Skip to content
Part 23 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Sai da Junior ya yi wata hudu sannan na samu ya barni na tafi Malumfashi.
A lokacin kuma har ya iya zama. Sannan ne aka sa bikin Husna da Sagir ɗinta watanni bakwai masu zuwa, dan wata biyar ne ya rage mata ta kammala karatunta.

Sanda Junior ya cika shekara ya yi daidai da tura Ahmad America za su yi bincike kan wasu cututtuka. Ba kaɗan yaso tafiya da ni ba nima haka, sai dai ba halin yin tafiyar ta mu tare, ga bikin Husna da ke zuwa Momi ma cewa tayi idan muka tafi duka shi ba shi ni bani, nima kam ba zan so a ce bani a bikin Husna ba duk da na san ba karamar kewa zan yi ba ta rashin shi tsawon watanni bakwai zuwa takwas.

Na dai hakura, sai dai hakan bai hana ana gobe tafiyar ta shi na tasa shi nayi ta mishi kuka ba, tun yana rarrashina har ya rasa yanda zai yi dani sai ya sa min ido ya ce. “To ko daga tafiyar zan yi har sai an maki biza sai mu tafi tare?” Na girgiza kaina ina share hawaye da bayan hannu. “Na hakura sai dai ina tuna tsawon watannin da zan kwashe a gidan nan ba ka.” Ya janyo ni ya kwantar sai ya kwanta rigingine ya dora kaina saman kirjinshi, kalamai masu dadi yake gaya min, har na ji na dan samu nutsuwa, daga lallashi abu ya zarce wanda al’amura masu tsayawa a rai suka faru tsakanin mu a wannan dare.

Duk da gajiyar da na ke ciki bai hanani tashi da safe na shirya mashi breakfast, sai da na ajiye komai inda ya kamata sannan nayi wa Junior wanka na shirya shi, wanda lokacin ya fara tafiya, na kai shi wurin Baba na dawo wajena dan in yi nawa shirin, gyara kaina nayi na fito cikin kamshi na musamman, material na sa dinkin doguwar riga, na same shi yana cin abinci, tunda na fito idansa na kaina, har na ja kujera na zauna tafi na yi da hannayena ya dan ja ajiyar zuciya na ce, “Ya dai Yallabai?” Ya ce “Tunani, anya zan iya tafiya in bar ki” “Akwai ka da san maida zance baya na samu na rarrashi zuciyata za ka kuma jagula min ita.” Ya ce “Tuba nake madam dina, kin yi min kyau fiye da kullun.”

Dan murmushi na yi sai banyi magana ba na fara cin abinci yana tambayata Junior na ce, “Yana wurin Baba.” ya ce “A kawo min shi” na mike sai na yi wa Ma’u magana ta amso shi ana kuma kawo shi ya fara halin nashi na barna na ce, “Ka ga irinta ko da ka kyale shi sai mun kamala.” Mikewa ya yi da shi a kafadarshi ya ce “Ki hanzarta dan zan biya ta gida.” Na ce “To” takalmi da jaka nasa sai abaya na rufe jikina da na fito na samu har ya zauna a mota shi da danshi ga ma’aikatan gidan sun taru yana masu sallama har Baba tana wajen na matsa kusa da ita ta ce, “Ubangiji yasa aje lafiya a dawo lafiya, Allah yasa a dace da abinda aka je nema, gaba salamun baya salamun.

Na yi murmushin jin zancenta na karshe na ce, “To Amin Baba.” Na shiga baya kusa da shi, ya amsa sallamar ma’aikatan na shi da dinbin alheri da ya bi kowannen su da shi. Direba ya ja motar muka isa gidansu, kowa ya yi mashi fatan alheri, muka fito da Najib da Farhan da Ummi da Abakar suma za su yi masa rakiya, suka biyo bayanmu a motar Najib. Wayarshi ta shiga kara ya daga jin maganar da yake na gane da Abdullahi suke waya “Sai dai mu hadu a airport dan har na fito na ma biya gida na sallami su Momi.” Ya dan saurara “Ok thanks.”

