Washegari muka je gidansu ya gaishe su sai muka taho da Junior. Kwananshi ashirin da dawowa na haifi diya ta kyakykyawa wacce ita da ubanta kamar an tsaga kara. Tana fadowa ya ce Aminar shi ta dawo. Tare da shi muka yi haihuwar dan zan iya cewa shi ya yi komai muka yi tsaf ni da jaririyata. Ko Baba Kulu sai da safe ta gan ni da baby dan ta dare ce, tayi ta kakkabi.
“Ina gidan nan har ayi haihuwa ban sani ba?” Ta yi min fadan kar in sake mata irin haka na ce “To” ranar suna yarinya ta amsa sunan Amina. Ubanta ya hana in sake mata suna, ya ce in kirata da Aminarta. Watanta hudu aka yi masa transfer zuwa babban asibitin Katsina. Shi ya rigamu wucewa, satin shi guda da tafiya muka samu sakon haihuwar Anty Kubra. Ta samu tagwaye mace da namiji, muna da zuwa New Delhi kenan zo ka ga murna wajena.
Sai dai Ahmad ya yo min waya in bari idan ayyuka suka yi masa sauki sai ya shirya mana tafiyar ni da shi, marairaice masa nayi ya bar ni in je ayi suna da ni, ta Lagos zamu tashi dab da haka saura kwana uku tafiyar na isa birnin Ikko ni da Aminata dan Junior Momi ta kuma karɓe shi, gidan Husna na sauka muka yi mata baƙunta na kwanakin kafin muka wuce.
Mun sha sunan yan tagwaye, inda aka bar su da sunan su. Yan gidansu mata duk sun je, Rufaida bata sauya ba sai wani gani gani take min. Mun sha yawo kasantuwar Husna ƴar gari, kwanaki goma muka share sannan muka yo ƙasar mu ta gado, cike da dinbin karamcin da Aunty Kubra ta yi mana ita da mijinta. Muna dawowa Ahmad ya zo dan mu wuce ban so haka ba na so sai na je Malumfashi tukuna. Dan har lokacin ban tafi ba tunda na haihu, Mun yi parking din kayan amfaninmu daga ni sai shi a motar, direba kuma na janye da baba kulu da ma’u. Na samu gidan me kyau, wanda aka ƙayata da kayan alatu, ya ji komai na more rayuwar ɗan adam, duk da dai bai kai gidanmu girma ba.
Ban haɗa wata ba sai da ƴan gidanmu suka yo mota guda dan ganin inda na dawo, Junior dai ya zama na Momi dan har an jefa shi play group ta ce Amina ma da ta isa yaye da nan na bar mata ita. Muna makotaka da wata Rabi mutuniyar kankiya mijinta ne dan Malumfashi, mun so juna ni da ita, ni dai ina sonta saboda mace ce me tsoron Allah, da san gaskiya, duk wani abu na sabon Allah za ka ga tana kyamarshi, tana da kamun kai ƙwarai, yaranta biyar, ita tayo min Register a makarantar islamiyar da take zuwa, muka riƙa tafiya tare. Ina jin daɗin makarantar dan ina ƙaruwa sosai.
Wani hantsi ina zaune a falona ni da Yusuf, ziyara ya kawo min karon farko tun dawowata Katsina, Ahmad baya gari yana Abuja, kasantuwar ƙarshen mako ne kuma ma dai a ɗan datsin nan duk weekend sai ya tafi saɓanin da da sai ƙarshen wata muke tafiya tare, yana cinikin wani fili wanda ya ce min yana son fara ginin asibitin shi ta kanshi. Idan ya kammala zai ajiye aikinshi sai ya rungumi tashi, riƙe yake da Amina wadda ke ta ƙoƙarin cire mashi glass din idonshi
Na ce “Da ka ajiyeta ka sha lemon ba ta ji, ba za ta barka ba.” Ya ce “Haba kyaleta ai ni daɗi na ji da bata yi min ƙyuya ba, dan sabgogina basu bari ta san ni ba.” Na ce “Ai kuwa kayi wuyar gani na je Malumfashi ya yi sau uku amma ban gan ka ba, sai innarmu ta ce min kana Kaduna, ni ina ta murna da Ummu ta ce min takardunka sun yi kyau sosai, ina cewa sai aiki, sai kuma na ji shiru.”
