Skip to content
Part 11 of 26 in the Series Da Magana by Matar J

Misalin karfe biyar da rabi na yamma, muna kitchen tare da Aunty, abincin dare muke hadawa, lokaci daya kuma ina ba ta labarin abin da ya faru dazu.

Dariya take yi sosai, wanda ni ma nake taya ta lokaci daya kuma Ina shafa kumburin da ke goshina, knocking din da aka yi ne ya sanya mu dakatawa, lokaci daya kuma na nufi kofar.

A tsorace na ja baya lokacin da na bude kofar na ga Ya Azeez da Ya Naseer tsaye, jikin Ya Azeez duk jini, ga bandage a dantsen hannunsa na hagu, sai nevy blue din shirt din Shi da ya sagala a kan kafadarshi ta dama, fara ƙal din vest din sa jangab da jini, yayin da aka nadeta kadan daga kasa, don ba ciwon da ke gefen cikin shi damar shan iska.

Da wata irin murya mai firgitarwa na rika kwalawa Aunty kira.

A rude ta fito hannunta rike da ludayin miya, zuwa lokacin tuni su Ya Naseer sun yi hanyar dakin Ya Azeez.

Da alama ta hangi abin da nake son fada mata, shi ya sa kai tsaye ta doshe su a firgice.

Lokacin da na shiga dakin ne na samu Ya Naseer na cewa “Fada suka yi da wani shi ne yaran wancan din suka yanke shi”

Da wata irin firgita Aunty ta ce”Suka yanke shi? Suna ina yanzu?”

“Bamu sani ba, amma su Anwar sun yi report wa ƴansanda, kuma suna tare da police din suna neman su.”

“Wane policestation ne?”

Aunty ta tambaya bacin rai shimfide a kan fuskar ta.

Lokacin da Ya Naseer yake fada mata address din station din, gefen ciwon Ya Azeez din take tabawa.

Kafin ta mike tsaye tare da fadin “Ko wane lokaci Naseer muna gargadinku, ku san da su wa za ku yi mu’amala, ba ku san halin wasu ba, yanzu wannan yankan da ke gefen cikinshi da ya shiga ciki Allah ka dai ya san abin da zai faru. Amma wlh ni ba zan yarda da wannan ba, Sai na tabbatar an hukunta yaran nan, abu da ba dasu ake fadan ba. “

Ta karashe maganar da fadin” Je ki kawo min wayata Maryam da ruwan zafi, hade da towel”

Na juya jiki ba kwari, ba jimawa na kawo mata duk abin da ta bukata, Hammah ta fara kira ta shaida mishi, ina jin yadda hankalinsa ya tashi, rai a matukar bace yake fadin ko cikin uwarsu yaran suka koma sai an kamo su, an kuma hukuntasu daidai da abin da suka aikata.

“Je kawo min detol” cewar Aunty bayan ta sauke wayar

Toilet din Ya Azeez na shiya hade da dakko mata detol din, a ruwan zafin ta sanya, ta shiga gogewa Ya Azeez din jiki, lokaci daya kuma tana yi masu fada, wani lokacin kuma ta juya kan batun lallai sai a hukunta yaran nan hankalinta zai kwanta. Domin a tauna tsakuwa aya ta ji tsoro

Sai da ta gyara mishi jiki tsab, sannan ta cewa Naseer ya kai ta police station din, ni kuma in zauna gida in karasa abinci.

Jiki a sanyaye na koma kitchen, cikin rashin kuzari nake komai, yayin da hankalina kaf yake a kan Ya Azeez din, daga karshe dai dakin na koma, kishingide yake a kan gado, shigowa ta ce ya sanya shi bude idanunshi da suke lumshe hade da jan wani dogon tsoki, alamun ya yi nisa cikin tunanin da yake yi

“Sannu Ya Azeez, kana bukatar wani abu ne in kawo ma?”

Kafin ya amsa wayar shi da ke kan mirror ta shiga vibration.

“Give me my phone” ya yi maganar idanunsa a kan mirrorn

Medina, shi ne sunan da na gani yana yawo a kan screen din, wani bacin rai ya mamaye zuciyata, kamar kada in mika mishi, Sai dai babu yadda na iya, haka nan na mika mishi raina babu dadi.

Kamar ba ya so haka yake maganar, ban kama komai ba har ya aje wayar hade da jan tsoki.

“Me kika ce?” ya tambaye ni idanunsa a kaina.

Karamin yatsana na kai baki hade cizawa kadan sannan na ce “cewa na yi ya jikin naka?”

“Da sauki” ya amsa hade da mikewa ya nufi wardrobe din kayan shi, tsaye na yi ina kallon yadda yake sanya wata jar riga a kan bakin wandon da ke jikinshi , lokaci daya kuma yana ta zuba tsoki.

