Mahaifina mutumin Gora ne wani ɗan ƙauye da ke daf da Malumfashi, Sunansa shi Umar. An ce mahaifinsu ya rasu tun suna yara su shida maza biyar mace ɗaya, ita ce Gwoggo Rakiya ita ce ta uku. Riƙonsu ya koma hannun ƙanen mahaifinsu wanda bai taɓa haihuwa ba, sai bayan ma ya cire rai aka haifa ma shi Innarmu. Ya tura babanmu karatun allo Maiduguri ya samu karatu me zurfi.
Ya’u da ke bi ma shi ya tura Kano, amma saboda laulayinshi ya dawo da shi. Bai kuma ƙara tura kowa ba, Babanmu ya dawo gida da zancen auren wata shuwa Arab, Ƙanin tsohonshi ya tsaya ma shi. Sun kashe dukiya me yawa aka ba shi ita. Ita ce Haj Hauwa mahaifiyarsu Haj Zinatu da Haj laila sai ƙaramin su Mustafa.
Ya ware masu ɓangaren su daban, yana shiga kasuwar malumfashi ya yi saye da sayarwa, Cikin ɗan lokaci Allah ya buɗa masa, har ya sayi fili a Malumfashi ya gina. Ya so tasowa da iyalinsa Ƙanin tsohonshi ya hana, dan haka sai ya sayar. Ganin ya samu alheri sai ya ci gaba da sayen filaye yana ginawa ya sayar, tuni har an yi wa Rakiya aure, ƙannan shi biyu ma sun yi aure, Ya ƙara sayen fili makeke ya gina. Ya kuma ƙara roƙon ƙanen mahaifinsu da ya koma, wannan karon bai hana shi ba Nan da nan suka tare.
Daga baya ne ya roƙe shi ya ba shi auren tilon ƴar shi Fatima, Murna sosai tsohon ya yi ya ɗaura masu aure, in da duk shekara biyu sai ta haihu da Azima ta fara, sai Amina sunan ƙanwar mahaifiyarta Haj kenan, Sai Yusuf Sai Ummu Sai ni, sai haihuwar ta tsaya har sai da na shekara biyar, sannan ta samu cikin Salma, Watan cikin bakwai Allah ya yi wa mahaifin mu rasuwa a sanadiyar hatsarin mota. Iyalanshi da ƴan’uwansa sun ji mutuwar sa. Dan tun Innarmu na goyon Azima mahaifinta ya rasu. Duka yan’uwansa ya nemi su dawo gidansa, Hidimar Ƴaƴansu kaf shi ne me yi. Gwoggo Rakiya ma tun mutuwar aurenta na farko ta shiga yi yana mutuwa karshe ta watsar tayi zamanta a ɗakin da aka dawwama mata.
Tun daga nan Innarmu ta shiga wahala, dan mahaifiyarta ma ta rasu, tun tana goyon Ummu. Kanwar mahaifiyarta Haj ke tallafa mata, dan tana da ɗa me kudi yana zaune a Katsina da iyalin shi. Gidan da muke ciki babanmu tun yana da rai ya ce ba shi cikin abinda za’a raba gado, duk dan’uwanshi me sha’awar zama ya zo ya zauna, Mun ci gadon wani gidan babanmu da gonaki biyu an sa yan haya ana ɗan samun na cefane. Gonakin kuma akan ba manoma noma tashi su ɗan bada wani abu.
Ƴaƴan Haj Hauwa mutanen gidan suna ce mata Hajiyar Mustafa, Mustafan tsaran Ummu ne. Ƴaƴanta sun yi aure tuni Haj Zinatu tana kano Haj laila na Sokoto dukansu masu hali suke aure, Suna matuƙar hutawa, suna taimakawa mahaifiyarsu, dan duk gidan babu me jin dadinta kowa sai ya fita zai samo na masara. Yusuf tun soma girman shi ya ga yanda innarmu ke shan wahala kafin mu ci abinci ya dage da neman kuɗi duk abinda ƙarfin shi zai iya tana saida kayan miya wanda ba su zuwa ko ina ake cinye jarin, in ta samu ɗan kudi sai ta ɗora, tana dinki sosai.