Dan tsaki ya ja “Kin san komai kyan sakamakonka, sai kana da ƙafa, sha’anin ƙasar ne wa ka sani wa ya sanka ake yi, nayi fafutukar neman aikin har na gaji sai dai alƙawuran da aka yi min, Akwai wani abokina Sabi’u shi ya ce in zo muje Kaduna mu riƙa zama shagon yayanshi, dan shi tun gama sakandire ɗinmu ya koma wurin yayan nashi, sai da ya tambayi yayan ya ce ba matsala ya zo da ni, kin ji yanda aka yi na koma Kaduna. Kuma Alhadulillahi na gane kasuwanci na kuma san jama’a ina kuma samu gwargwado dan yayan nashi ba shi da mugunta, ciki har na yi wa innarmu aike, duk da cewar da take in sauƙaƙe wa kaina ba abinda ba ki yi mata.”
Sai da ya ci abincin rana ya yi sallar azahar muka gama firarmu, sai ya yi haramar tafiya, ɗaki na shiga na fito da wayata, sai nayi mashi transfer, jin shigowar sako ya ciro wayar shi yana dubawa, cikin rashin fahimta ya ɗago yana dubana, “Na mene ne waɗannan makudan kuɗaɗen da kika turo min?” Na ce “Ka yi amfani da su, kayi naka jarin, Allah ya sanya albarka a ciki.”
Kallona ya yi cikin sauri, “Kin kuwa san nawa kika sa Shuhaina? kuɗaɗen suna da yawa fa.” Na ce, “Na sani, fatana Allah ya sanya maka albarka a ciki.” Godiya ya shiga yi min har na ji kunya. Ahmad bai kai ga dawowa ba ya yi min waya an kammala cinikin, ya ma bari sai an sanya harsashin ginin kafin ya bar garin. Nayi murna ƙwarai tare da yi mashi fatan alheri, domin samun wurin ya ɗan ba shi wahala saboda yanayin wurin.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya wanda tuni na yaye Amina. Momi ta zo ta tafi da ita, daga ni har babanta rashinta kusa damu ya taɓa mu, dan yana matuƙar santa, muddin yana gida bata ƙara kallona, komai shi zai mata, baya taɓa gajiya da hidimarta ko wajen kwanciya tare suke tana manne da shi. Ranar wata talata misalin ƙarfe uku da kwata na rana ogan ne ya shigo ina zaune kan carpet ina cin abinci, ɗago ido nayi na kalle shi tare da yi mashi barka da zuwa, na rage ƙarar TV, dubana ya yi yaya dai maman twince ba ki tambayeni minata ba?
Dan murmushi na yi sai ban yi magana ba, ya ce “Na samu har ta zama ƴar gida, ta ƙwace wa junior fada har a wurin Abba, kowa zai fita ita ce ƴar rakiya, har mamaki ta bani tana tare da ni daga ganin Abba zai fita ta gudu wurinshi ta barni.” Na ce “Ka san bata da wuyar sabo ko makaranta na je da ita ba a barina da ita sau da yawa sai an tashi zan amsota.”
