Tafiyar awanni kusan biyar ta kaimu Abuja. Mun isa gidan bayan ya tsaya damu a wani Restaurant na sa shi ya amso mana abinci. Sai da ya ci abinci ya yi sallah sannan na sallame shi da alheri mai yawa. Ma’u ta gyara ko’ina dan yarinya ce mara ƙyuya. Baba Kulu ta kira ni ta ce, “Gobe idan Allah ya kaimu tana tafe, dan ƴar ta ta ta samu sauƙi.”
Na ce kawai ta wuto Abuja dan na baro Katsina. Muna sallama kiran Ahmad ya shigo yana shaida min ya yi tafiya zuwa Ibadan in kula da kaina. Haushi na ji ya ƙara turniƙeni. Sai nake ganin kamar tare da Yasmin ya tafi. Na kira Momi da Khausar na shaida masu zuwana. Da daddare na kwanta kafin barci ya ɗauke ni naji abu na bi na,na tashi na ƙara hasken fitila, na duba sai na ga jini, hankalina ya ɗan tashi dan ban taɓa naƙudar jini irin wannan ba, can dai ina sauraron ikon Allah. Abu sai gaba yake, zuwa can ciwo ya taso, na rasa wanda zan kira a wannan dare, da dai naji azaba sai na ɗauko waya Zainab maƙociyata na kira, ta ruɗe cikin shaƙaƙƙiyar murya take tambayata lafiya?
Na ce “Labour nake, kuma ina cikin wani hali.” Aje wayar kawai ta yi ba a ɗauki wani lokaci ba naji bugun ƙofa, ina tafe jini na zuba haka nan na yi ƙoƙari na buɗe, ta rungume ni a jikinta tana, “Ikon Allah da yamman nan da na shigo lafiyar ki ƙalau ammaganar mijinta muka jiyo daga waje yana cewa “Memakon ki yi kokarin taimaka mata ku fito,sai ki tsaya surutu.” Da sauri ta wuce ciki, ta fito da zannuwa ta taimaka min na canza kayan jikina, ta kuma riƙe ni zuwa in da motar mijinta take.
Gaba ya zauna kusa da direba ni da ita a baya, kai tsaye asibiti aka wuce da ni, da gaugawa suka karɓe ni, ni dai kafin a shigar da ni na ɓata lissafina, dan ban san kuma abinda ya ci gaba da faruwa ba. Na farka na gan ni a ɗaki na musamman, dan ni kaɗai ce, sai mutane da na gani kewaye da ni, na bi su da kallo kowa na ta ƙoƙarin gaishe ni. Khausar ta wuce da sauri dan kiran likita, na dubi hannuna,wanda na ji ya yi min wani dundurumdin,ƙarin jini na ga an cire min, na kalli ƙarfen da ke tsaye,wanda ke maƙale da ledar ƙarin ruwa ko jini, sauran ledar jini ke maƙale wurin, sai na tabbatar da ƙarin aka yi min. Ƙwaƙwalwata na ta tunanin har Husna na gan ta a wurin, na shafa cikina na ji wayam,na lumshe idona ina tunanin ko ya Allah ya yi da shi?
Likita ta zo ta duba ni, ta ɗan jima riƙe da hannuna, kafin ta fita, wani barcin ya kuma awon gaba da ni. Washegari na farka da sauƙi ƙwarai, ganin har lokacin ba a ce min ga abinda na haifa ba sai na yanke wa kaina babu shi. Can likita ta zo ta bamu sallama, kasancewar da safe ne, daga ni sai Momi, sai Husna da ta zo da safe, Husna ta shiga harhaɗa kayanmu, Husna na riƙe da hannuna muka fito.
A harabar asibitin sai na hango Ahmad akan motar shi zaune, ganin fitowar mu ya yi saurin tasowa. Ya iso wurinmu ya shiga gaishe da Momi, ta amsa ba yabo ba fallasa, ya yi min sannu, ya ce “Momi ga motata” ta ce “An gode, akwai mota.” Muka shiga yana biye da mu a tashi motar. Ga mamakina sai na ga mun nufi gidan Momi, muna isa ɗakin da na zauna Momi ta kaini, ɗakin na ta fitar da daddaɗan ƙamshi, na haye gadon na kwanta, ta wuce bayi ta haɗa min ruwa, ta umarce ni in shiga in yi wanka.
