai kamshi take. Da ya kammala ya ce.” Taimake ni ki yo wanka mu wuce ina so har in samu office, yanzu ma Momi ta kira ni, Husna kuma ta ce me ya samu wayarki dan tayi nacin in taho da ita.” Na mike naje nayo wanka na shirya kaina cikin shadda dinkin riga da siket, na tsuguna gaban innarmu, fada tayi min sosai tare da nasiha, Ahmad ya shigo yana mata sallama cikin sanyinta take mashi godiyar dawainiyar da ya yi.
Sai da nayi ma kowa sallama sai na same shi a mota, ya tashe ta yana kallon fuskata hannuna daya cikin nashi yana cewa “An min kitso dan ubansu, an min kunshi amma a bari akai min in gani sai kika gudo ke da zuwa sai dai in kin haihu raurau nayi da ido ya ce, “A’a kar ki min kuka gaban Momi zan kaiki tayi miki hukuncin gudun da kikayi ba saninta. Gudu sosai yayi dan haka daya da wani abu muna Abuja, saukeni kawai ya yi ya juya kan motarsa.
Ni kuma na rasa yanda zan yi in shiga ciki sai dai nayi ta maza. A falo na hango ta zaune tana kallo. “Oyoyo yan hijira” ta fara fadi tare da tambayar su Innarmu da mutanen gidanmu, nan na gane abin da nayin dai bai bata haushi ba. Ta ce ” Ki samu Husna a daki tun da ta tashi bata gan ki ba bata cikin walwala, sai ki zo ki ci abinci. na amsa da “To” Ina shiga Husna da ke kwance tana dago kai ta yi arba dani ta duro ta rungumeni muka fada gado. “Su Anty yan duniya.”
Na ce, “Ai sai ki fada min waye dan lahira” Muka kwashe da dariya. Ta ce, “Jiya kin kada min ciki ba kadan ba, musamman ya Ahmad ba ki gani ba an dawo masallaci an sha kwalliya za a dauki amarya Momi ta ce ai tun safe aka tashi ba a gan ki ba.” Tashin hankali, ko ni sai da na tausaya mishi kawai sai muka ga ya zari key Momi ta ce ina za shi?
Ya ce Malumfashi ya gani ko can kika tafi, ai fa nan Momi ta rufar mishi ai dama sa maka ido nayi in ga iya hankalinka tun da mutanan nan suka baka diya ka taka kafarka ka je kayi musu godiya ya gagara, ka dawo ka je kayi ban hakuri nan ma ba daya, yanzu ai sa gan ka, ta kyauta kwarai idan can din ta tafi. Ya fice falon na aika Abakar zan bi shi ya koro shi na mashi text ba amsa. Na ce, Ya gaya min. Da muka gama hirar mu sai muka ci abinci Husna ta shiga azalzalata in tashi in yi wanka in shirya nayi banza da ita, sosai nake cikin jimamin rabuwa da Momi da yayanta, mun saba ba kadan ba Hausawa kuma suka ce sabo turken wawa, rai kuma ba abin da take so irin me kyautata mata. Husna ta hada min komai nawa ina kallon ta. Da na idar da sallar la’asar Momi ta ce kiyi kokari ki shirya yana hanya.