Skip to content
Part 27 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Ta jeho min tambayar, ƙara duƙƙad da kaina na yi, na fara kuka, a hankali kuma na zayyane mata zamana da Ahmad tun daga samun kwangilar shigo da kayan asibitin Yasmin. Ajiyar zuciya me ƙarfi ta saki, jin na kai ƙarshe, ta ce “Ki ƙara haƙuri, komai zai wuce in sha Allah, babu abinda ya gagari Ubangiji, kema kuma sai kin dage kina tashin dare dan kai ma Allah kukanki.

Baba Karami ni na hana shi shigowa tun a asibiti, dan an ta neman layukan shi a rufe, sai a kira na ƙarshe ni ce na kira kuma na samu amma muryar mace na ji, shi yasa hankalina ya ɗaga da na ji abubuwan da kike faɗi, ki yi haƙuri.” Ta tashi ta fita, na cigaba da kukana mara sauti, ƴan yarana suka dawo, dole na bar kukan na riƙa sauraron shirmen su.

Da azahar Khausar ta zo suka haɗu da Husna suna min hira, sai na samu sauƙin zuciyata, tafiyar Khausar ba daɗewa na ji an turo ƙofar a hankali, ɗaga kaina nayi Ahmad ne, ya zauna kusa da ni, hannuna ya kamo ya riƙe cikin nashi, mun daɗe shiru yana bi na da ido har na kosa da zaman shirun, gyaran murya ya yi “Ki yi haƙuri Shuhaina, na rasa ta yanda zan ba ki hakuri dan na san ban kyauta maki ba, amma dai ina rokon ki da ki yafe min.”

Ni dai share ƙwalla kawai nake, har ya gama gaya min kalaman sanyaya zuciya, Sannan ya ce, “Da safe zan koma wurin aikina, na san ko na biyo Momi ba za ta bar ni ganinki ba, kuma sammako zan yi.” Da ƙyar na furta ma shi “Allah ya tsare.” Ya tashi ya fita. Bayan an yi sallar isha’i ina ɗaki, Momi ta ƙwala min kira, na amsa sai na fito, zaune na same ta tana sanye da hijab, ita da limamin gidan, me koyawa yaran gidan karatun addini, shima yana zaune, na gaishe shi, sai na zauna kan carpet, suka kare maganar su ina sauraren su, yana gaya mata kar ta damu, in sha Allah wannan ba wani abin damuwa bane za a gaya wa Allah za kuma a nemi temakon shi. Ita ma kuma ta dage da addu’o’in da ya bata, nima sai na daɗa warwarewa zai bani addu’o’in da zan riƙa yi.

Momi ta yi ma shi godiya ya tashi ya tafi. Nima na koma ɗaki ina tunani ita Momi gani take asiri ke ɗawainiya da Ahmad, sai ka ce ta manta halin mazan zamanin nan, iya shegen su ya girmi asirin. Asirin ma ai hali yake taddawa. Na cigaba da zama da Momi, cikin tsantsar kular da take bani, Dr da ta karbi haihuwata ita ke zuwa har gida tana dubani, hatta abincin da zan riƙa ci sai da Momi ta nemi shawarar ta, nan da nan kuwa na wartsake nayi mulmul, sai dai matsala ɗaya Ahmad tun daga zuwan nan bai kuma zuwa ba, sai dai ya kan kira waya ita ma sai jefi jefi, cikin tashin hankali Momi ta yi ma malam magana, ya ce ta kara hakuri sai a hankali in sha Allah komai zai dawo daidai.

Nima ya bani addu’o’i muka duƙufa ni da Momi. Sai dai wani abu da ke ɗaure min kai, Ummi ƙanwar Ahmad ƴar wajen Aunty Amarya da ta tare wajena, indai tana cikin gidan to za ka same mu tare, da ta ga zan yi abu za ta karɓa ta yi, ko kayan sawa ta ita ke zuwa ta dauko min. shiri sosai muke yi har nayi arba’in. Abba ya ce wa Momi ta kintsa ni in koma ɗakina, daga na warware ba da san ranta ba ta ce “To” Na roƙe ta ina son in tafi Malumfashi tukuna, dan na san hankalin innarmu yana kaina, hakuri da kawaici ne kawai irin nata shi ya hanata zuwa ganina, ba ta yi musu ba sai ma tsaraba da ta shiga haɗa min, Wani ƙarin mamaki sai Ummi ta ce za ta bi ni, hakan kuwa aka yi tare muka tafi, hadda Junior. Ummi ke raɗa min ita bata ga wannan yayan nawa ba da suka gani a katsina, na ce “Yana Kaduna” Dan halak ɗin sai ga shi ya zo washegari, tunda ya zo ta karɓi girkin dare, ita ke yi dama ga ta gwanar shi, dan shi ta karanta, wanda ba ra’ayinta bane, mahaifiyarta ce ta matsa mata kanshi.

