Skip to content
Part 25 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Peck ya bani a kunci, ya shafi cikina “Ina zuwa Shuhaina” ban samu ikon motsa laɓɓana ba ya wuce ni cikin sauri, bayan ya ɗauki wayar shi, ban an kara ba sai dai na ji hawaye na bin fuskata. Bai shigo ba sai bayan isha’i.

Tun daga ranar sai na tsangwami kaina ba hali in ga zai fita sai zuciyata ta raya min wajan ta za shi, nayi na yi in kauda zuciyata kan abin da bani da ikon hanawa amma na kasa.

Ranar wata asabar kasantuwar ba aiki, Ahmad ji da ni yake tun safe muna ɗakinsa.  Girki ma yana tare da ni na yi, ƙarfe uku ya dube ni “Idan muka yi sallah sai mu fita ki yi shopping ɗin ko? Daga mashi kai nayi, dan haka sai da muka sallar la’asar ɗin sai na sheƙa kwalliya, dan in ƙara janye hankalin shi, wani ƙanƙararren less na sa, me ruwan hanta yana da duwatsu,na sa sarƙa da ƴan kunne na English gold, cikin irin waɗanda Ahmad ya saya min a China hannuna bangul ne sai ɗayan na sa agogo, wata haɗaɗɗiyar after dress na ɗora sabuwa dal, ga ƙamshi me sanyi ina yi mara tashi saboda sanin illar hakan.

Kamshin turaren shi na ji a bayana sai na waiwaya, “Oya fito muje.” Ya ce min, ya yi kyau cikin ƙananan kaya farar shirt ce da blue wando, sai na bi bayanshi. Wani shopping mall muka je duk da ba yau ne farkon zuwanmu ba hasalima nan ne wurin zuwanmu idan za muyi sayayya irin wannan, wuri ya samu ya zauna na zagaya na zaɓi abubuwan da nake buƙata na iso wurinshi miƙewa ya yi sai ya biya kuɗin ta hanyar miƙa atm ɗinshi, muka jero yana riƙe min da ledojin, fira muke har inda ya ajiye motarshi gaya min yake “Sai mun ƙara dawowa sai ki duba kayan sabon baby ko? sai da na dube shi sai na ce “Ka san Khausar ta fita mana sari nayi mata saƙo.” Ya ce, “Ok to ki yi min list ɗin kuɗaɗen da kika bayar sai in tura maki ta account ɗinki.” Kai na ɗaga mashi, sai na ƙara waigawa inda wata matashiya ke tsaye jingine jikin wata rantsatstsar mota, tunda muka fito na lura da irin kallon da ta kafe mu da shi, haka nan na ji na tsargu da ita, buɗe min ƙofar ya yi na shiga sai da na zauna ya rufe ya zagaya ya buɗe ƙofar kenan daga bayanshi aka riƙa faɗin “Ran Dr ya daɗe.” Gaba ɗaya muka waiwaya, take na samu faɗuwar gaba, matashiyar da ke kallonmu ce doguwa ce fara wadda tsawonta ke tafe da jikinta, daga ganinta ka ga gogaggiyar ƴar boko, wayayya wadda hutu ya ratsa, sanye take da riga da siket na atamfa kayan sun kamata tamkar tana yin tari zasu kece, sun tona asirin komai na halittar jikinta, gabanshi ta tsaya tana wani rausaya jiki yanda take da ido ma kaɗai ya isa ban al’ajabi. “Yaya dai Yasmin? ya ce yana kallonta ta haske shi da wani ɗan iskan murmushi “Shopping na zo yi mu shiga ciki mana.”

Kanshi ya girgiza “Ina tare da madam ɗina, ki leƙa sai ku gaisa.” Ya leƙo “Shuhaina ga Yasmin me Kadara, me asibitin Yasmin Hospital. Gaisuwa muka yi kowa kamar bakinshi na ciwo dan ni tun ban gan ta ba ina tsananin kishin muryarta me zaƙin tsiya. Ya shiga ya yi wa motar key duk yadda yaso ja na da magana zuciyata cushewa ta yi na kasa furta mashi komai, da muka isa ɗaki na shiga nayi ta kuka a haka ya shigo ya same ni ya yi tambayar duniya me ya same ni na ƙi magana, har ya gaji ya ja min tsaki ya bar ɗakin.

