Skip to content

Cikin Baure 1

Part 1 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

BismiLlahi rRahmani rRahiim

Wannan lttafi kirkira ne, ban yi shi don cin zarafin kowa ba.

Tunda na shigo layin nake jin kamar na shiga ɗaya daga cikin gidajen cikinsa, ko da Allah zai sa na ga wanda na daɗe ina dakon soyayyarsa a cikin zuciyata.

Dan dakatawa na yi da tafiya tare da jefo ma kaina tambaya “Toh idan na shiga gidan na ce me?”, domin na kasa samun k’aryar da zan shirga ma matar gidan idan na samu sa’ar shiga, saboda ba sosai na shak’u da ita kamar sauran matan unguwa ba, kawai dai na kamu da ƙaunar mijinta ne, har nake ganin rayuwata zata k’are a garari idan ban same shi a matsayin miji ba, duk da kuwa mako d’aya ya rage a d’aura aurena.

Cigaba na yi da tafiya a hankali, duk da ina da yaƙinin Aunty na can tana jira na, domin sai na kai waken da na siyo ne za a girka mana abincin rana.

Tafe nake gami da sak’awa da kwancewa a raina, kwatsam! Sai wanda nake muradin gani ya hutar da ni daga jidalin shiga gidansa, domin kuwa hango shi na yi ya fito ta k’aramar k’ofar katafaren gate d’in gidansa mai d’auke da ado.

Sanye yake cikin farin yadi, kansa kuma d’auke da bak’ar dara, wadda take k’ara ma fuskarsa da na daɗe ina satar kallo kyau da kwarjini. A dalilin son da nake mishi ne na fahimci ba abin da ya kai ganin masoyi sanya farinciki a zuciya, domin kuwa tuni yalwa ta samu mazauni a fuskata.

Cikin wani irin salo wanda nake sa ran zai d’auki hankalinsa na cigaba da takowa, shi kuwa a yadda na lura kamar ma bai ganni ba, saboda idanunsa na kan wayarsa da nake zaton iPhone ce.

“Allah ka sa ya kalle ni”, na fad’a a lokacin da na zo dab da shi.

Rufe bakina kenan Allah mai jin roƙon bayi ya karb’a addu’ata, ta hanyar jefo tagwayen kiran da suka rabu a cikin wayoyinmu ni da shi, take suka ɗauki rurin da ya yi sanadiyyar sark’ewar idanuwanmu a cikin na juna. Ras! Na ji gabana ya faɗi, don ban taɓa ganin ƙwayar idanunsa ba sai yau, tare muka d’auke idanuwanmu, shi ya maida nashi a kan waya, wadda sautinta ya ƙara tabbatar mini da Iphone ɗin ce. Ni kuma na wuce ba tare da na fiddo wayata keypad mai ɗaurin gaba da Lobaree ba.

Cike da farincikin sa’ar da na taka na ce a fili “Farin masoyi mai farar aniya”, bayan na sauke ajiyar zuciya kuma na ɗora da faɗin “Allah ka ba ni shi”, saboda tamkar auren jeka na yi ka na ɗauki Aurena da Abbas da ake shirin d’aurawa.

Alhaji Nasir kenan! Wanda duk Jama’ar da suka san shi suke mishi lak’abi da Alhaji Nas. Matashin mai arziki ne da baya ƙyashin jama’a su mora, domin duk wata buƙata idan ta taso wurinshi ake zuwa, kuma cikin ikon Allah bai hana abin da aka je nema. Sosai ya ke samun kyakkyawan yabo a wurin mutane. Yabon ne kuma da tarin dukiyarsa suka haɗa hannu wurin tsunduma ni a kogin soyayyar shi.

Yana da mata d’aya da kuma yara hud’u duk mata, kuma itama matar ba laifi ana ɗan yabon ta, duk da bata cika shiga jama’a ba.

Ni kuwa Asma’u marainiyar Allah ce, ina zaune a wurin babbar yayarmu da ta ɗauko ni tun bayan rasuwar mahaifiyarmu. Mu ɗin talakawa ne waɗanda ba don sana’ar Cicin-bread da Aunty take yi ba, da tuni ci da sha sun gagare mu. Amma a haka na d’auko ma kaina rigimar son wanda ko ƴar aikin gidansa ba zai ɗauke ni ba, saboda ba wata tsaftar kirki gare ni ba, sai yanzu ma ne nake d’an kula da kaina duk don na kutsa kai a rayuwarshi.

Da tarin farincikin ganin Alhaji Nas na isa gida, a d’an matsakaicin tsakar gidanmu mai ɗauke da d’akuna uku na taras da Aunty, zaune take a kan tabarmar da yara duk sun tsige kusan rabinta sun yi wasa. Kujerar da ke gabanta na jawo na zauna, lokaci d’aya kuma na aje mata waken dana siyo a kan tabarmar.

