Skip to content
Part 3 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Innarmu tana kan kekenta Amina tana waya. Da na gama sai nayo wanka, na ƙara tsaftace bayan gidan, na kai ma Anty Amina ruwa, duk da dai gidanmu duk yawanmu Allah yasa mutane gidan suna da tsafta, da wuya ka ga abinda za ka ce tir! Mai na shafa na murza hoda nasa atamfa (deluxe) baƙa, me ratsin yellow – yellow, na aje hijab dina gefe.

Amina ta fito wanka, sagale na yi ina kallon kwalliyar da take yi, dauko wannan body spray, fesa goga wannan, shafa wannan body lotion, fuskarta wata ‘yar hoda, ta dan shafa. Nan take ta dauki sheki, wet lips kawai ta shafa ma labbanta, sai ta shiga sa kaya, wani tsalelen leshi mai matuƙar laushi da rashin nauyi, kalar sa ruwan zuma, yana da stones. Ta gyara dogon gashinta, ta kama shi da wani tafkeken ribbon, duk da tsawonta, wani high hill shoes tasa da jaka da gyale, duk kalarsu ɗaya, white. Sai tasa sarƙa da dan kunnenta suma white. Sai daukar ido suke yi, hannunta bangul ne sai agogo.

Na ce, “Daga jiya, zuwa yau kin mayar mana ɗaki na ‘yan gayu, saboda kamshi. Ba tayi magana ba, murmushi tayi “Bari in shiga ɗakunan mutanen gidan, in gaishe su, sai mu wuce.” Ɗaga kai na yi. Ta bi daki ɗaki kowa kuma abinda Allah ya tsaga rabon sa shi ta ba shi. Sannan ta zo muka fito tana ce ma ummu. “Ke ba za ki gidan yayar tamu ba? ta kaɗa hannu, “Ina da hidimomi da yawa, idan na kammala da wuri za ku gan ni.”

Muna zuwa ƙofar gida na ga tana murmushi, na kai idona inda na ga take kallo. Mijinta ne zaune gaban motarsa ya zuro kafarsa ɗaya waje, ya fito ya rufe motar yau har ya fi jiya kyau, wata dakakkiyar shadda ce sky blue da tayi matukar dacewa da hular kansa, agogon (Fiaget) ɗaure a hannunsa. Fuskarsa ɗaure take na tsaya a inda nake, ta ƙarasa gaban sa.

“Ba ka wuce ba? ya yi shiru ta ce, “Likitana ba ka ji na ne? nan ma bai tanka ba, kama kunnuwanta ta yi, ” Na amsa laifina. ya ɗan saki fuska,

“Dama tunda na ji kin hanani zuwa na san yawo kike son zuwa.” Rage murya ta yi. “Yi haƙuri Dr, nan gidan yayarmu za ni kawai, daga nan sai gidan hajiya sai abi dokar oga, sorry sir! Ta sara mishi, wani malalacin murmushi ya saki irin nasu na miskilaye.

“Mu je in gaishe da su mama, zan wuce, ina da appointment da Dr Sada.” Ya duba agogon hannunsa, gaba na suka wuce gaisuwar da na yi masa ma lafiya kawai ya ce ya wuce, tun anan na shaƙa, me ma ake da mutum miskili ita ta ji zata iya ni kam Allah ya tsaran da auren miskili, na ɗan jima a tsaye kafin suka fito, shi ya buɗe mata ta shiga kafin shigarta sai da ta buɗe min baya, ban san me ya ce mata ba ta ce masa “Ba ka gane ta ba? shuhainarmu ce.

Wani kallo ya min wanda ya ƙara min takaici, kamar in ce ban zuwa dan ni duk miskili ba wai shiri nake da shi ba, dan ban san wulakanci yafito ni ta yi, “Shiga mana Shuhaina” na kama murfin ƙofar na shiga na rufe, ya tada motar. Mun fara tafiya ya dube ta, “Me zan bar maki ne? ta ce “Kamar me kenan? ya ce. “Wai ko kina buƙatar kuɗi” ta gyara zama.

“Yanzu dai kam akwai wasu, sai dai ka san hidimar biki, ban san ko za su isa ba” nuni ya yi mata da wurin da yake ajiye kuɗi a gaban motar, “Akwai kuɗi a ciki ki kwashe su, idan kina da matsala sai ki kira ni, in tura maki”. Godiya tayi masa, muna isa ƙofar gidan yayarmu ni na fara fita, a sauka lafiyar da nayi mishi ma kamar yana ciwon baki ya amsa,,, tabe baki nayi a zuciyata na ce,

“Ka ci arzikin kana auren yar’uwata, da ko kallon ka na bar yi. ” Wuni me daɗi muka yi gidan yaya Azima . Inda tayi mana danbun shinkafa da kunun aya, sun yi daɗi ba kaɗan ba. har mijinta ya dawo shi kam me sakin fuska ne, sai da ya jajjamu da wasa, sannan ya fita. Yamma sosai muka tafi sai muka biya gidan hajiya, sannan muka gangaro gida.