Mutanen gidan mu duka suna girmama Hajiyar Mustafa wanda ko makaranta bata dame shi ba sai dai ya wanke goma ya tsoma biyar Suna gulmar ta kan wai ƴaƴanta suna badawa ta ba mutanan gida ita ke dannewa. Ana haka aka tashi auren Azima, wata uku ya rage bikin Amina ta raka Haj biki Katsina, anan Ahmad ya gan ta ya kuma manne mata dan bikin na gidan abokin shi ne na ƙut da ƙut Abdullahi, Kannan babanmu sun ce ba yanzu za su yi mata aure ba na yayarta za su yi tukun, ya nace har sai da mahaifin shi ya zo wanda babban mutum ne, ya roƙi alfarmar su ɗiyar kawai suke so, ana ɗaurawa a basu ita dan shima karatu yake yi bai shirya yi mashi aure ba, duka a lokacin shekarun sa ashirin ne da bakwai hutu ya zo, za a yi mata biza sai ya tafi da ita ta ci gaba da karatunta acan. Hakan akayi ana ɗaurawa aka wuce da ita Abuja gidan mahaifinshi, daga can suka lula England. Mahaifinshi ƙusan gwamnati ne da ya riƙe muƙamai daban daban a ƙasar nan, ya mallaki matan aure uku Mahaifiyar Ahmad ce ta biyu.
Idona biyu har na yi tozali da dutsen Abuja, Wayar da direban ke yi yasa na kalli in da yake, “E ranki ya daɗe mun shigo yanzu.” Ya saurara kafin ya ce, “An gama ranki ya daɗe.”
Babban asibitin Abuja National Hospital Muka yi wa tsinke rukunin gidajen ma’aikata direban ya nufa da motar. A gaban harabar gidan wanda ya ƙayatu da shuke shuke masu ban sha’awa ya tsaida motar, wasu mata guda biyu suka tare mu tare da yi mana jagora zuwa ciki, Gwoggo Rakiya ke riƙe da ni.
“Shiga da bismilla.” Ta raɗa min, Yayin da ƙafata ta taka tattausan kilishin da ke barazanar shanye min ƙafa dan tsananin taushinsa. Wani ni’imtaccen sanyi da ƙamshi suka ratsa ni, Zaunar da ni da Gwoggo Rakiya tayi bai sa na buɗe fuskata ba. Lale lale suke ta yi da maraba suka gaggaisa kafin suka gabatar masu da abinci, sallah suka fara yi. Matan biyu suka yi sallama da su gwoggo bayan sun nuna masu akwatuna masu ɗauke da kayan aurena, suka ce za’a kawo mota a tafi da mu gidansu Ahmad. Wucewarsu su Gwoggo ladi suka zuba abinci. Haj ta miko min nawa na ajiye a gefe sun yi nisa da ci Baba Ramu ta ɗago ta dube ni, “ki ci abincin mana Shuhaina.” Na jawo shi gabana nayi cokali biyu sai na ajiye. Duk da daɗin abincin da kasantuwar ban taɓa cin abinci me daɗin shi ba ji nayi yana shaƙe ni, Saboda halin da nake ciki na ruɗani da tausayin kai, Gwoggo Rakiya ta dube ni,
“Anya Shuhaina ba za ki ci abincin nan ba? To mu dai ci zamu yi gara ke yanzu za ki soma ci, mu kuma gobe gida zamu koma.” Shiru na mata sai dare sannan Ahmad da abokinsa Abdullahi suka zo suka gaida su gwoggo, wani abincin aka kuma kawo masu me rai da lafiya, Suka ƙara ƙona yatsu ga kaji suka karya ƙashi.
Da safe duk da halin da nake ciki sai da na kusa dariya, akwatunan auren da aka gaya masu suke son gani, Sai dai an rasa wadda zata ko matsa kusa da wardrobe ɗin da suke ciki, Wardrobe ɗin gadon ce bango guda Gwoggo Rakiya ta kama baki,
“To abu ne duk gilasai ka ce za ka buɗe ina zaka taɓa? ka je kayi masu barna? Da jin wannan zancen nata ban san sanda nayi dariya ba, kallona ta yi,
“Ja’ira kike min dariya, to tashi ke ki buɗe mana.” Sanin halinta bata wasa da yara yasa na miƙe sai da na gama kallonta tsaf sannan na buɗe masu. Na koma inda na tashi suka firfito da akwatunan Ina jin su suna ta mamakin yawan kayan da kyan su. Sai da suka gama aka yiyyi wanka tsaye nayi cikin bathroom ɗin ina kallon tulin turarukan wanka da aka jibge, a rayuwata Ina matuƙar san kamshi dan haka ban cuci kaina ba, zuzzubawa nayi a ruwan wanka na kwanta cikin bahon wankan, na wanke jikina fes na fito ina ƙamshi, Gwoggo Ladi ta turo min akwatin da kayan kwalliya suke,
“Ki yi kwalliya da su.” Ban musa mata ba na tsinci na tsinta na ɗora su kan tsalelen dressing mirrow da ke fuskantar gadon na yi kwalliya, ita ta miƙo min kayan da suka cire min na akwatin, Atamfa ce da mayafi zuwa su sarƙa da ƴan kunne, hada takalmi na shirya tsaf, kamar jira aka yi masu magana direba ya zo, ba motar jiya ba ce, sai dai direban shi ne Ya kwashe mu zuwa gidan su Ahmad.
