Washegari haka na tashi fiyot da ni, komai ba ya min dadi, don ciwon kunnen ya dan yi sauki. Ga rashin bacci saboda zaryar da na sha jiya da dare.
Cike da karfin hali na rika taya Aunty ayyukan gida, saboda ba na son ta kara tayar da hankalinta, amma kam ciwon kunne na daya daga cikin ciwukan da zan iya lissafawa masu azaba. Na sha wahala sosai.
Ban iya zuwa school ba, lafiyar gadona na bi, bayan na sallami su Dog da donkey. Cikin bacci na ji ana buga min kofa, ko ban tambaya ba na san Ya. . .