*****

An shiga hidimar biki ba kama hannun yaro. Bajinta sosai Anty Amina ta yi wajen bikin. An daura aure an ci mai daɗi an sha mai dadi.

Ran wuni na dawo daga gidan amarya dama can na kwana, lokaci zai kama sha biyu da rabi na rana. Yan biki suna ta hidindimunsu, Haj Zinatu ce hakimce kan wata kujera na yi imanin idan aka kira ta da zinaru zata iya amsawa dan saboda adon gwal ɗin da ta sha sai sheƙi take ga wata marokiya gefenta tana mata kirari da mata biyu sun fi ƙarti goma. Shi kaɗai na riƙe cikin kirarin da take zabga mata” Kusa da ita na matsa ina gaishe ta, ta amsa da fara’arta ta ce,

“Ashe ba ki gidan shuhaina? na ce mata, “E na kwana gidan amarya ne,” “yanzu kuka iso?” ta ce, “E jiya direbana baya nan” Na ce, “oho.” Dakin kishiyar innarmu na shiga na gaida jama’ar da na samu a dakin sannan na wuce uwar dakanta inda Haj laila take zaune itama kamar yar’uwarta ta sha kwalliya ba magana amma ita jiya ta zo, na gaishe ta ta ce, min anjima za ta wuce. Na ce, “Haj ai ba ki gano ɗakin amaryar ba.” Ta ce “Za mu biya da direbana in zan wuce.” An yi buɗar kai, kowa ya ga ɗakin Amarya zai ce ma sha Allah ɗaki ya yi. Washegari tun da safe nake haɗa ma Anty Amina kayanta, dan mijinta yayo waya direba na hanya. Kafin ta tafi sai da ta saya ma innarmu waya, ta gaya wa Yusuf ya yi ƙoƙarin neman admission, ya fara karatu, za ta ɗau nauyin karatun nashi. Da za ta wuce da iyakacin ƙarfinmu mu ke mata godiya a bisa dinbin alherin da ta baibaye mu da shi, ita kam ƙwalla tayi tayi. Bayan kwana uku da tashin biki aka ba Yusuf kudin adashinsa, wanda ya yi zuciya ya ƙi karɓan kuɗin, sai da innarmu ta kashe wutar ta karɓa,

Wannan kenan.

Na ci gaba da zuwa makarantar islamiya har hutun mu ya kare. Wata ranar alhamis ba islamiya dan haka nayi niyyar zuwa ma Haj yammaci. Zama na yi na gyara jikina ina kamshi wasu riga da siket nasa cikin irin kayan da Anty Amina ta kawo min na kalli kaina a madubin da ke rataye a uwar ɗakinmu, ko ba’a gaya min ba nasan nayi kyau, sai dai ni kam Allah ya zuba min kunya, ganin yanda ta toni asirin ƙirjina kamar in cire ,sai dai na bar ta, takalma marasa tudu nasa na zura hijabi, Sallama nayi ma innarmu na bar gidan.

Sannu a hankali nake takawa har na isa. Ginin gargajiya ne bulo da bulo shafaffe da siminti, a tsaftace ba ka cewa me shi ɗin tsohuwa ce, sannan an ƙayata shi sosai da kayan alatu. Sanda nayi sallama tana lazimi dan haka wucewa kawai nayi na zauna, na ce, “Wash tsohuwar nan ki na jin daɗinki, ki ci kaji ki sha sanyin raɓa me ya fi ranki?

“Ai kam babu.” Ta faɗi tana miƙewa, “Kema ki fiddo miji ya ɓoye ki a gida ko kya huta da wannan tafiye tafiyen” Baki na kama “Lallai ma, ba laifin ki bane samu kika yi ina zuwa gaishe ki, kuma wa ya ce maki ma na isa aure? Hararata ta yi “A wannan cika da kika yi idan ba’a yi maki aure ba sai yaushe?”

Ɓata fuska na yi, “Wai ke duka nawa nake, na ma gama makarantar ne? “Duk a yan’uwanki wa ya yi cikarki a yanzu haka? Na ce “Kin ga dai ki raba ni da labarin cikar nan, mu dawo maganar gaskiya wanda nake so mutum ɗaya ne, to inda matsalar take, me shige min gaba nake tunani, In kuma za ki je ki zo min da shi ko gobe ba matsala.”