Da kanta take shirya abincin da Yusuf zai ci, Wani dare take gaya min ita fa wallahi san wannan yayan nawa take, tun ganin da tayi ma shi a Katsina ta rasa yanda za ta yi da ƙaunar shi, dan haka tana buƙatar taimako na. “Na daɗe ina juya al’amarin a raina, na ga Allah kenan, shi babu ruwan shi, duk girman gidan su, da ɗimbin arziƙin babanta, da sunan da ya yi, ta zo cikin gidanmu ta ga yanda yake kuma ɗan cikin gidan take so, so kenan ba ruwan shi.

Ana gobe zamu bar garin, muna zaune da Yusuf, yana cin abincin rana, Ummi sun tafi gidan Ummu ita da Salma, loma ya kai bakinsa ya tauna sannan ya ce “Ina amfanin macen da bata iya girki ba, girki ai shi ne mace.” Duban shi kawai na yi “Ai fa kam yayana, to ko za ka shiga wurin me girkin ne? Ka ga shi kenan ciki lafiya baka lafiya.” Saurin kallona ya yi.

“Kin kuwa san abinda kike faɗi? Wannan ƙanwar mijin taki ai tafi ƙarfina.” A’a mace bata fin ƙarfin namiji sai dai idan baka san ta. “Ya ce “Sosai take burgeni, sai dai tunanin ajin rayuwarmu ba ɗaya bane shiyasa nake ya kice abin a raina.” Na ce “Kar ka ji komai faɗuwar gaba ai asarar namiji, kuma a rashin ta yi akan bar arha.” Ya shafa sumar kanshi “Ban ƙi ta taki ba, amma hausawa na cewa “Yaro tsaya matsayinka ka da zancen ƴan duniya ya ruɗe ka.” Na ce “Kai dai ka jaraba, dan ga alamu da nake gani itama kamar hakan take.” Da sauri ya ce “A haba? na ce “Kai dai gwada ka gani.” Da ta a dawo ya aiko kiranta, ba wani ɓata lokaci ta ƙara gyara fuskarta ta fita. Washegari da za mu tafi, tana motarshi, tamu tana gaba suna bin mu a baya, sai da muka iso Kaduna sai ta dawo tamu, a hanya har muka isa zancenta ɗaya ne Yusuf. A harabar gidan direba ya yi parking. Idona Ahmad ya gane min zaune kan motarshi, daga kallo ɗaya da nayi ma shi ban kuma ba, muka fito direba ya biyo mu da kayan mu, na samu Momi ta fita, sai Abakar shi ya shaida min hakan, ya zo daga Ibadan inda yake karatu, Farhan dai mutumina Abba ya cilla shi Malesia can ya maida karatun shi.

Ban yarda na zauna ba sai da na gaido mutanan gidan, Sai bayan nayi wanka na yi sallah yara suka shigo ɗaya daga cikin masu aikin Momi tana biye da su da ledoji, haye ni suka yi suna bani labarin yawon da babansu ya kai su, Sai ganin shi nayi shima ya shigo, kallon shi kawai na yi na ƙyale shi, ya riƙa tambayata mutanen gidanmu, mun ɗan jima ya ce “Idan kin kintsa ki same ni mota sai mu wuce gidanmu.”

Kallonshi na yi galala “Gida kuma? Momi ma kuma bata nan” ya ce “Ki bar saƙo idan ta dawo sai a faɗa mata.” A raina na ce “Wannan ma ya maida ni wata shashasha da mamaki na dube shi “Ba za a yi wannan rashin ta idon da ni ba.” Daga haka ban kuma bi ta kanshi ba, kan akwatin talabijin na maida hankalina. Ba a jima ba Momi ta dawo, ta yi murnar dawowar mu, na faɗa mata akwai tsarabar da aka haɗo min in kawo mata, ta yi godiya, Ahmad ya faɗa mata buƙatar shi ta san tafiya da ni, ɗaure fuska tayi ta ce ba yau ba, bai ce komai ba ya tashi ya fita, bai daɗe da fita ba Abba ya yi kiran Momi a waya, ta ɗan jima can sai ga ta ta dawo.

