Skip to content
Part 9 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Ya amsa cikin yanayin shi da har na soma sabawa, ya wuce cikin sauri, a sanyaye na shiga daki tare da dana sanin fitowa ta a haka, sai na nemi yunwar da na ke ji na rasa, da kyar na karya.

Wunin ranar sai na samu kaina da jin kunyar kaina saboda tunanin yadda ya gan ni. Sai da nayi sallar isha’i sannan na shiga wanka Kan stool na zauna ina goge jikina da tawul na busar da gashin kaina da (Hand dryer) na mulke jikina da mayuka kala kala ina tuna Khausar, “Allah sarki masoyiya ta hakika alherin Allah ya kai ma ki.”

Ina murmushi na fara shafa humrorin da ta kawo min masu matukar kamshi mai sanyaya rai, jikina har ya kama kanshin, na tsura ma jikina ido ta madubi, ko ba’a gaya min ba na san na samu sauyi me yawa, fatata ta dada gogewa tayi lukui lukui. Duk da dai dama fatar tawa me laushi ce, da wani sheki da kawayena ba su gajiya da tanbayata man da nake shafawa, in na ce Vaseline babu me yarda, sai su ce ban san gaya masu ne kawai.
Mikewa na yi na sa kayan barci na riga da wando ne rigar guntuwa ce Iyakacin ta cibi wandon iya gwiwa Skin tight ne sun lafe da fatar jikina na koma jikin window ina leka yadda ruwan sama ke sauka kamar da bakin kwarya ajiyar zuciya na saki dan ni kam ina son ruwan dare sai in ji dadin barci na koma kan stool na zauna ina kallon kaina ta madubi. Wai a haka Khausar ke son in rika fita gaban Ahmad ba zan iya ba na fadi a raina. Jin turo kofa ya sa gabana faduwa Ahmad ne cikin jallabiya fara sol na dukar da kaina na gaishe shi. Ban ma yi tunanin amsawar shi ba, ban san me yake ciki ba ji na yi kawai an wurga ni bisa gado, kan in yi yunkurin mikewa ya biyo ni, ban san al’amarin babba bane sai da na ji ya raba ni da kayan jikin, ban kuma tsinkewa ba sai da na ji azaba ta ratsa ni, tabbacin cewa abinda na ke ji yana faruwa ga sauran mata to ni ma ya iso gareni yau. Ban san iya lokacin da ya dauka yana abu daya ba, abinda na sani dai na yi kuka har na ji ba dadi kafin ya hakura ya bar min dakin.

A haka na kai asuba, ina tuna abubuwa kala kala sai da na gyara kaina a bathroom sannan na fito na yi sallar asuba na koma na tattake to rannan fa ban tashi ba sai sha biyu shima yunwa ce ta tashe ni. Gogan kuwa ya ma bar gidan.
Tun kuma ranar ban kara ganin sa ba, sai dai in ji shi, a yanzu sai takaicin sa ya fi yawa a zuciyata. Sau da dama zan ta zubda hawaye ina tuna abinda ya faru tsakanin mu, Sai in rika tunanin dama abinda ya kawo shi wurina kenan, Yana samun biyan bukatar shi dakin da nake ma bai ishe shi kallo ba, ya cuce ni ya maida ni second hand wannan wace irin kiyayya ce ya ke min? Ina yawan tanbayar kaina hakan.

Mai zai faru? Ana cika wata guda da faruwar hakan a tsakanin mu, ba sai na tsinci kaina cikin wani irin lalaci ba baki na ba dadi komai zan ci ba ya zama sai zuciyata ta yi ta tashi abinda nake so nake marmari tuwon dawa miyar yauki. Tonny shi ya yi aikin sawo ta da nikanta ban jira kudin Ahmad ba da na hannuna na yi amfani. Sai ko Apple da ban gajiya da cin shi idan na gama tuwon nan miyau na zan ji har yana tsinkewa kafin in fara ci da haka na soma tunanin to wai meke damuna. Wani sashen na zuciyata na rada min ko dai ciki na samu gabana ya yi saurin yankewa ya fadi na yi saurin ture zancen tare da karfafa zuciyata da ba yanda za’a yi daga sau daya hakan ta faru, amma kuma ban ga al’adata ba, hakan ba damuwa ba ce dan a gida na kan shafe wata hudu ban yi ba, wancan watan kuma na yi, dan in ban manta ba kwana biyu ne da gamawa ta Ahmad ya shigo dakina. Sai nake ta kara ma kaina kwarin gwiwa da cewa yanayi ne kawai na yau da kullun idan kana yawan cin abu ka ji ya ishe ka.

