Skip to content
Part 13 of 26 in the Series Da Magana by Matar J

Washegari haka na tashi fiyot da ni, komai ba ya min dadi, don ciwon kunnen ya dan yi sauki. Ga rashin bacci saboda zaryar da na sha jiya da dare. 

Cike da karfin hali na rika taya Aunty ayyukan gida, saboda ba na son ta kara tayar da hankalinta, amma kam ciwon kunne na daya daga cikin ciwukan da zan iya lissafawa masu azaba. Na sha wahala sosai.

Ban iya zuwa school ba, lafiyar gadona na bi, bayan na sallami su Dog da donkey. Cikin bacci na ji ana buga min kofa, ko ban tambaya ba na san Ya Azeez ne, saboda Aunty ta ba shi keyn main pallor Tun lokacin da ta ce ya dawo gida da kwana. A gajiye na isa kofar lokaci daya kuma na murza handle din da zummar budewa, Sai dai me kofar ta rike gam, iyakar bakin kokarina ba ta bude ba, wannan yake tabbatar min da jamlock din ya shiga ciki ga shi ba key.

“Wai ba za ki bude kofar ba?” karon farko da ya yi magana cikin daga murya 

A dan tsorace na ce “kofar ta datse kuma ba key”

“What!” ya fada da sauri.

Na kara maimaita abin da na fada.

“OK wait.” ya ce lokaci daya kuma Ina jiyo takun tafiyarshi.

Ba jimawa na ga kanshi ta window, wannan ya tabbatar min da ya dakko abin da zai kara mishi tsawo ne.

“ki murza, ki ja  da karfi” ya ba ni umarni.

Jiki na rawa na yi kamar yadda ya ce

“Ke dalla can ki ja abu da karfi Malama.” ya daka min tsawa.

Sai ya kara rudani na shiga jan kofar da iya karfina.

“Oh God!” ya yi maganar cike da takaici hade da jan tsoki, kafin ya ce “Na kina ja da karfi kenan? A haka kofar za ta bude? Eh za ki kare rayuwarki a daki kenan” ya kai karshen maganar tashi hade da kokarin sauka.

Cikin murya kuka na ce “Wlh da karfina nake ja”

Ya dakata daga saukar da ya yi niyya tare da zubawa kofar ido, Sai kuma ya sauka din.

“Matsa.” ya fada daga wajen kofar.

Na ja baya kadan wanda ya yi daidai da wata irin karar da ta sanya har ginin ya motsa, sakamakon duka da Ya Azeez ya yi wa kofar da kafa.

Ni mai rububben kunne tuni na gigice, ban dawo hankalina ba, na kuma jin saukar wata karar, da sauri na haye gadona hade mikewa na leka ta window “Ya Azeez  wait please, don Allah jira” da karfi na rika maganar yayin da hannuwana ke dafe da kunnuwana.

Ya dakata tare da kallo na. “Kunnena ke ciwo, ba na son abu mai ƙara.” cikin kuka na yi maganar.

Wani irin kallo yake yi min, irin na cika matsalolin nan, sannan ya juya zuwa dakinshi.

Cikin kuka na shiga kwala mishi kira, gaf zai shiga corridorn da zai kai shi dakinshi ya tsaya, tare da juyowa yana kallo na, yayin da na ci gaba da rera kukana

“Me kike so in yi? Ki jira Aunty ta dawo sai ta bude ki, ni na gaji da matsalolin ki, idan kina son wani abu just call me” ya kai karshen maganar tare da dage yatsunshi biyu babba da kuma karami zuwa saitin kunnen shi.

Sautin kukana na kara, tare da fadin “Ni dai ka zo ka bude ni don Allah.”

Shiru ya yi, kamar yana nazarin kukan nawa, kamar wanda ya tuna wani abu ya ce “Wait I’m coming.”

Bai jima da fita ba, ya shigo hannunshi rike da dutse.

“ki buga jam lock din da karfi zai fita” ya ba ni umarni lokacin da yake mika min dutsen ta window

Na shiga buga kofar amma ko gezau, wannan ya sa na dakata tare da dagowa ina kallon shi. Saboda har zuwa lokacin yana tsaye a kan windown yana kallo na

Baki ya tabe, alamun ban yi abun yabo ba.

“Me kike tsoro sosai?” ya tambaye ni idanunshi a kaina

Na dan yi shiru kafin in ce “Kadangare”

Ya shiga jinjina kai a hankali kafin ya ce “So let’s assume kin shiga toilet Kawai Sai ki ga kadangare irin katon nan mai jan kai. Kina juyo wa ya biyo ki, Sai kuma kofa ta rufe, amma kika yi sa’ar samun Dutsen nan na hannunki”

Na dauke idanuna daga kanshi zuwa  kan dutsen da ke rike a hannuna.