Na shiga na gasa jikina da kyau, na fito na shirya kaina, cikin wata doguwar riga da ta ajiye min. Shigowa tayi da wani gasashshen naman kaza, jin ƙamshin da ya bugi hancina yasa ni haɗiyar yau, zama tayi tana yanko min,har sai da na girgiza kai, ta miƙe da farantin bayan ta miƙo min ruwa, sai ta fice. Na gyara kwanciya inda tunani barkatai ya yi ta yawo a ƙwaƙwalwata. Ƙarar buɗe ƙofa ya sa na kai ganina wurin, ashe Husna ce, ta zauna kusa da ni tana ƙara tambayata jiki, nan na samu nayi mata tambayar da ke cin raina, na kuma rasa wanda zan ma ita na dai yi ƙarfin halin cewa,
“Wai Husna ya bayanin abinda ke cikina? Idanta kawai na ga ya tara ƙwalla, Aunty Shuhaina kin bani tausayi ƙwarai, dan da ƙyar Allah ya ba likitoci sa’a suka ciro abinda ke cikinki, yaro ne namiji, sai dai ko kuka bai yi ba, dan shima ya sha wuya har ya rasu a ciki, ke kuma sakamakon jinin da ya zuba a jikin ki sai da suka nemi jini dan a ƙara maki, hakan yayi daidai da isowar ya Ahmad, dan an ta shan wuya kafin a samu wayar shi, a taƙaice dai jinin shi aka ƙara maki dan yayi daidai da naki. Yau kwana huɗu kenan da haihuwar ki, ƴan gidanku ma sun zo shekaranjiya suka tafi. Y
Yan’uwanki sun bani tausayi da ƙyar suka tafi sai kuka suke. Na runtse idanuna, saboda nauyin da na ji ƙirjina ya min dan baƙin cikin rasa babyn da na haifa wanda ko ganin shi Allah bai bani iko ba, na share wasu hawaye masu zafi da suka taho min,na shiga maimaita Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musiybatiy wakhlifniy kairan minha.
Ji nayi an haye jikina an maƙalƙaleni, na buɗe idon Junior ne da Amina, cikin uniform ɗin makaranta, na ƙara rungume su ina jin daɗin ganinsu, me kula da su ta zo dan tafiya da su ta cire masu uniform ta basu abinci, da ƙyar ta samu suka bi ta. Momi ta sake shigowa da kwanonin abinci, ta zuba ina kallonta, Cuscus ne da yaji haɗin hanta da ƙoda da kayan lambu sai ƙamshi ya ke, ta miƙo min ban jin sha’awar cin komai dan yadda zuciyata take a ɓace, amma na miƙa hannu na karɓa saboda girmanta da nake gani na soma ci a hankali.
“Ga farfesun naman kai can ko zuwa anjima sai ki ci” Na ɗaga mata kai, sai da ta ga na ci sannan ta miƙe ta fita da kwanonin, ta dawo Haj Babba ta shigo, na gaishe ta ta gaida ni da jiki, ta ce ma Momi “Ai ban san kun dawo ba, zan wuce asibitin direba ke shaida min dawowarku.” Momi ta ce “E an sallame mu saboda yanayin jikinta sai na wuto nan da ita.”
Hajiyar ta ce “Ai hakan ya fi, ga ma mijin nata ba mazauni bane, Allah dai ya ƙara lafiya.” Momi ta amsa da “Amin” ta fita, Momi ta janyo kujara ta gyara zama “Shuhaina” ta kira sunana na amsa a hankali “Meke tsakanin ki da Baba ƙarami? Dan shiru na yi kafin na ce “Ba komai Momi” ta yi duk ƴan dabarunsu na manya ina ce mata ba komai, can ta ƙare ta ce “A ranar da kika haihu ba ki cikin hayyacinki kin ta faɗar abubuwa na zaman ki da Baba ƙarami, Allah ya taimaka daga ni sai ke ne a ɗakin sai ko likitar da ta ƙarɓi haihuwar, dan na kira ta ta gane min abinda kike yi, ta ce min jininki ya hau sosai, dan sai ma da ya sauka aka samu ƙara maki jini, sai na danganta hakan da halin da kike ciki, “Wace ce Yasmin?
Dakyau Allah y kara basira