Bismillahir Rahmanir Rahim
Na kashe datar na ajiye wayar, na gyara kwanciya. Haj tuni tayi nisa cikin barcin ta. Babyn ba shi da rigima da zarar an mashi wanka to ya shiga barci kenan. Hasken da na gani a wayata yasa ni ɗauko ta, saƙon Ahmad ya shigo zolayata yake in zo in taya shi kwana ni kaɗai yake jira, ɗan murmushi na yi na rufe wayar na ja bargo na rufe rabin jikina.
Da safe cikin nishad’i me yawa na tashi, saboda yau zan ga ƴan uwana a daki. Isowar la'asar suka yi. . .