Ta faɗaɗa fara’arta “Ke kuma waye wannan, har sai an je an zo maki da shi? Ai indai yana sanki sai in yi hakan ai ba kaɗan ba nake son in ga kema an kauda ki, zan ma je in samu uwar taku” na ce “Ita za ta min auren? Ta ce “To ko waye sai in je, waye baƙona? Ina kallonta ƙasa ƙasa na ce, “Ai sai ki hanzarta, amma wanda nake so malam musa ne (Mijinta da ya rasu).”

Zuba min ido ta yi, “Ja’ira.” Ni kuma na kwashe da dariya. Ta ce, “In kin gama shakiyancin sai ki isa kitchen akwai farfesun kayan ciki, ki zubo ki zo ki ci, ki ji daɗin shakiyancin.” Na miƙe “Inda nake sanki ƴar tsohuwar nan, me wuya mutum ya zo ba ki ba shi abin daɗi ba.” Bayan na zubo na zauna ta ke ce min “An ce takwarata ciki ne da ita ko? na ce “E har ma da ummu.” Ta ce “Ma sha Allah, ubangiji ya raba lafiya.” Na ce, “Amin” Ta ƙara da cewa “Ke kuma kafin su sauka in sha Allah kina ɗakinki.” Na dafe kumatu, “Kai ni kam ko bisa kanki aka ɗora ni iyakarta kenan, kin tasa ni gaba kamar cikin fari ni ba ki san bamma san meye son ba, duk wanda zai ce yana sona ɓata min rai yake.”

Ta ce, “Ba an ce mutum uku sun zo sun tanbayi babannin naki ba, ai sai su zaɓi wanda ya fi hankali a ba shi, fatanmu dai wanda za’a zauna lafiya. ” Baki na turo “Da yake an ce maki zamaninku ne, in ma barci kike gara ki wartsake, ni ban ma yin auren idan ba samo saurayi kika yi ba ayi mana tare.

“Kwafa tayi “Taƙadara ki tsaya ayi maganar gaskiya sai ki ta sako shakiyanci, ni cire wannan hijabin da ba ki gajiya da shi kamar matar liman ki ɗora min tuwo, talatu abincin rana ta bar min, kin san kuma na fi san sabon abinci” Na ce “Ina Talatun ta je? “Marabar ƙanƙara duba jikanta da ya sha fama da baƙon dauro.” Na tashi na shiga kitchen ɗin Ina cewa “Tsohuwar nan ki dai ta da mutane tsaye, amma wani abincin kirki kike ci.” tana ta mitar na ƙi cire hijabi, na yi shiru ban ce da ita komai ba.

Watan cikin Anty Amina bakwai, kullum sai ta yi waya ta yi mita da magiya Innarmu ta zo ta ga ɗakinta, ita kuma sai ta ce sai an kwana biyu. Rannan dai ba masaniya sai ga ta tana tura cikinta, da ya yi tamkar ba na fari ba dan tsananin girma. Direba ya kawo ta, ta ce kwana ɗaya za tayi dan mijin nata ma baya nan, ya je aiki ibadan, dan yanzu ya kama aiki da babban asibitin Abuja (National hospital) A matsayin shi na ƙwararren likitan mata da ƙananan yara.

Ta tasa innarmu har kuka tayi kan su juya tare Innarmu ta ƙi. Ta ce “To innarmu ki bani Shuhaina in tafi da ita, idan na haihu sai ta dawo.” Ta ce, “Hauka kenan, sai ta je ku zauna kanku ɗaya.” ta ce “Kai innarmu Shuhainar ce ta kai ni? Ta ce, “Tsawo kawai za ki gwada mata, amma bata fi ki cika ba? Ni dai Ina zaune ina saurarensu a raina na ce “Ai ni kuma na bani da wannan cika da ake ta yayata min” Inna tayi mata alkawarin tana haihuwa za a zo da ni, saboda yanzu akwai makaranta.

Ta ce, “In kika bani ita sai in sa ta wata a can” ta ce “A’a indai kika haihu bayan yan suna sun zo nima zan zo maki.” Da zan ta tafi ta bani waya Infinix Hot 10 nayi ta murna. Da watan cikin ta ya tsaya Gwoggo Rakiya kanwar babanmu Ita ta tafi ta zauna mata. A lokacin ne ummu ita ma ta dawo haihuwa, dan an maida mijin aiki katsina, ga gida ita kaɗai ji da ita muke, ban bari tayi komai na ƙosa ta haihu in rinƙa mata reno.

*****

Ranar wata juma’a aka yo waya Anty Amina tana ɗakin haihuwa, za a yi mata aiki. Mota guda suka cika mutanen gidanmu hada innarmu suka tafi. Na kira su dan mu ji halin da ake ciki, wayar Haj kishiyar innarmu na kira, abinda take gaya min yasa ni wurgi da wayar, jikina na rawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 2Canjin Bazata 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×