Ya maida wayar inda take, hannuna ya kamo ya rike cikin nashi ya kira sunana na amsa tare da kara nutsuwa dan sauraronshi ya ce, “Na yi niyya bana ni da ke zamu sauke farali, sai ga wannan tafiyar da ta same ni, dan haka kujera daya a baiwa Mama, dayar kuma cikin babannin gidanku waye ya ce ma Abba an bani ke? kallonshi na yi “Baba Ya’u ne.” To sai a ba shi dayar ” Saboda tsabar murna ban san sanda na haye cinyarsa ba, ban ankara ba ina ta murnata sai da na ji ya cire min abayata na ce “Kai lafiya? Ya ce “Ita ta kawo haka, ba ki san sanda kika hayeni ba?” Cigaba ya yi da abinda yake yi dan har idanuwanansa sun soma sauyawa “Ke kuma da Momi za ku je umara idan ya rage two weeks sallah.” A kunnansa na rika rada masa santsar farin cikin da ya sanya ni.

Da muka isa sai da na goge mashi jambakin da na manna mashi a kumatu muka fito dan glass din motar tinted ne. Na sha mamakin dinbin abokan shi da suka zo wurin karkashin jagorancin Abdullahi, bin su dai dai ya rika yi yana masu sallama hade da godiya, Junior na kafadarshi aka fara kiran matafiya ya zo inda nake tsaye ya miko min Junior, peck ya bani a kunci. “Ki kula da kanki, ki tsare min kanki, muyi wa juna fatan alheri, sai Allah ya dawo dani.” Ina share kwallar da ke taho min ina mashi addu’a ya wuce mu ya shiga jirgi yana daga hannu.

Abdullahi ya karbi Junior motarshi ya sanya shi, ya ce zai kai shi wurin Al’amin su yi wasa sai yamma zai dawo da shi. Kai na daga mashi ba tare da nayi magana ba, na wuce motar da muka zo ciki, idona nata zubar hawaye, mun kusa gida na ji shigowar sako a wayata na duba wayar Ahmad ne zantuka masu sanyaya rai ya turo min, sai ga shi ina kuka kuma ina murmushi. Muna zuwa gida dakina na wuce na hau gado kwanciya na yi rub da ciki, wunin ranar sukuku nayi shi.

Da yamma Abdullahi ya maido Junior tare da kayan ciye ciye da na wasa, ko da na bashi nono kamawa daya ya yi ya saki ya kama wasan shi a zuciyata na kudurta yaye shi, dan dama ba wani damuwa ya yi da shi ba ya fi san ya ci abinci kamar ba shekarar shi daya ba.

Dawowar Husna sati guda kacal da tafiyar shi na wartsake, dan kwananta guda a gidansu naje na tarkatota muka yo gidana tare muke komai da ita dan wai yanzu take son koyon girki, ana son burge oga Sagir. Shirye shiryen bikin duk a gidana muka yi, kasuwa na shiga nayo mata sayayya ta makudan kudade. Ana saura sati biyu bikin Aunty Kubra ta iso, an sha shagalin biki irin na yarinya yar gata, me dinbin wayewa da tsagwaron ilimi, tare da dan da duniya ke yi da shi ta fannin abin duniya.

Komai a wurin bikin tare muke gudanar da shi da Khausar har mamanta ta zo, su yayarmu ma sun zo ita da Ummu da kakarmu Haj, Yusuf ma ya zo daurin Aure, anan suke gaya min Innarmu ta ba yayarmu Azima kujerar makan da Ahmad ya bata, shi kuma baba wai zai zo godiya, na ce su gaya mashi ya hutar da kanshi, me kyautar ma baya kasar.

A legos aka ajeta. Bayan gama bikin da kwana bakwai aka fara azumin Ramadan. Sallah saura sati biyu muka wuce umara da Momi Junior yana wurin Baba, ranar sallah muka dawo, tunda muka dawo nake kwance dan tun a can nake fama da matsanancin zazzabin dare daurewa kawai nake, ga kasala sam bana jin karfi da kaina na fahimci ciki ne dani dan nayi missing period dina tunda ogan ya tafi ban yi ba, text na tura mashi a take ya kira yana son in tabbatar mashi da gaskiyar maganar, na tabbatar mashi da gaske nake, ya umarce ni in je asibiti kar in sake in ta kwanciya na ce mashi, “To”