“Ki shirya ku tafi, dan Alh ya ce bai ga dalilina na riƙe ma shi mata ba, dan ya kai ƙarata, na so a ce kun tsaya dan wani temako na amso maku ke da mijin naki hada ƴaƴanku na sammu ne sai ku tafi da shi, dama na so ku gama amfani da shi, zan ba ki sai ki wuce da shi.” Na amsa mata cike da ladabi tare da gode mata bisa karamcinta a gare ni, ta sallame ni ta ce in je in yi sallama da mutanen gidan, har Amina muka tafi ɗan ta ƙi zama fafur.

Baba Kulu ta yi murnar dawowata, dan da ta dawo gidanmu ta sauka, sai da na kwantar da yara a ɗakin su, na tofe su da addu’ar da manzon rahma kan yi ma Hassan da Hussaini ita ce (A’uzu bikalimaatillahi tammat wa min kulli shaiɗanin wa hamma wa min kulli ainin lamma) na bar su na je na gama shirina na hau gado, sai da na tofe jikina da ayatul kursiyu da ƙulaƙuzai sai na cika da (Allahumma ƙi ni azabaka yauma tub’asu ibadika) yayin da na ɗora kaina kan pillow sai ga Ahmad ya shigo, sha’anin miji da mata duk haushin shi da nake ji kafin safiya ya mantar da ni.

Mu’amala me daɗi muke yi kamar da kafin shigowar Yasmin cikin rayuwar mu. Sati guda ya share a Abuja, har sai da na riƙa tuna ma shi aikin shi, ya ce”To ya zan yi da ke? Kin ce ba ki komawa Katsina ni kuma yanda nake jin kin koma ko na tafi ba wata moriya zan yi ba. An ya ina zargin ba wani shiri da Momi ta yi maki? Baki buɗe nake kallon shi, “Abin kuma hada Momi? Ka da ka yi wa Momi, wane shiri kenan kake nufi nufi za ta yi min? Maganganun da ya cigaba da faɗi ne suka sa ni tashi sai na bar ma shi wajen. Da zai tafi sai ga ni ina kuka, dan kishi ke cin raina kuma baƙin cikin da na ƙunsa a Katsina yasa zaman garin ya fita raina.

Ba a ɗau wani dogon lokaci ba Abba yasa ranar auren Yusuf da Ummi sakamakon ƙaunar da ta sarƙe a tsakaninsu, babannina suka zo nema ma shi auren, ni kuma na haɗa ma shi lefe na gani na faɗa. Mun sha biki, ni dai saboda zirga-zirga bani Abuja bani Malumfashi bani kaduna inda ya ajiye ta, flat hause ya kama me kyau a unguwar dosa, kafin ya kammala ginin filin da ya saya a kinkinau, sai da na kwanta bayan biki na yi jinyar gajiya.

Kammala bikin da sati biyu na gama shirina tsaf, cikin ƙananan kaya riga da siket na English wear, sashen mai gidan za ni dan yana gari ya zo weekend, na zo daf da shiga wurin shi na tsinkayi muryar shi da shi da wani da ban gane ko waye ba, sai na ɗan dakata jin maganar da wancan ɗin yake yi, “To yanzu dai ita ta ce duk wannan maganar a bar ta, in dan ta ce ka aure ta ne, to ka dawo ku ci gaba da soyayyarku, dan ba za ta iya jure rashinka ba, sosai take sanka, ba ka ga yanda ta shiga tashin hankali ba, ni idan ta kira wayata har rasa yanda zan ce da ita nake, ni ne kai Allah na tuba na samu wannan garaɓasar, ai kwantar da kaina zan yi in ta cin duniya ta da tsinke.”

Muryar Ahmad na ji ya amshe maganar “Kai mutumina daga na samu Allah ya tsamo ni, ai ba zan yi gangancin komawa ba, dama ni na san ba wani abu ke fizgata zuwa ga Yasmin ba sai sha’awar ta, ka san tana da manyan abubuwa, ni kuma ba abinda ke ɗaukar hankalina a wurin mace irin su.” Dariya abokin ya yi shi kuma ya cigaba Allah ya taimake ni na dawo daga rakiyar sheɗan. Matata ta ishe ni dama bata rasa komai ba, kuma sosai nake san ta, dan ban taɓa san wata mace ba kamar yadda nake san ta.”

