Skip to content
Part 10 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Ya turo ƙofar ɗakin ya shigo. Na gaishe shi ya ce, “Ki haɗa kayan ki waɗanda kike ganin zaki buƙata zan yi tafiya ne zuwa course kasar Canada na kimanin shekara ɗaya, gobe zan wuce ke kuma daga Airport direba zai wuce da ke gidanku, maybe sai na dawo zan zo in taho dake. Kamar in buɗe baki in ce kawai ba ni takarda ta kayi tafiyar ka, amma kwarjinin shi ba zai iya barina in buɗe baki in yi wata doguwar magana a gaban shi ba, bare har in iya faɗa mishi mara dadi.

“Ina wayar ki? Ya tambaye ni, da hannu na nuna masa dan idan na buɗe baki kuka ne zai fita daga bakina, yasa hannu ya ɗauke ta. “Ban san kowa yasan ba tare dake na tafi ba, dan haka ki kiyaye ki iya bakin ki. Bandir ɗin Kuɗi ya ajiye kan mirrow har guda biyu, “Ki yi amfani da su.” Tun kafin ya bar ɗakin na fara sauke akwatunana, uku na cika, ban kwanta ba sai ɗaya saura, idona kuwa ya ce bai san wani abu barci ba, saboda yadda zuciyata ke ɓace.

Ina idar da sallar asuba na shirya cikin sauri na ja akwatunana zuwa harabar gidan. zama na yi na ta sa su, ba sai na fadi irin suyar da zuciyata ke min ba. Tonny nan ya fito ya same ni, yana gaishe ni tare da tambayata “Madam lafiya kuwa? Murmushin yaƙe nayi na ce “lafiya lau.”

Ya kama aikinsa ina nan zaune. Direba ya zo Ahmad ma ya fito cikin shiri direban ne ya kwashe akwatunan yasa a boot, sannan ya ɗauko na Ahmad suma ya zuba su, Ahmad ne ya zauna a gaban motar kusa da Tunau direba ni kuma ina a baya. Har muka isa Airport ɗin babu wanda ya yi ko tari. Ya sauka ya ɗauki jakarsa, da ƙyar na danne zuciyata na yi masa fatan alheri. Tunau direba na biye da shi a baya sai da suka ɗan yi nisa da motar suka tsaya magana yake masa shi kuma ya ɗan rusunar da kan sa cikin saurare. Ya zo ya ja motar muka bar wurin, muna tafe zuciyata na sake-sake duka wata nawa da yin auren? Ni kunyar yadda ƴan gidan mu zasu ji zancen ya fi damuna lokaci-lokaci ina share kwallar da ke sauko min.

Ana sallar azuhur muka shiga garin Malumfashi. Yan gidan mu na ta oyoyo ga Amarya ga Amarya masu riƙe ni na yi ni dai yaƙe kawai nake kokarina bai wuce in ga na isa ɗakinmu ba, Uwar ɗaka na wuce na haye ƙaramin gado. Duk wanda ya leƙo dan mu gaisa sai Innarmu ta ce; ga ta can uwar daka ta tattake ko bata iso da lafiya ba? Ko ruwa ta ki tashi ta sha wasa-wasa sai zazzabi ya rufe ni mai zafi abin ne ya hadu da yunwa ga rashin barci.

A daren su yayarmu da Ummu suka zo ganina, halin da suka same ni yasa su tafiya da sanyin gwiwa. Yusuf ya sayo min magani amma da zazzabin na kwana, da safe sammakon asibiti muka yi ni da Innarmu wadda har ban san kallon ta in na tuna duk dadin da take ji na ganina, tana jin yadda tafiyar take hankalin ta zai tashi.

Na ga likita ya yi min tambayoyi kafin ya tura ni gwajin jini, mun jima kafin nan aka fito da sakamakon, likitan da kansa ya faɗa min ina ɗauke da juna biyu na wata biyu sai na sa kuka kawai Innarmu ganin ina kuka ta balbale ni da faɗa, to shege ne da kike neman tara mana mutane? Ki samu a cikin zargi ga duk wanda ya ga kina kuka.