Wani hantsi ina zaune a falo wa’azin Dr Isa Ali fantami na ke kallo ina kuma saurare. Jikina duk a mace yake murus dan wa’azin tashin alkiyama yake da aikin da ke gaban dan Adam. Sai sallamar makociyata Zainab na ji na daga kai ina amsawa tamu ta zo daya, muna matukar mutunci, “Manya manya karaso mana.” Na fada ina rage karar da remote din da ke gefena, ta zauna tana dan murmushi. “Wash! wallahi duk na gaji.” kallonta na yi “Me kika yi ya gajiyar da ke? Form na je saye, direba ya fita shan mai na kasa hakurin jiranshi sai na tafi, kinsan ana dan wahalar man fetur ga zafin rana.”

Na mike zuwa kitchen ina tambayarta “Form dinme ki ka je sawo mana?” Na dawo da lemo da ruwa hada kofuna akan faranti, na ajiye mata na karbi form din a hannunta ina dubawa, ta ce “Tallar wata makaranta na gani cikin wata magazine, course ne kan harshen turanci tsantsa akwai tsada amma akwai biyan bukata, mallakar wasu masu jajayen kunnuwa.”

Na ce “Turawa kenan” ta daga kanta “Kwarai kuwa, saboda wannan kishiyar tawa nake son yin karatun, kin san ma’aikaciya ce.” Kallonta na yi sosai, “Kamar ya?” Ta ci gaba tana kai lemo bakinta “Ita da yaranta yan rainin wayo ne, wai su masu ilimi, tun ina karama mahaifina ke da burin ganin na yi ilimi me zurfi kasantuwata yar shi ta farko, amma na sa shiririta na ki a shiririce na kare karatun sakandire. Saboda rashin kyawun sakamakona dole sai da na maimaita shekarar, in takaice maki sau biyu ina sake zana Waec da Neco duk bata canja zani ba. Babana ya yi fushi ya rabu da ni, sannan ne babansu walida ya fito neman aurena, ba a dau lokaci ba babana ya ba shi ni, Shima farkon aurenmu babu yadda bai yi da ni ba in yi karatun naki fafur, sai yanzu na ga yadda idan muka hadu da kishiyar tawa take min salo yasa nake son karatun shi kuma ya hau dokin na ki. Wai sai yanzu ya gane ka dawo gida ka iske matarka ba abinda ya kai shi dadi, dan ita ma’aikaciyar banki ce, shi ne da na ga wannan course din na makale ma shi da na ga wata shida ne kacal karshenta ya hakura ya bar ni in yi karatun idan ya ga a wannan din na bada himma.”

Jin ta yi shiru yasa na dubeta cike da labarin da ta bani “Ai ni Zainab banda ke da kanki kika gaya min haka da ba zan yarda ba dan ni aka ce min masters ne da ke yarda zan yi.” Yar karamar dariya ta yi, “Saboda me? “Saboda tsabar wayewarki da gogewarki.” ta ce “Ba mamakin hakan dan mahaifina ma’aikacin gwamnati ne, mun yi zaman garuruwa da dama, shima ogan me yawan tafiye tafiye ne, kuma ko’ina da ni yake tafiya ita bata samun dama saboda yanayin aikinta.” Girgiza kai na yi “Nima da Dr zai yarda ai da kin zo min da foam din na gaji da zaman kadaicin nan.”

Ta ce “Ki gwada sai mu rika fita tare.” Ta kara kallona “Kin fada sai dai kuma kin kara kyau.” Yar harara na bata. “Kin manta azumin Ramadan muka kammala ga sittu shawwal na fara.” Ta ce “Haka, amma ina sha sai da Dr ya dasa kwanshi ya wuce ya bar yarinya da aiki” kallonta nake cikin mamaki ta mike tana dariya “Bari in shiga gida ruwa zan watsa in kwanta”. na ce “Farfesun yan ciki na dora nasan kina so, ki tsaya” ta wuce tana cewa “In kin kammala Ma’u ta kawo min” na rakata ta wuce na dawo.
Kullun sai Dr ya kirani dan jin yanayin jikina, ina son yi mashi maganar makaranta amma fargaba ta hanani, da kyar na yi kunar bakin wake sai na shaida mashi, ai fada ya rufe ni da shi har sai da na ba shi hakuri, na kuma tura mashi text ina kara ba shi hakurin bata mashi rai da na yi, na mashi bayanin gajiya nake da zaman gidan kadaicin rashin shi na damuna, Junior ma kullun Momi ke aikowa a tafi da shi sai yamma a dawo da shi.