Tun daga nan zaman mu ya ɗauki wani irin salo na daina zuwa ɗakinshi shima bai nema na, kwata kwata ya ma daina zaman gidan, A haka wani zazzaɓi me zafi ya kamani sai da na kwana na wuni sannan ya sani ya kula da ni ya bani temakon da ya dace a matsayin shi na likita amma duk da tsayuwar shi sai da na shafe sati biyu ina fama da jiki kafin Allah ya kawo min sauƙi, sai dai duk na lalace ban iya cin komai in ba dangin fruit ba. Tunda yaga na samu sauƙi sai ya koma fitarshi.

Wani dare ina zaune tsakiyar gado na rasa yanda zan yi barci ya ɗauke ni, hawaye ke sintiri bisa fuskata ina sharewa da bayan hannuna, na ƙara kai idona bisa agogo, ƙarfe sha biyu saura minti goma na dare, komai ya yi tsit duk da dai dama unguwar koyaushe shiru take. Har sannan Ahmad bai dawo ba, duk da dai tun sauyawar al’amuranshi ya fara kai dare bai taɓa kai sha biyu ba. Dirin mota na ji da ƙyar na cicciɓa na sauka gadon saboda nauyin cikin da ke jikina na yaye labulen Ahmad ne ke shigowa na tsaya har sai da na ga ya kullo ko ina, na kwanta hawaye na cigaba da tsiyaya min.

Bayan kamar wucewar minti arba’in na ji an murɗa ƙofar ɗakina, ƙara runtse idanu nayi dan na riga na gane ko waye turarenshi ya riga ya yi masa iso, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ban yi ba har ya hayo gadon ya kwanta gefena. Wanda na rasa dalilin hakan, dan rabon da ya zo ɗakina an kwana biyu. Wayar shi ta shiga ƙara ya ɗaga gane da wacce yake magana yasa hawayena ya ƙaru, sun jima suna magana kafin suka yi sallama, ya shiga barcin shi, ni dai ban san iya lokacin da na kwashe idona biyu ba. Da safe sallah kawai na yi na koma gado barci na samu nayi har sai goma na tashi, na shiga wanka na fito na shirya kaina cikin jallabiya baƙa me gajeren hannu sai na shiga kitchen neman abinda zan ci, ban hango motar Ahmad ba, da yawan lokaci sai in ta ganin kamar ba shi bane wanda ya nuna min tsantsar so da kulawa amma yanzu kamar be sanni ba, na daɗe a kitchen ɗin kafin na fito.

Karfe sha ɗaya Yusuf ya zo gaishe ni ba ƙaramar murna na yi da zuwan shi ba musanman yanda na ga ya canza dama ga shi kyakkyawa da gani ya samu hutu dan mun daɗe bamu haɗu ba, shi kuma sai tambayata yake wane irin ciwo kika yi kin ga yanda kika koma? Murmushi na yi “Ai na ma murmure” muka shiga hira yana gaya min shagon da ya buɗe na sayar da kayan masarufi ya karbu sosai har ya sayi mota Honda Civic mai ƙofa ɗaya, na leƙa na gan ta na yi mashi addu’a ya ce kuma kamfanin jaridar New Nigerian da ya nemi aiki da su sun neme shi dan ba shi aikin zai tsaya a fannin computer ne dan ita ya karanta, na taya shi murna.

Muna ta hira har na manta da halin da nake ciki ina yi ina duba girkin da na ɗora, ƙarfe ɗaya na kammala sai da ya fita zuwa masallaci nima na shiga ɗaki na yi tawa sallar ina idarwa hannuwana sama ina gayawa Ubangiji matsala ta tare da neman ɗauki daga gare shi, wayata ta hau kuka na miƙa hannu na ɗauka Ahmad ne, “Hello Assalamu alaikum” Shi na furta cikin sanyin murya, ya amsa sai cewa ya yi “Kar ki ga shiru ban dawo ba,aiki ya tsare ni.” Na ce “To abincinka fa? Ko in ba direban su maman Ihsan ya kawo maka? “No ki bar shi kawai, sai na dawo ko? ya katse wayar wani abu na ji ya tsaya min ƙwafa na yi na zuba ma wayar ido, abincin ma za ta fara janye shi ta hana shi cin nawa, “Allah ka kawo min agajinka.”