Tarba me kyau muka samu daga jama’ar gidan. Sashen mahaifinshi aka soma kaimu, wanda ya yi ta godiya kamar ba babban mutum ba, da suka miƙe ya cika su da kuɗi. Daga nan sai sasan uwargidan shi Haj Babba, ita ma ta cika su gwoggo da kuɗaɗe sai sasan amaryarshi da na ji an ambata da Haj Asmau, itama da suka miƙe kyautar kuɗaɗen tayi masu. Sasan Haj Hadiza mahaifiyar Ahmad ne ƙarshe ta karɓi su gwoggo da mutuntawa. Sun ɗan zauna aka ce su fito, turamen zannuwa ta basu da kuɗaɗe su yi ɗinki.
Su gwoggo suka tafi suna ta godiya, ta dawo daga rakiyarsu ta samu ina share hawaye. Zama tayi tana ta rarrashina ƙarshe ta ƙare da gaya min maganganu masu daɗi akan Amina, na irin halayyarta da daɗin da suka ji basu ni da aka yi bayan rasa ta. Ko ba komai zuciyata tayi sanyi, a yabe ka bayan ba ka ai ba ƙaramin dace bane, Ina tare da ita har dare.
Ta sani nayi wanka ta bani wasu kayan na sa. Sai takwas da rabi Ahmad ya zo, Ce ma shi tayi ya je tare da ni wurin mahaifinsa, Nasiha ya yi mana da muka miƙe kuɗaɗe ya ba Ahmad ya ce ya riƙe min, Ina biye da shi kamar wadda ƙwai ya fashe mawa, har inda ya ajiye motarshi, sai da ya shiga ya rufo na ƙaraso na dan tsaya jim ganin ba shi da alamar ce min ci kanki, yasa na kama ƙofar baya na shiga, har muka soma tafiya bai yi ko tari ba, illa ƙira’ar Sudes da ta ke fita cikin taushi. Da muka isa sai da na ga ya fita nima na balle murfin na fice, ban gan shi a falon ba. Kofofi uku ne a falon, ɗaya wadda za ka shiga ta kai ka ɗakina, ɗayar kuma kitchen za ta kai ka, dan da safe nan na ga me ma shi aikin gida da ban ruwan fulawoyi yana karakaina, ɗayar nake kyautata zaton ɗakin shi ne nawa ɗakin na shiga, na cire kayan jikina katafaren gadon na haye, duk da ni’imar da ke cikin dakin be hana tunani ya dabaibaye ni na yan’uwana da innarmu, wani ɓarayin kuma tsoro ne taf a cikin raina na kwanan da zan yi ni kaɗai, saboda sabo da gidan mu na yawa.
Na raba dare kafin in samu gwanin iya sata ya yi awon gaba da ni. Asuba nayi lokacin da na saba tashi sai na farka, addu’a a bakina na miƙe na kewaya na ɗauro Alwala Na haye prayer mat na ta da sallah, da na idar nan nayi ta zama nayi azkar da karatun Al-Kur’ani, ƙarshe na haɗa kai na da gwiwa Ina tunanin gidanmu da al’amuran mutanen gidan.
Ina nan zaune har gari ya waye sosai, Ba zato na ji an murza ƙofar ɗakin, hantar cikina ta kaɗa, ta da kaina nayi na dubi ƙofar, ya yi kyau har ba magana, Cikin ƙananan kaya farar riga ce da bulun wando, Agogon dura king ɗaure a hannunsa, Sumarsa ta sha gyara sai sheƙi take, cikin abinda bai gaza sakan ashirin ba na ƙare masa wannan nazarin.
Dama mata suma suna yi wa maza kallon ƙurilla irin haka?