Har na manta da batun makaranta na cigaba da sabgar gabana, sai ga wani abokinshi a sanin da na yi mashi shi din lecturer ne ya kawo min foam din makarantar hada kudade in sa yi hijabai in ji Ahmad, mamaki ya rufe ni. Ba dadewa muka fara zuwa da Zainab, kwarai fitar da haduwa da jama’a ya dauke min kewar Ahmad da nake ciki, da kuma laulayin da ya sanya ni gaba.

Wata ranar asabar gidan Momi naje tana kallon yanda Junior baya barina sakat, ya haye ni ya yi ta tumurmusa ko kuma ya ce sai na goya shi, da muka tashi tafiya ya ce in dauke shi Momi ta ce, “Sauke shi, ki ma bar shi nan daga yau, ya barki ki ji da kanki, idan Allah ya saukeki lafiya ya dawo, Tunau zai zo zai amshi kayanshi.” Kunya na ji ta rufe ni, sai na bar falon ganin da sauran lokaci gidan Khausar na wuce, jakata kawai na ajiye na isko ta kitchen inda na ji motsinta, fridge na bude na dauki ruwa sai na zauna kan wata kujera da ke a kitchen din ta ce yar halas yanzu nake tunaninki, daga ina da yamman nan?

Na ce “Daga gidan Momi, wai dama ana gane ina da ciki? Ta ce “Me ya faru?” Na kwashe yanda muka yi da Momi na shaida mata, ta ce “Ai makaho ne kadai ba zai gane hakan ba, kin fa canja sosai da da farko ne kika yi rama sai ki ka yi kyau, yanzu kuma sai kika yi yar kiba me ban sha’awa, kallo daya za a yi maki a shaida hakan. Ogan ya sani?” Kai na daga mata tare da tambayarta Al’amin, ta ce sun fita da babanshi, kin kuwa leka shago?” Na ce “Tun dai wani sati da na dawo makaranta sai na biya, sosai wurin ke ci gaba ai dace da samun mutum me amana ya tsaya maka kan harkarka ba karamin dadi ke gare shi ba.” Murmushi ta yi na dan tura baki “Ai cikin ma da ke ya dace ba ni ba, kin fa huta.” Yar dariya ta yi “Ba yanzu ba tukun, muna honeymoon din da cikin shi bai barmu ba.”

Sai da na ci abincin da ta girka sai na isa gida. A kwana a tashi sai ga shi Ahmad ya kammala watanninshi, sai sa idon dawowar shi muke yi, cikina ya tsufa dan watanninshi takwas kenan na kammala course din da kwana shida ya dawo dirar ba zata ya yi min, dan bai sanar dani dawowar shi a ranar ba.

Zaune nake a falo ni kadai canjin channel na ke a talabijin, naji an rungumoni ta baya tsoro na ji ya kamani gabana ya fadi sai dai sassanyar kamshin da ba zai yuwu in iya manta mamallakinsa ba ya sani waiwayawa muna hada ido na kankame hannuwan shi da ya rufe min ido da su. Zagayowa ya yi ya zauna kusa da ni yana dafe da ni ni kuma sai kallon irin kyan da na ga ya kara na ke yi. Sanye ya ke cikin suit bakake agogon police shima baki daure a hannunshi.

Mun dade a wurin yana nuna min irin kewata da ya yi, kafin daga bisani ya mike tare dani zuwa bedroom dinshi, ba yanda banyi ya bar ni in kawo mashi abinci ya ce, “In kyale abincin muyi abinda yafi abincin muhimmanci. Dan haka kiran sallar magrib ya dawo damu daga duniyar da muka lula, cikin sauri ya zare jikinsa ya fada bathroom.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 22Canjin Bazata 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×