Ya dai girgiza kai yana shafar sumarshi “Ina ruwan Minata” ɗan lumshe idanuwansa ya yi ya watso min “Albishir” na ce “Goro” ya ce “Wancan satin da ya wuce wani tsohon class mate ɗina a turai ya same ni yake gaya min mahaifinsa yana nemana, da naje sai mahaifin nasa yake gaya min contract yake son bani na shigo mashi da kayan aiki, dan ya gina ma ƙanwar abokin nawa asibiti, dan jin daɗin yadda ta tsaya tayi karatu saɓanin ƴaƴan shi maza da dukkan su ƴan shiririta ne, shi kuma harkokin shi sun yi mashi yawa bashi da lokacin bincike da tsayawa a shigo da abubuwan, da kanshi yake ce min ƴaƴan shi maza duk sun ƙi karatu sai dai su shiga cikin dukiya su yi ta facaka.
Ya ce “Ai kin san Alh Shuaibu me kadara? na ce “Ina dai jin sunan shi a Abuja ko? ya ce “Haka ne, amma mutumin Katsina ne uwargidan shi ke zaune katsina amaryar na Abuja tare da shi, ya shahara ƙwarai fannin dukiya sai dai rashin sa’ar ƴaƴa, abokin nawa tun rabuwarmu a makaranta sau biyu na ƙara haɗuwa da shi. Ajiyar zuciya na fidda nayi mashi fatan alheri. Sati biyu tsakani muka bar ƙasar zuwa ƙasar China inda ya turo na’urorin, watanmu guda cif muka dawo, Ahmad ya kashe min kuɗaɗe fiye da zatona har na nuna mashi abin ya yi yawa, shafa kaina ya yi “Yarinya kin kuwa san miliyoyin da suka shige account ɗina? Girgiza kai nayi tare da cewa “Allah ya sanya ma abinda aka samu albarka.”
Ya ce “Yawwa kin ji abinda za ki ce” A Abuja muka sauka sai da hutun da ya ɗauka ya ƙare sai ya koma ni na zauna sai da muka sha sunan Khausar wadda sai yanzu tayi wa Abdurrahim ɗinta ƙane. Wani dare muna kwance wayar Ahmad ta hau ƙara, ɗaukarta ya yi tare da saurin yaye bargon da muka rufa, zaune ya tashi ina ganin tunanin shi nayi barci, ƙara lafewa nayi muryarshi ta ratsa dakin “Wai ba ina hana ki wayar daren nan da kike yowa ba? ɗan sautin dariya ya fito ta wayar “Ran Dr ya daɗe tuba nake, amma meye laifina?”
Ya ce “Amma kin san a halin yanzu ina tare da iyalina,” yar dariya ta ƙara yi “Kai dai ba ka da zance sai na wannan ƴar katsinawar taka, kamar daga ita babu sauran mata, lallai ta iya shafta dan ta samoka da yawa” Cikin gajiya da zancen za ka fuskanta daga muryarshi ya ce “Ya isa, idan kuma zancen matata za ki yi min idan kin kira to ki daina kiran dan ni ba sakaran namiji ba ne.”
Cikin lanƙwasa murya ta shiga ba shi haƙuri, kashe wayar ya yi yana jan tsaki. Ya dawo ya kwanta lamo na ƙara yi cikin tunani, dan tunda muka dawo ba daɗewa ya fara samun wayar dare kuma baya amsa ta gabana saɓanin da da zai ce in amsa idan yana wani aikin, kuma yana yawan fita idan ya dawo daga wurin aiki ba kamar da ba da idan ya shigo indai ba bukatar shi ake wurin aikinshi ba bai kuma fita, sai ko idan zamu fita tare dan akwai kyakkyawar mu’amala tsakanina da gidansu Abdullahi ina kai masu ziyara. Ƙwaƙwalwata ta cika da tunanin to wannan wace ce? Kuma meye tsakanin su?
Na daɗe barci bai ɗauke ni ba ba tare da na gano amsar tanbayoyin da suka cika min kwanya ta. Sati guda da yin haka muna zaune da safe, wayarshi ta shiga ƙara ya ɗauka ya duba, fuskarshi ta washe da murmushi Hello ya kike? ya faɗa yana wani lumshe ido, zuba mashi ido nayi dan na lura ya shagala ƙarshenta ma ya manta dani a wurin, “Yanzu zan fito, ok to ki ɗan jirani, bani 20minute zan iso in sha Allah.”