Dole na yi shiru amma kar ka tona zuciyata haka muka dawo gida. Ranar da na samu kwana hudu na wartsake Innarmu ta tasa ni gaba dan jin damuwata dan ta ce Ta lura ba wai ciwon kadai ke damuna ba, ina da wata mas’alar ta daban. Ban yi ko dar ba na bata labari dan an ce ba’a boyewa abokin kuka mutuwa, sosai jikinta ya yi sanyi sai dai ta horan da in maida al’amarina ga Allah babu abinda ya gagare shi.

Da safe ta kira kannen babana ta mai da musu yanda aka yi, dukkan su alhinin su suka nuna Illa Baba Ya’u da ya kwakwkwara min zagi wai an kai ni inda zan huta har suma su huta na yi halin tsiya an koro ni.

Ranar maganar ta kewaye gidan wuni aka yi kowa na fadin albarkacin bakin sa. Tuni ni kuma na rasa nutsuwa da kuzari da zarar na tuna cikin da aka ce ina dauke da shi sai in rasa inda zan sa kaina Lokuta da dama sai in rika zargin kaina kila da na bi shawarar Khausar da ba wannan labarin ake ba. Sai kuma Inna tuna bawa bai kubce ma kaddarar sa. Ga ciki me kwashe kwashe yanzu kuma ya tashi daga san tuwon dawa ya koma ina ganin abincin mutanen gida sai in ji miyau na ya tsinke ban ankara sai dai in ji miyau na na zuba kasa sai ka ce wata mayya sai in shige daki duk da dama ba wani fitowa na cika yi ba.

Na samu Yusuf ya na cigaba da karatunsa kudaden da aka ba innarmu na gadon Amina Yahaya aka ba dan wajen Baba Sani wanda tun kafin rasuwar Babanmu dan dakin innarmu ne, haka bayan rasuwar shi yana temaka mata da abinda ya samu. To yana da shago, sai kudaden jama’a su ka karye masa. sai ya zama dan abinda ya rage da shi ya biya mutane, Innarmu ta ce Yusuf ya fito da kudin a ba shi ya tada shagonsa, to anan ake samun na cefane, shima ya yi hidimar iyalin sa da yake yana da mata da yaro daya, Yusuf ma yana dan hidimar karatunsa. Kudin da na zo da su ma bayarwa nayi aka kara ma shagon.

Kwanci tashi ciki na ya yi girma bai fito ba sai ya bi jikina Innarmu duk yadda ta ga na shiga damuwa sai ta yi ta gaya min kalaman kwantar da hankali har in samu nutsuwa. Sai dai lafiya ta ki min, ko da yaushe muna hanyar asibiti Likitan ma sai da ya ce ma Innarmu, “Yarinya karama kamar wannan me ke sa ta yawan tunani ga shi a yanda ya nuna jinin ta yana gab da hawa ga hawan jini hatsari ne ga me ciki.”

Da kansa zai rika lallashi na, su yayarmu ma basu daukar lokaci suke zuwa duba ni wai tausayi nake basu. Mutanen gidan mu kuwa har mamaki suke ba ni kiri kiri innarmu ta hakura da zaman tsakar gidan, dan da ta zauna za ka ji ana sakin maganganu wanda duk me hankali zai gane da ni a ke. A haka har cikina ya kai watannin shi ranar wata juma’a na tashi da ciwo tun safe ban samu kaina ba sai azahar inda na samu santaleliyar yarinya wanda duk ya gan ta sai ya fadi tubarkalla. Kamar ta daya da Anty Amina dan duk wanda ya san Amina sai ya jinjina kamar su. Kan ka ce me sun gyara ni ni da yata. Cikin rufin asiri kwana biyar kafin nan Ummu ta yo min sayayyar su kayan sanyi kayan jarirai su pampers. A duk sadda na zauna daki ni daya Sai in ta kallon jaririyar Ina jin tausayin kaina ko yaya rayuwata ta gaba za ta kasance? Da innarmu ta tambaye ni, Ko ina da sunan da nake so a sanya ma yarinyar? Sai na ce “Amina” jikin ta na ga ya yi sanyi ta fice.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 9Canjin Bazata 11 >>

2 thoughts on “Canjin Bazata 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×