Na faɗa ina miƙewa tsaye jin motsin Yusuf a falo na gabatar mashi da abinci na zuba nawa, kallo ya bi abincin da shi “Dole ba za ki warware da wuri ba ai ba ki cin abinci.” Murmushi na yi sai na ƙara, ban ankara ba na ci fiye da zatona, da muka kammala ma’u ta kwashe kwanukan. Tsayuwar mota muka ji na miƙe na yaye labulen sai na leƙa Aunty Luba ce yayar Ahmad sai Rufaida sai ƙanwarta Ummi ke fitowa daga motar, dama duk family ɗin su sun zo su kaɗai ne basu zo duba ni ba, har Husna ta zo daga Lagos. Suka shigo ina ta masu maraba ni da Ma’u muka cika masu gabansu da abinci da abin sha, sai da suka yi sallah sannan suka fara cin abincin, Aunty Luba tana ta faɗin irin ramar da nayi, Rufaida dai abun na nan sai shan ƙamshi take, Ummi ma miskilar ce ba ta ƙara magana ba tun da ta gaishe ni. A raina ina ta kakkaɓin abin, Haj Babba ita ce miskila magana ma wuya take mata, amma ƴaƴan ta ba wanda ya ɗauko ta duk ƴan faran faran ne, ita kuma Haj Asma’u Aunty Amarya da take da fara’a ƴaƴan ta duk ƴan shan ƙamshi ne.

Yusuf ya ce min zai wuce na raka shi har gaban motar shi kuɗaɗe na ba shi ya kai ma Innarmu da babannina. Na ƙara mashi addu’a, sai muka yi sallama ya wuce, na dawo wurin baƙina sallar la’asar kawai suka yi suka ce za su wuce, na ce “Kai Aunty na sha kwana za kuyi min, ga shi ko Ahmad ɗin ma baku gani kuka gaisa ba.” Ta ce “Jirgin yamma za mu bi, Ahmad kuma mun ta try ɗin nombarsa bamu same shi ba, ai weekend ɗin da ya wuce da ya shiga Abuja ya je gidana, idan ya dawo ki gaishe shi Allah ya ƙara sauƙi.” Na ce “Amin na gode, ina zuwa na shiga gidan maman Ihsan na roƙi babban ɗanta ya zo ya sauke min su a airport, sai ya dawo min da motar hakan aka yi.

Da daddare da Ahmad ya dawo ko duba dinning ya yi ya ga wayam sai ga shi ya biyo ni ɗaki, “Ina abincina? na ce “Ban yi ba” ya ce “Meye dalili? na ce “Na ga na rana ma ka ce a bar shi so ban yi tunanin za ka ci ba.” Ya ce “Zo ki bani na ranar dan yunwa nake ji.” Na ce “Su Aunty Luba da Rufaida da Ummi sun zo su na ba abincin da ka ce ba za ka ci ba.”

Sai kawai ya rufe ni da bala’i, ina sauraron shi har ya ƙare ban ce komai ba sai share hawaye nake da zanen jikina, me kuma ya gani sai ya zauna bakin gadon jawo ni ya yi jikinshi yana lallashi, “Gaya min me yake damunki? Dan na san ba ciwon bane dan kin warware, ba ki sakin jikinki da ni a duk ƴan kwanakin nan, why? Shiru na yi “To tashi mu fita mu samo abinda za mu ci, dan kema na san ba ki ci komai ba.” Ya shafa cikin “Ko baby ai ba zai bar ki barci ba idan ba ki ci ba.” Miƙar da ni tsaye ya yi, da kanshi kuma ya nemo min hijab kan dole na sa wani mr bigs muka je ya yi saye sayen kayan ƙwalam muka dawo.