Jawo ledar waken ta yi tare da bud’ewa ta duba ciki, d’ago fuskarta mai cike da yalwa ta yi tare da duba na ta ce “Yau kam an samu wake mai kyau, ba kamar na jiya ba da Aliyu ya siyo”.

Ce mata na yi “Ai ba wuri d’aya muka siyo ba”, ta ce “Da alama”, shagon da na siyo waken ta buk’aci na fad’a mata ko da zata aiki wani idan bana nan.
Tashi na yi na nufin kwandon wanke-wanken da ke kusa da ƙofar shiga kitchen, roba da faranti na d’auko na zo muka cigaba da tsintar waken a tare. A nan ne take fad’a mani wai Abbas ya kira ta yanzu ba da daɗewa ba.

Jin sunan Abbas na d’aya daga cikin abubuwan da ke ƙona mani zuciya, domin ban d’auke shi mutum ba ma bare har in iya rayuwar aure da shi, Saboda Nas ne zab’in raina ba shi ba.

Raina a d’an ‘bace na ce “Shi dai bai da hak’uri wallahi, daga kirana ban d’aga ba har ya kawo miki k’ara?”. Girgiza kai Aunty ta yi “A’a ba k’ararki ya kawo ba, ya ce dai idan kina kusa a ba ki”.

“Auho! Ni ban son nacin tsiya”, na fad’a tare da turo baki.

Tambaya mai cike da tuhuma Aunty ta jefo mani, don tuni ta lura da yadda nake fad’in magana gatse-gatse idan an ambaci Abbas “Toh me ya hana ki d’aga wayar ma?”.

Wayata da ke kan skirt na d’aga tare da nuna mata “Dubi wayata fa duk ta sha d’aurin gaba da Lobaree. Ni wallahi ba zan iya fiddo ta a gaban mutane ba”.

Wani irin kallo Aunty ta yi mani “Hu’um, d’anwake ka fi ubanka, wani ma ko mai d’aurin gaban bai da ita”. Ko da na ga bata goyi bayana ba sai na yi shiru.

Nasiha ta cigaba da yi mani da in kasance mai godiya da abin da nake da shi. Kuma ai komai ya zo k’arshe tunda aure zan yi, duk abin da nake buk’ata mijina zai yi mani.

Sosai na ji nasihar, amma ban gamsu da cewar mijina zai yi mani komai ba ta hanyar fad’in “Aunty anya Abbas zai iya yi mani komai, ki duba wayar nan ‘yar ya yi ya kasa siya mani”.

Cewa ta yi “Bakya gani hidimar aure yake, ki bari ya gama komai ki ga idan bai chanja maki ba”, Aunty ta fad’i haka ne saboda ta san waye Abbas a wurin son kyautata ma duk mai hakk’i a kansa.

Duk yadda na so kushe Abbas ban samu goyon bayan Aunty ba, hakan ya sa na chanja hirar.

Muna gama tsintar waken na tashi na wanke a bakin rijiya, kitchen na wuce na had’e waken da surfaffen geron dake cikin roba na juye a tukunyar da ta dad’e da tafasa a kan wuta.

Gero da wake na d’aya daga cikin abincin da muka fi girkawa, sai kuma taliyar hausa da kuma tuwo. Duka wad’annan abincikan uku sun fita kaina, ga shi kuma da alamu ko na yi aure ba zan fasa cin su a gidana ba.

Wayata da na bari kan tabarma ce ta fara sabon ruri, ban yi wani hanzarin zuwa d’aukarta ba don na san Abbas ne mai kiran.

“Asma’u wayarki fa”, Aunty ta fad’a cikin d’aga murya.

Fitowa na yi, kafin na k’araso ma har kiran ya tsinke, kan kujerata na koma da zama ina jiran shigowar wani kiran na Abbas.

Muna nan zaune d’aya daga cikin almajiran da ke yi ma Aunty tallar cicin ya dawo, daga ni har Aunty mun yi murna da ganin bokitin tallar empty.

Aunty na dariya ta ce “Kin ga d’an albarka har ya siyar”, almajirin na dariya shi ma ya ce “Iro ma na hanya, don ya kusa sayarwa shi ma”.

Cinikin da ya yi ne ya juye mata a gabanta, wanda kuma k’ananun kud’i sun fi yawa a cinikin saboda ‘yan makaranta ke siye.

Turo mani su Aunty ta yi a gabana “K’irga mu ga nawa ne”, d’an maraircewa na yi don ban iya ƙirgar k’ananun kud’i ba, ce mata na yi “Don Allah ki k’irga da kanki”, tunawa da shirmen da nake mata ne ya sa ta janye kud’inta ta cigaba da k’irgawa ita da Almajirin.

Daga can kitchen na jiyo zubar ruwa cikin wuta, da hanzari na je kitchen d’in na bud’e tukunyar, sannan na gyara wutar na fito.