Abokin ya amshe “Ka dai duba lamarin yarinyar ta shiga wani hali saboda rashin ka, ko ka san ta dawo garin nan ta baro asibitinta saboda ta ji an ce ka ajiye aikin ka dan ka kammala naka asibitin? Faɗuwar gaba na samu jin maganar shi, amma sai na ƙara fakewa in ji amsar da Ahmad zai bayar, “Ko zan buƙaci ƙara auren, bana jin zan iya aurenta dan yara ne waɗanda iyayensu suka basu lasisin lalacewa da sunan gata, ballantana na gaya maka matata ta ishe ni.”

Barin wurin na yi dan yanda na ji gabana na harbawa, na koma wurina cike da tunanin waye kuma wannan me ɗaure wa ɓarna gindi? wannan ma ai ba abokin ƙwarai bane, daga labulai nayi ina hangen harabar gidan, kallo ɗaya na yi wa baƙon nashi na gane shi, wanda ke ƙoƙarin buɗe motarshi, Ahmad na bayan shi, wani ɗan manyan ƙasa ne idanuwan shi kawai ka kalla za ka san ba ƙaramin ɗan duniya bane, sunanshi Jibrin. Ya kan zo wurin Ahmad jefi jefi, na lumshe idanuwana ina ta ma mijina addu’ar Allah ya kare shi daga faɗawa halaka da sharrin mugayen abokai, da kuma faɗawa saɓo kowane iri ne. Tattausan hannunshi da na ji kan wuyana yasa na buɗe idanuna ina kallon shi, peck ya bani a kunci “Kwalliya aka min haka shi ne ba a zo in gani ba? “Na ga kana da baƙo ne Coffee na miƙa ma shi dan dama shi na je kai ma shi na saurari zancen su, yana sha muna yar fira da ya kammala sai ya miƙe “Sanya lulluɓinki, ki ɗauko Mina, sai ki same ni mota.” Kallon shi na yi “Ina zamu? “Ki dai yi yanda na ce.”

Sai ya fice wajen Baba na je na ɗauko ta, a shirye take kodayaushe yarinyar kamanninta da ubanta ƙara bayyana suke, Junior dai tuni Momi ta karɓe abinta. Kama hannunta nayi zuwa wurin motar wadda bai daɗe da shigo da ita ba samfurin ANACONDA baƙa wuluk. Muna tafe ina ƙara tuna ma shi haihuwar Husna, yaushe zamu tafi? dan Khausar ta ce min za ta je ,ta wutsiyar ido ya dube ni “Ko ranar suna sai ku tafi” Marairaice mishi nayi “Yi haƙuri likitana” ya ce “Amma kin san ba zai yiwu ki tafi ki bar ni ba.”

Daga kaina nayi mun daɗe shiru kamar ba zai yi magana ba ,”Sai ya ce ki shirya ana gobe suna sai ku tafi nima ranar zan wuce, in haɗo ya nawa ya nawa in dawo gaba ɗaya.”

Na ce “Na gode” Parking ya yi a harabar asibitin, wanda na ga an sa wa suna MINA Specialist Hospital, rabona da zuwa wurin tun ginin bai yi nisa ba, muka zo tare da shi. Cikin matuƙar girmamawa aka tarbe mu, sai zagayawa muke ko’ina cikin asibitin komai ya yi, wurin ya yi kyau ƙwarai, da gani ba tambaya ka san an narkar da miliyoyin kudi, ba abinda ya fi burge ni irin ƙayataccen masallacin da a ka tanfatsa a harabar asibitin. Na yi ma shi addu’ar fatan alheri, sai muka bar wurin, mun tsaya wurin shan ice cream ya saya sai muka yo gida. Muna zaune a falona muna magana kan asibitin, Knocking aka yi na bada izinin shigowa, Rufaida ce, da ganin yanayinta hankalinta baya kanta, Kan carpet ta zube Ahmad na faɗin lafiya? ta ce “Mijinta ne ya yo mata auren wulakanci da cin mutunci, ko gaya mata bai yi ba.” Mikewa na yi zan bar masu wurin da na ga kamar sirrin su ne Ahmad ya ce, “Ke ina za ki?

<< Canjin Bazata 26Canjin Bazata 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×