Ni dai shawarma na ci sosai sai na ɗora fresh milk sosai nake jin kuzari hakan sai ya sa ni gane hada ƙin cin abinci da nake yake sa nake ƙara rafkewa. Har a shinfiɗa ranar ya nuna min kulawar sa, wanda har na manta rabon da hakan ya faru tsakanin mu. Addu’a ita na riƙe ina neman ɗauki wurin me duka bisa ga wannan al’amari dan na san ba halin Ahmad bane shaiɗaniyar mace ya haɗu da ita, ita take son wargaza min rayuwar aure, Kuma duk yadda raina ya kai ga ɓaci da yanda yake ko oho da ni ban iya tarar shi in ce zan faɗa mashi mara daɗi, dan ina ganin mutuncinshi rashin kulawar shi gare ni kuma na san sharrin shaiɗanun mata ne da Allah ya haɗa shi da ɗaya daga cikin su.

Ina nan dai ina faɗawa Ubangiji kuma na san shi assami’u ne me ji kuma almujibu ne me karɓar addu’ar bayin sa. Muna nan a haka har watan haihuwa ta ya kama, zuwa lokacin idan ba farin sani kai min ba me wuya ka shaida ni saboda yanda na yi duhu na kuma rame, ni da Ahmad sai ido tun ina abinci in ajiye mashi har na hutar da kaina Ma’u na kan bari ta yi, abinda kan haɗa mu duba lafiyar cikina dan da farko samuna ya yi wai yana so in fara awon ciki a Yasmin Hospital, dan akwai ƙwararrun ma’aikata da za su duba ni yanda yake buƙata.”

Duk yanda nake ganin girmansa bai hanani galla masa harara ba dan takaicin maida ni sakarai da ya yi na ce, in dai ka gaji da yi min awon saboda ka fara gajiya da haife haifen da nake maka ba wai laifinka zan gani ba, amma ba inda za ni wurin wata banza awon.” Na miƙe nayi tafiyata biyoni ya yi cikin tsananin mamakina dan bai saba ina musayar magana da shi ba, sai wani gaya min ya yi “Ina tunanin wani abu ne kan Yasmin? Mutunci ne kawai tsakanin su,kuma ma ai ba ita za ta riƙa min awon ba.” Ni dai in kai da baka nan ka tanka to nima na tanka.

Wani yammaci ina ɗaki yana zaune falo suna firarsu ta waya, tunanin shi barci nake, ni kuma saƙe saƙen abinda zan yi in taimaki kaina nake, dan na gaji da wannan zaman ƙuncin har daga ƙarshe na samo mafita inda na yanke ma kaina shawara, har na ƙagara gari ya waye, tun da wuri ya fita wanda nayi murna da hakan, yana fita nima na fita zuwa gidan Maman Ihsan, a falonta na same ta “Ah maraba da amaryar Dr “ɗan tura baki nayi a dai dai lokacin da nake zama ƴar dariya ta yi.

“Satin nan kwata kwata ba ki ko leƙa makaranta ba, ga shi za a fara Exam.” Dubanta kawai na yi na ce “Ke ba ki san ko na je ba daɗin zaman nake ji ba.” Bayan mun ɗan taɓa fira na ce “Zuwa fa nayi Maman Ihsan in roƙi alfarmar direbanku ya kai ni Abuja idan ba takura.” Saurin dubana ta yi “Abuja da wannan tsohon cikin, ke kuwa me za ki yo? na ce “Na gaji da zaman nan ɗin, gara na koma can idan na haihu sai in dawo.” Ta ce “Shi ne ba za ki jira Dr ba? Na ce “Ƙyale wannan aikinshi ya yi masa yawa.”

Ta ce “Ba damuwa mu fita sai in ma direban magana, amma zan yi kewar ki wallahi.” Muka fito tana ma direban magana na wuce gidana na ci gaba da kintsawa. Tare suka shigo da direban ya amshi key ya yi gaba, Ma’u ta riƙa fito da kayan mu Maman Ihsan ko sai maimaita Allah ya sauke ki lafiya ina nan zuwa. Muka shiga ɗagawa juna hannu har muka ɓace ma ganinta. Sai da muka tsaya aka yi mana juyen baƙin mai sai muka ɗau hanya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 24Canjin Bazata 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×