A wannan karon ban zauna ba, daga tsayen da nake na ce ma Aunty “Da ma kin ƙara cicin d’in ko na rabin tiya ne tunda ana siye sosai”.

Nisawa Aunty ta yi domin hidimar bikina ce yanzu gabanta, saboda duk lokacin da na ce ayi wani abu na kud’i sai ta ce “Bari a gama hidimar aurenki”, yanzu ma abin da ta fad’a kenan, wanda ya yi sanadiyyar kawar da murmushin da ke fuskata, a raina na rik’a jin dama wanda na mutu akan son shi ne zan aura.

Murmushin yak’e na yi tare da faɗin “Aunty kina ji da auren nan”, tana dariya ta ce “Ba dole na ji da aurenki ba Asma’u, Allah dai ya bamu yadda zamu yi”.

“Amiin” na fad’a tare da duban wayata da ke ta ruri, d’akin mu na shiga wanda ba komai cikinsa sai lak’umammiyar katifa da jakunkunan kayanmu. A kan katifar na kwanta lokacin wayar na a kunne na, ko kusa ban ji me Abbas ke fad’a ba don ba cikin nutsuwata nake ba sadda ya ce “Hello Asmy, bakya ji na ne?”.

Idan akwai abin da na tsani ji daga bakin Abbas shi ne “Asmy”, shi a dole sai ya birge ni da soyayya, bai san duk shirme na d’auki abin da yake yi ba.

Amsa na ba shi ba tare da tausasa murya ba “Eh yanzu ina jinka, amma d’azu sam!”.

Daga can ya ce “Okay, d’azu ba ki d’aga kirana ba, na kira Aunty kuma ta ce bakya nan”.

“Umm bana kusa da wayar ne, sai da na dawo take fad’a mani”

“Shi ne kuma baki neme ni ba Asmy”.

Baki na turo tare da dalla harara kamar yana ganina, cewa na yi “Ba kati fa a wayata”.

‘Dan shiru ya yi, daga bisani ya ce “Ayya, bari to na turo maki. Dama so nake na ji me zaku shirya ke da k’awayenki ne na auren”.

Auren da ban d’auke shi serious ba, ba tsiyar da zan yi a cikinsa, cewa na yi “Ni ba abin da zan yi fa”.

Maraicewa ya yi “Haba Asmy! Sai ka ce bikin mutuwa? Ki fad’i duk abin da kike son yi Insha Allahu zan k’ok’arta”.

A gadarance na ce “Duk abin da muke so fa?”, ya ce “K’warai, madamar bai fi k’arfina ba”, cewa na yi “Yanzu na ji batu, idan na yi nazari zan neme ka”, ina fad’in haka na datse kiran.

Bayan ‘yan mintoci kad’an ne ya sake kira na, ina d’agawa ya shiga yi mani k’orafin datse mashi kira, k’arya na yi mashi cewar batterin wayar ne ya zame, ko da jin haka sai ya sarara mani. Ya so mu yi hira, amma na ce girki nake, ba don ranshi ya so ba ya tsinke kiran, cikin abin da bai fi minti biyar ba katin d’ari biyu ya shigo a layina na Airtel.

Abbas na so na, ni kuma Alhaji Nas nake so da k’auna.

Auren shi ma da zan yi umurnin Aunty ne kawai, amma ko kad’an bana k’aunarsa don bai da arzki irin na Alhaji Nas, sannan bai iya wankan shaddoji irin na Alhaji Nas ba. Kullum dai zaka gan shi cikin yadinsa wanda ake ma lak’abi da Yishirunka Maraya, shi ya sa na matuk’ar raina shi, duk kuwa da irin kulawar da yake bani wadda bata wuce k’arfinsa ba saboda lebura ne, yana aiki a wani k’aramin kamfanin block da ke can unguwarsu, kuma da d’an abin da yake samu ne yake taimakon mahaifansa, kuma a ciki ne yake tara kud’in aurena, har ta kai ga ya gina mana k’aramin gida da kuma lefe.

Batun soyayya kuwa daidai gwargwado yana nuna mani, sai dai ni ban taba kallon shi a matsayin masoyi ba, bare har na ‘bata lokacina wurin gwada mashi soyayya, ya sha yi mani koken me ya sa bana son kula shi? Shiru ita ce amsata, domin idan na fad’a mashi Alhaji Nas na yi ma tanadin soyayyata ba zai ji daɗi ba.

Gyara kwanciyata na yi akan katifar, lokaci d’aya kuma na shiga duniyar tunanin da ke sa ni nishad’i. Ba kowa nake gani a k’wayar idanuna ba sai Alhaji Nas. A yau da muka kalli juna ne na fahimci tarin sirrin dake cikin kallon k’wayar idon masoyi, domin a yanzu ji nake soyayyarsa ta k’ara k’aimi wurin bin duka sassan jikina.