“Oya! Buga da karfi ga shi nan yana zuwa”

Na ji kamar da gaske kadangaren ne, shi ya sa cikin irin karfi na tsoron, abun tsoro na buga kofar da karfi, karar ta ratsa dodon kunnuwana, kafin in warware ya kuma cewa

“Yana zuwa buga da karfi” 

Da sauri na kuma bugawa da karfi fiye da dazu.

“Ki buga da karfi zai hau jikinki” cikin hargowa ya yi maganar kamar kadangaren na kokarin hawa jikina.

Wannan ya sa na kara tsorata sosai, na fasa kara tare da tattara duk wani karfi nawa na buga jamlock din, take ya fita, na fisgi kofar tare da ficewa a guje zuwa falo. Hannayena a kan kunnuwana

Can karshen falon na tsaya, ina kallon cikin dakin, tamkar ina jiran fitowar kadangaren, yayin da Ya Azeez ke gyara jamlock din.

Ina tsaye a wurin ya gama gyarawar, daidai zai wuce ni ya ce “Ki shirya an jima za ki raka ni wani wuri.”

Kai na daga alamar to, kafin in yi magana ya ce

“Idan akwai hanta kidan yi min pepesoup din da Aunty ke yi, ko turarawa ne ma i don’t know, just I want it.”

Kai na kuma dagawa tare da nufar kitchen.

Na gane abin da yake nufi, marinating yake so a yi mishi na kayan ciki.

Sai na hada aikin biyu har da abincin rana, na shi na fara gamawa na kai mishi, sannan na dawo na idar da namu abincin.

Misalin karfe biyu Aunty ta dawo, Sai da na ba ta 30mns sannan na kai mata abinci, tana cin abincin hade da tambayata ya nake ji, ni kuma ina amsa mata da sauki.

“Aunty!” na kira ta alamun zan fadi abu mai muhimmanci.

Ba ta amsa ba, amma ta dakata da cin abincin da take yi hade da kallo na.

“Dama Ya Azeez ne ya ce an jima zan raka shi.”

“Ina?” ta tambaya da sauri

“Bai fada min ba”

“Je kira min shi.”

“Aunty kar fa ki ce za ki yi fada” na fada a marairaice

Harara  ta watso min, wannan ya sa na nufi kofar fita ba shiri.

Lokacin da na shiga dakin kwance yake a tsakiyar gado yana taba laptop din Shi, ba tare da ya dago ba ya ce “Me ye?”

“Dama Aunty ce ta ce ka zo” na yi maganar karamin yatsana a bakina.”

“Me kika fada mata?” har zuwa lokacin bai dago kanshi daga tabe-taben da yake a laptop din ba.

“Ban fada mata komai ba.”

Yanzu kam ya dago tare da watso min wani kallo. A daburce na ce “Na fada mata ne zan yi ma rakiya.”

Ya dauke idanunshi a kaina tare da fadin “Je ki.” ya rufe maganar da siririn tsoki

Ina shiga dakin, shi ma ya shigo, don haka ku san a tare muka zauna a gefen gadon muna fuskantar Aunty wacce ke zaune a kan sofa tana danna wayarta.

“Barka da dawowa Aunty” ya fada da kyar kamar ba ya so.

“Yauwa” ita ma ta amsa kamar wata sarauniya, a zuciyata na ce yau duk sarauta suke ji.

“Maryam ta ce za ku fita, ina za ku je?”

Ya ɗan yi shiru, kamar mai tattaro abin da zai fada, har na fitar da rai zai amsa, Sai kuma na ji ya ce “Eh, za ta raka ni ne.”

“Ina?” idanunta a kanshi

“Aunty! She’s my sister fa.”

“I know, just tell me, Ina za ta raka ka?”

Ya cuskune fuska kamar zai yi ihu.

“Ke tashi fita da Allah” ya yi maganar idanunsa a kaina.

Sumi-sumi na nufi kofar fita. 

Aunty & Azeez

“ina jin ka” cewar Aunty bayan fitar Maryam

Ya kuma tsuke fuska sannan ya ce “Aunty she is my sister, Kuma kin San ba zan bar komai ya same ta ba, amma…”

“just answer me, Ina za ku je?”

Ta katse shi.

“Mubarak ne ya shirya mana dinner, shi ne nake son ta raka ni.”

Aunty da ta bude baki cike da mamaki tun lokacin da ya fara magana ta rufe bakin tare da fadin “Are you serious? In ba ka Maryam zuwa wurin taron ku Azeez, are you in your common sense. Please get out”

“Aunty wait please, ba fa wani abu ba ne babba, kawai akwai  yarinyar da za ta je wurin ne, so ina son ta ganni tare da wata.”

