A soro ya kafe mashinɗinsa kana ya shiga gidan. "Abbas ne?" Aunty ta faɗa, lokaci ɗaya kuma tana karantar yanayin fuskarshi, da dariyar yaƙe ya bata amsa da "Eh ni ne Aunty", hakan ne ya yi sanadin faɗuwar gaban Aunty, domin duk wanda ya san Abbas, toh zai iya banbance yanayinsa a halin farinciki ko baƙinciki. Jiki a mace ta yi mashi iso a ɗakinta. Kan tilon kujerar dake ɗakin ya zauna, ita kuma ta zauna gefen gado suna fuskantar juna. Cike da girmamawa ya gaishe ta, amsawa ta yi tare da tambayar shi Asma. . .