Ya kashe wayar ya miƙe ya gyara zaman rigarshi, ya ɗauki breaf case ɗinshi kaina yana sunkuye ya ce “Na wuce” “A dawo lafiya” Na furta ban ko ɗago ba, a gurguje ya bar wurin. Na miƙe gwiwata a saɓule na leƙa shi ta window har ya tada motarshi zai bar gidan ban san iya lokacin da na ɗauka zaune ba takaici na cin raina da na fara gane bakin zaren tsaki na ja tuna ni kaɗai ce a gidan bare in samu wanda za mu yi fira in rage zaman ɓacin ran, Baba Kulu ta tafi garinsu jinyar ƴar ta da ke fama da rashin lafiya. Bed room ɗinshi na shiga na gyara komai tsaf na fito na ƙwala wa Ma’u kira, ta iso cikin hanzari na ce “Ki gyara kitchen da falo har zuwa bathroom ni zan shiga wajen Maman Ihsan (Rabi)” Cike da ladabi ta amsa na wuce.
Ina zaune ɗakin Maman Ihsan tana min fira, sai dai rabi da rabi nake fahimtarta har ta ƙare ta taɓa ni “Wai yaya ne maman twince ko har an fara tunanin labon, ƴar dariyar yaƙe nayi sai na miƙe.
“Haba dai, bari in je gida, ta ce “Tun yanzu? Na ce zan yi girki ne ta raka ni gate, sai da na kammala girkin sai na sha wanka na ɗanɗasa kwalliya ina jiran Dr. Tunani kala kala nake yayinda nake zube mai da ido shi kuma yana cin abinci, ɗaga ido ya yi shima ya duban “Yaya dai Shuhaina? Na ɗan narke fuska “Ka ce idan ka dawo zamu fita in sayi kayan kwalliyata dan saura kaɗan komai nawa ya ƙare.”
Ki yi haƙuri ina da appointment idan na samu lokaci sai muje.” Ya goge bakin shi da tissue dama ya kammala sai ya miƙe, “Bari in yi wanka.” ya wuce ni na bi shi da kallo. Ƙarar da wayarshi ta ɗauka ne ya dawo da ni hankalina hannu na kai na ɗauka Yasmin me kadara shi ne sunan da ke yawo kan screen ɗin, kamar in maidata inda na ɗauke ta amma zuciyata ta ƙi bani goyon bayan hakan, sai na samu kaina da ɗagawa “Hello Honey ina ta jiranka muyi lunch, kai fa ka ce idan ka tashi daga office nan za ka wuto mu fita tare.
Ba zai yiwu in manta da mamallakiyar wannan zazzaƙar muryar ba, wadda tun da na soma jinta na kasa samun kwanciyar hankali. Latse wayar nayi na maida ita inda na ɗauke ta, kasa haƙuri nayi na kuma ɗaukota ɓangaren received call na shiga kiran da ake mashi da dare na ta ne na koma WhatsApp ai ji nayi kamar zuciyata za ta tarwatse dan wasu fitinannun text text da take tura mishi, kasa ci-gaba na yi da binciken wani kiran nata ne ya kuma shigowa na kashe wayar gaba daya na maida ta na aje tagumi na rafka da hannu bi biyu, fitowa ya yi cikin wata ɗanyar shadda army colour sai masƙi take ɗinkin half jamfa, bai sa hula ba sai kyakkyawar sumar shi da ke ta sheƙi shaidar ta sha gyara, agogon hublort ɗaure a hannunshi, fitinannen ƙamshinshi me narkar min da zuciya ke ƙara cika hancina, idan na ce ya yi kyau ya haɗu ƙarshe zai zama kamar ma ina ɓata bakina ne.