Ranar da na cika kwana talatin da biyar sati biyar kenan, muna kwance da daddare, kaina ya shafa "Har kin yi barci ne? Na ce "A'a" "Akwai aikin da zan je yi ibadan ina sa ran zan yi sati biyu." Dan shiru na yi, jin ban ce komai ba.
Ya ce, "Ba ki yi magana ba? Maimakon maganar sai na kama mishi kuka, rarrashi ya shiga yi ya ce, "Kin fi san in tafi da ke? Ba halin hakan ne, wadda Momi ta samo maki za ta iso gobe kin ga za ta debe maki kewar zama ke. . .