A hankali na bud’e idanuna da ke lumshe na ce “Ina son ka Alhaji Nas, kai ne zabin zuciyata. A fili na cigaba da sambatun soyayyar da nake mashi. Aunty kuwa ta d’auka waya ce muke da Abbas, mafarin tana gama lissafin kud’inta ta koma kitchen.

Bani na fito daga d’akin ba sai k’arfe d’aya saura, shi ma yara ne suka dawo daga school, kuma hayaniyarsu ba zata bari na yi tunanin Nas ba cikin kwanciyar hankali.

Yajin da zamu ci gero da waken na daka, bayan na kai shi kitchen ne na yi alwala tare da gabatar da sallar azuhur, bayan na gama kuma muka ci abincin rana.

Sosai Aunty ta lura da yadda nake yawan yin shiru, wani lokaci fara’a ta biyo bayan shirun, toh a lokacin ina tunanin Alhaji Nas kenan.

Da zaran na had’e fuska bayan shirun kuma toh Abbas ne nake tunani, ina lura da yadda take satar kallo na, amma dai bata yi mani magana ba.

Da yamma ne na shirya ni da k’awata Khadija muka tafi raba katin Aurena ga k’awayenmu, amma fa ba da son raina ba aka yi rabon katin, ina yin basaja ne kawai domin bana son kowa ya gane abin da nake ‘boyewa a cikina.

Bayan mun dawo ne a Napep muka had’e da Alhaji Nas, shi zai fita unguwar, mu kuma Napep d’in mu ta shigo.

Gani na yi mai Napep d’in ya russuna kai tare da fad’in “Ya Hajj”.

Cike da so na kalli Alhaji Nas lokacin da ya d’ago ma mai Napep d’in hannu yana dariya.

Bayan ya wuce ne na tambayi mai Napep d’in “Ka san shi ne?”.

Cewa ya yi “Yo a garinnan waye bai san Alhaji Nas ba, yana da kirki sosai”.

Wannan yabo da aka yi ma Alhaji Nas sai na ji tamkar ni aka yi mawa, maganarsa muka cigaba da yi da mai Napep da kuma Khadija har muka zo k’ofar gidanmu.

Zuciyata cike da k’aik’ayin son Alhaji Nas na shige gida, Khadija kuma ta wuce gidansu saboda magrib ta k’arato.

A wunin yau sau biyu na ga Nas, aikuwa cikin dare na nemi bacci na rasa, ba abin da zuciyata ke yi sai k’una domin soyayyar da nake ta ɓangare d’aya ce, ma’ana ni kad’ai ke fangimata a soyayya ba tare da ya sani ba, kai ko ya sani ma aikin banza nake tunda aure zan yi.

Idanuna dake bushe na d’an lumshe, hannuna dafe da k’irji na ce “Allah ka agaza mani. Ina son Nas, son da ba zan iya kula da Abbas ba idan mun yi aure”, wani irin gululun bak’inciki ne na had’e tare da tashi zaune. Da rugwgwar wayata na haska su Nafisa da ke ta baccinsu a natse.

A raina na ce “Su fa basu da damuwar komai”, cike da tausayin kaina na ce “Allah ni ma ka yaye mani damuwata, ka sa wanda nake yi don shi ya lura da ni”.

Washe gari kuwa nake tambayar Aunty “Wai kam an gayyaci Aishar Nas?”, domin na d’aukar ma raina yau sai na shiga gidan.

Cewa ta yi “Kin ta’ba ganin ta zo gidannan?”.

Kai na girgiza “A’a”, ta ce “Toh bamu kalar dangi, kin san masu kud’innan warinmu suke ji mu talakawa”.

Kariya na shiga ba Aishar Nas, inda na ce “Kai Aunty, ita fa ba haka take ba”, cewa Aunty ta yi “Toh shikenan”.

Nafisa da ke d’aki ta kwad’a ma kira akan ta zo ta kai ma Aishar kati, Nafisa kuwa na zuwa ta ce ita bata son shiga gidan. Aunty na dariya ta ce “Toh Nafisa bata zuwa dai, sai dai ki je da kanki”

Maso zuwa birni bare Sarki ya aiko kira, ban wani binciki dalilin Nafisa na k’in son zuwa gidan Nas ba na ce “Na ji zan kai”.

Ban tsiri zuwa kai katin ba sai da na tabbatar da ya dawo gida cin abincin rana. Knocking k’ofar na shiga yi a hankali, aikuwa na jiyo muryarsa mai dad’i a wurina yana tambayar “Waye?”.

Gira na d’age sama ina dariyar murna, lokaci d’aya kuma na ce “Ni ce…”

Bookmark

No account yet? Register

Cikin Baure 2 >>
Share |

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.