Can cikin kayansa ya dakko wata golden din karamar akwatu, Ya shigar da wasu lambobi akwatun ta bude, wata yar karamar bindiga na ga ya dakko hade da soke ta a kugunshi.

Ido na fitar cike da tsoro, ganin ya nufi inda takalmanshi suke, da sauri na dauke wayarshi da ke kan mirror na fita zuwa falo a guje, kofar fita na nufa hade da jingina bayana, kokarin kiran Aunty nake yi sai dai ban san lambobin sirrinshi ba, kamar daga sama sai ga kiran Ya Anwar, da sauri na daga a kuma tsorace na ce “Ya Anwar, kana ji na?”

Daga can ya ce “Ina jin ki, Maryam ce?”

Na kai kallo na hanyar da na san Ya Azeez zai fito, ganin har zuwa lokacin bai fito na ce “Eh ni ce, don Allah Ya Anwar ka yi sauri ka zo gida, ga Ya Azeez nan ya dauki karamar bindiga zai fita, kuma gidan ba kowa”

Cikin karaji ya ce “What?” na yi saurin yanke kiran ganin Ya Azeez din ya fito a fusace.

“Give me my phone, idiot! “a tsorace na mika mishi, lokaci daya kuma na juya baya na murza key din kofar hade da zarewa na rike a hannuna, da alama, bai ga lokacin da na zare key din ba, saboda hankalinsa na kan wayar shi, a fusace ya nufi kofar, can gefe na koma ina kallon yadda yake murzata da karfin tsiya amma ta ki budewa.

A fusace ya juyo yana kallo na”Ina key din? “

Cikin murya kuka na ce” Don Allah ka yi hakuri kar ka fita. “

Wata irin tsawa ya daka min tare da fadin” Ba ni key din na ce miki.”

Ni ma na tsananta kukana hade da rokon shi kar ya fita.

Ganin ya yo kaina a fusace, sai na kwasa da gudu zuwa bayan kujeru, ni da kaina na fahimci bn yi dacen wurin boyo ba, da wuri zai kama ni, kuma ya karbe key din, wannan tunanin ya sa na nufi windown da ke fuskantar waje , cikin zafin naman da ban san ina da shi ba, na bude window tare da tilla key din waje.

“Ke!” ya fada da wata irin murya, lokaci daya kuma ya yo kaina, yadda na ga ya taho kamar doki, a guje na kuma nufar hanyar kitchen, burina in samu damar fadawa kitchen din in rufe kaina, Sai dai kafin in cimma wannan burin tuni ya yi wani irin tsalle tare da hawo kujerar, kafarshi ya sanya ya kwashe ni, kafin in kai kasa cikin hanzari ya dago ni lokaci daya kuma ya sauke min wani lafiyayyen mari, wanda ya sanya ni jin wani dummmm! A cikin kunnena.

daidai lokacin da jina ya fara daidaituwa ne, kuma na ji muryar Ya Anwar yana kwalawa Ya Azeez kira kamar muryarshi za ta fasa ginin, tare da buga kofar da karfi yana cewa mu bude mishi,

Tsabar rudewa da rarrafe na karasa wurin kofar, saboda yadda na ga Ya Azeez na kwanto belt din da ke kugun shi, “Ya Anwar! Yi sauri ka bude ni, zai kashe ni, key din na nan saitin window a waje na jeho, yi sauri Ya Anwar!”

Na kai karshen maganar cikin wata irin kara, saboda ganin yadda Ya Azeez ya yo kaina.

shigar key din da na ji jikin kofar ya dan kwantar min da hankali, lokacin da ya kawo min duka, cafke belt din na yi, har lokacin bakina bai mutu ba, ganin kofar ta bude da rarrafe na kutsa ta tsakanin kafafun Ya Anwar na yi waje. Yayin da Ya Anwar din ya yi caraf da belt din da Ya Azeez ya daga da niyyar kara fyada min.

Cikin tsawa ya ce “Azeez are you in your sense? Ka san abin da kake kokarin yi kuwa? Za ka kashe ta ne?”

Iska mai zafi ya furzar lokaci daya kuma ya sake belt din ya nufi kofar.

Cikin zafin nama Anwar ya dawo da shi “Where are you going?”

“I want to take a revenge. Anwar! Ni yaran KB zasu yanka da wuka? I? Never, I will show them…”

“Show them what?” Anwar ya yi saurin katse shi.
Kafin ya dora “Kana son kara ɓata abubuwa dai. Ko ka san naushin da ka yi wa KB ya yi sanadiyyar lalacewar idon shi?”

“and so what? Ni da sun kashe ni fa?”