Wata biyu bayan nan Momi mahaifiyar Ahmad tayo min waya kanwar Ahmad da suke uba daya ta haihu, ita ce yar farko wurin Anty Amarya har jibi suna, in yi kokari ya kai ni. A suleja ta ke aure. Sai na ce “Ko za ta gaya masa? Ta ce shi kenan, Na aiki Tonny ya sawo min turmin zane da rigunan jarirai masu kyau guda biyu zan kaiwa me jego, gaskiya ba kadan nake gode ma Abdullahi ba dan duk wani kudi da zan kashe shi ke bani matukar ya zo gidan zai min Alheri hakan ne ya taimaka min yin duk abinda na ji Ina bukata.

Ranar suna da misalin karfe goma na fito cikin kwalliya atamfa ce aura sai na sa farin hijab da takalmi da jaka. A mota na same shi kamar an buge shi dan mugun hada ran da ya yi. Ni dai na balle murfin motar na shiga har muka isa bai ko kalli wajen da nake ba waazin Sheik Jafar Adam yasa a CD motar gidan da muka je katon gaske ne irin na masu da shi sauke ni kawai ya yi ya wuce abin shi.

Kamar ba gidan suna ba masu aiki ne kadai ke ta shawagin su daya daga cikin su ta yi min jagora zuwa wani katafaren falo ta ce in zauna in jira hajiya bata fito ba tukuna. Na zauna har zaman ya gundure ni, bakin ciki ya kama ni, dama ya san ba’a fara sunan da wuri ya kawo ni ya shanya? Karfe daya na yi na nemi daya daga cikin yan aikin ta nuna min makewayi na zagaya na yi Alwala na yi sallah a falo, aka rika shigo da manyan kuloli na abincin da aka yi oda dan bikin sunan, a wata runfar shan iska da ke harabar gidan wata cikin su ta tanbayan abinda zan ci na ce idan akwai tuwon amala miyar yauki ta kawo min, ta ce “Drinks fa” Na ce, “Exotic is ok” Ta hado min hada robar ruwan faro na ci fiye da tunanina.

Kamar jira ake in gama, me jegon ta fito sai yauki take an sha kwalliya Ko ta ina sheki take na ganeta dan ta taba zuwa gida na kuma sunan da na ji Ahmad ya kira ta da shi Rufaida Sama sama muka gaisa Na yi mata Barka Da bata abin da na kawo mata da kyar ta motsa labbanta ta ce, ta gode mun zauna zaman kurame mutane suka fara zuwa kowa ya zo bai dadewa zai juya ko ganin ba ni da niyyar tafiya ta kira dan’uwan ta a waya ce mata ya yi in har ba wanda zata sa ya kawo ni to ta bar ni nan yar dariya irin ta su ta miskilaye ta yi, “Kai ma yaya ka nuna rashin bukatar ta bare ni ni me za ta min zan roki masu tafiya wasu su dan sauketa.”

Abin ya sosa min rai cin fuskar ya yi yawa, mata kuma sun yi biyar wa’anda ta yi wayar a gaban su. Wata hamshakiyar Hajiya tayi ma magana ta ce, “Ba matsala” Matar me mutunci na yi na yi ta sauke ni bakin asibitin ta ki sai da ta kai ni har kofar gida. Na yi mata godiya ta ce, “Ba komai”.
A ranar dai barci gaza daukata ya yi saboda bakin ciki.

Da gari ya waye kirana ya yi da miskilallar muryar sa “Ki shirya zan kai ki gidan mu.” Hakan aka yi sai da muka fara isa sashen mahaifin shi sannan na hajiya Babba, Hajiya Asmau anty amarya kenan Maaikaciya ce ba mu same ta ba. Muna zaune gaban momi sai tanbayata take “Babu abinda kike bukata idan kun je can? Duk da dai akwai abubuwan da na tanadar maki Sai idan zaku tafi sai ki wuce da su” Ni dai kaina a daure yake. “To wai ma ina zamu?” Ta ce ma Ahmad su waye masu maku rakiya airport saurin cewa ya yi “Jirgin safe za mu bi, na dai yi wa tunau direba magana zai zo ya kai mu dan haka mun hutar da kowa.” Ta ce “To ka kula da yar mutane amana ce a hannunmu suna ta firar su Ina sauraren su da ya tashi tafiya Ya ce in tashi muje.

Ta ce “A’a yi tafiyar ka zan sa a kawo ta, bayan ta gama min wuni.” Haka muka wuni tana ta ji da ni. Sai yamma likis ta sa aka mayar da ni gida.

Na fito wanka ina daure da tawul guntu daga kirji zuwa cinyoyi rigar da zan sa in kwanta nake nema.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 15

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 8Canjin Bazata 10 >>

1 thought on “Canjin Bazata 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×