“Look Abdul’azeez!” ya fada cikin tausasa murya

“Na san ka fi su gaskiya, but please calm down, muna kokarin ganin cewa a hukunta wadanda suka yi ma wannan, but ka fita yanzu za ka kara rikirkita al’amura ne, please, don Allah ka jira a nan.”

Wani murmushi mai ciwo ya yi sannan ya ce “Anwar! You mean in zauna a nan, ku kuma ku tare min fada? Ku ne za ku tare min fada Anwar?”

“Not like this Azeez…”

“Then what?” ya yi sauri katse shi cikin sauri,lokaci daya kuma ya bangaje Anwar din wanda ya tare mishi hanya.

Da yake karfi ne ya hadu da karfi, Sai kowa ya rasa yadda zai yi da kowa, Abdul’azeez na kokarin fita, yayin da Anwar ke shan matukar wahala wajen ganin bai fitan ba.

Ni dai kam ina tsaye a entrance dina Ina jinyar kunnena, don da gaske ba na ji sosai da bangaren da ya maren din, ji nake ma kamar wajen ba kunne. Yayin da kuma nake kallon yadda ake tafka kokawa tsakanin Ya Anwar da kuma Ya Azeez.

Daidai lokacin motar Madina ta shigo, ko parking mai kyau ba ta yi ba, ta fito da wani irin sauri wanda take hadawa da gudu.

“Azeez!” ta kira sunanshi da karfi lokacin da ta isa bakin kofar falon, dukkansu suka dakata da kokawar, yayin da Madina ta karasa shiga ciki, a sanyaye ta ce “What is all this? Haba da girmanku.”

Cike da haki Ya Anwar ya ce “Wai dole sai ya fita, kuma akwai bindiga a jikinshi.”

“what!” cikin zaro ido ta yi maganar, lokaci daya kuma ta karasa inda Azeez din yake tsaye, yana kumburi kamar zai yi aman wuta.

A marairaice ta ce “Sorry Abdul’azeez! Don Allah ka yi hakuri. Na san ranka a bace yake, saboda abin da suka yi maka, amma kai ma ka rama ai.”

“Ban rama ba, amma zan rama.”
Cike da bacin rai ya yi maganar.

“No ka rama Azeez, Kb idon shi ya fashe yana asibiti, kuma ka cirewa daya daga cikin yaran shi haƙori.”

“And shi ne me? I want kill them, Kamar yadda su ka yi kokarin kashe ni.”

“No dear! Ba za ka yi kisan kai ba, infact ba za ka iya ma kashe mutum ba. Just calm down my dear” ta yi maganar tare da kama hannayenshi du biyun bayan ta langabe kamar za ta fashe da kuka.

A zuciyata na ce lallai Ya Azeez yana shan soyayya da lallashi, tsohuwar mace ta koma yarinya yau. Kai soyayya akwai dadi akwai wuya.

Daga haka ta sake hannun shi daya, dayan kuma da yake rike a cikin hannunta ta ja shi zuwa daki.

Na sauke ajiyar zuciya da ta sanya Ya Anwar waigowa yana kallo na.

Namiji duk zafin shi, mace ce ke zama kankarar da take sanyaya shi, kamar yadda sansanyan namiji mace kan mayar da shi mai zafi idan taso.

Madina & Azeez

Cikin kwantar da murya Madina ta kuma cewa “Ka yi hakuri Dear, ka san ba na son bacin ranka, kuma duk wanda ya taba ka, zai ji ni, na yi ma alkawari yaran nan sai sun zauna gidan yari.”

“Ba wannan nake so ba, so nake da kaina in hukuntasu” ya fada cikin zafi.

“And you did” ta yi saurin tarbar numfashinshi.

“Ka fasawa KB ido, ka cire haƙorin daya daga cikin yaran shi, KB na asibiti kai kana gida, yaran shi suna prison kai kuma na ka abokan suna gida. Sannan daga wannan lokacin Azeez na yi alkawarin sun daina ma gori a kan karatu, za ka fita duk ƙasar da kake so ka karanta abin da kake so.”

Ta karashe maganar idanunta a kan shi.

Tsoki kawai ya ja, ba tare da ya ce komai ba, wannan ya sa ta dage rigar shi tare da zare karamar bindigar ta jefa ta cikin kayan shi na wardrobe, sannan ta kulle wardrobe din ta zare keyn.

“Azeez I promise you zan ba ka rayuwa irin wacce kake so, kowa sai ya rasa da abin da zai goronta ka muddin ina raye, just give me a chance.”

Uffan bai ce mata, illa ya zauna a gefen gadon, har zuwa lokacin ransa a bace yake, yayin da Madina ke ta tsara kalamai masu dadi, tana jifan shi dasu. Kuma a hankali kalaman nata suka fara tasiri a kanshi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Da Magana 10Da Magana 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×