“Fita ka ba ni wuri Abdul’azeez, ka daina saka Maryam a cikin shirginku, ita ba irin ku ba ce.”

“Haba Aunty, wlh ba zan bar komai ya same ta ba, I’m telling you, kawai ina son amfani da ita ne a kan wata.”

“Ba ga Madina can ba, ka dauke ta mana ku tafi.” 

“Madina Kuma Aunty” ya fada murya a sake.

“Eh ita”

“Ke ma kin san ba za ta je wurin ba.”

“Oh! Sai Maryam” ta fada hade da manna mishi harara.

“Aunty ba fa yadda kike tunani ba ne, and I promise you zan kular miki da ita.”

“Ban yarda ba, me ye hadin kifi da kaska, me ye hadin Maryam da taron ku?”

“Eyyah Aunty, ki sanya min time da zamu dawo Allah ba zan ke tare ba, kawai ina son tayar da hankalin wata.”

Bin shi da kallo Aunty take yi, wannan ya sa ya ci gaba da kwakkwafeta tare da alkawura kala-kala.

“Azeez Maryam amana ce a wurina, ina jin tsoro, ita ba ta dace da wurin da za ka je ba sam.”

“Aunty! Sau nawa zan fada miki babu abin da zai faru, ina wurin fa, kin san ba zan bar komai ya same ta ba, ni ma fa ba na son komai ya taba ta.”

Tabe ba ki ta yi kafin ta ce “Kai din, ga shi can ka sanya hannunka mai kama da katako a fuskarta ka kashe mata kunne daya.”

Ido ya fitar kafin ya ce “Ni din?” 

“Zan yi ma karya ne?” cike da harara ta yi maganar. 

Ya ɗan marairaice “Shi kenan ba zan sake ba.” 

“Da ka kyauta. Azeez Maryam na daya daga cikin masoyanka ni da na sani, ta yi kuka da damuwarka, ta yi farin ciki da farin cikinka, ta tsare cin ka da shan ka, ta tsare makwancinka, hatta biri da karenka sun ci arzikin darajar soyayyarka suna samun kulawa ta musamman kamar wasu ƴaƴan ta. “

“Ai ita ce ta faye shiga harkar da ba tata ba , wannan yana bata min rai “ya yi maganar bayan ya cusgune fuska. 

“Is that all? “Aunty ta tambaya idanunta zube a kansa

Kai ya jinjina alamar Eh. 

“Sai ka yi mata uzuri, kai abubuwa nawa ta yi ma uzuri a kansu.”

Duk suka yi shiru, kafin ya katse shirun da fadin “An ba ni aron ai?” 

Sai da Aunty ta jefa mishi harara sannan ta ce “To yana iya, amma wlh ka dawo min da yarinyata lafiya lau.”

Karon farko da ya yi dariya mai sauti tare da fadin “Ɗaya kika ba ni, Ɗaya zan mayar miki, I promise you.”

Ba ta ce komai ba, hakan ya sa ya kuma murmusawa tare da mikewa tsaye “Aunty ta yi kyau fa, ina son tayar kura ne.” ya kai karshen maganar tashi cikin dariyar tsokana, yayin da Aunty ke watsa mishi harara fuska a daure.

Ya fice daga dakin yana dariya.

Ajiyar zuciya ta sauke kadan, Allah Ya sani tana yi wa Abdul’aziz wani irin so, bayan son uwa da ɗa, shi kaɗai ne take gani a matsayin jininta, kawayenta da aka yi musu aure tare wasu har sun dauki jikoki, ita ba ta san ranar da za ta ga auran Azeez ba, bare ta dauki ɗansa, to yaushe ya tsaya ma ya gina kansa bare ya yi tunanin gina kan wani.

Nisawa ta yi hade da mikewa zaune saboda tuno wani furuci da Mamansu Huzaima ta yi mata lokacin da gano akwai alamun ciki tare da ita.

Misalin karfe hudu na yamma ta kwankwasa mata kofa, lokacin da ta bude ta gansu tsaye ita da aminiyarta Gana.

“Ciki gare ki ko?” ita ce tambayar farko da Aunty Adama ta fara yi mata.

“Eh” ta amsata ba tare da gardama ba.

Wani irin murmushi Aunty Adaman ta yi kafin ta ce “Amma wannan cikin ba a daki aka yi shi ba?”

Wannan karon ma amsata ta yi da “Eh.”

“A Ina ne?”

“Kitchen ne” ta kuma amsa mata tambayar.

“Ina fatan ki haihu lafiya, ki ɗanɗana da in da iyaye suke ji, a lokacin da suka haifi yaro ya zame musu ala-ƙa-ƙai.

Abin da ta furta kenan haɗe da jan hannun aminiyarta suka wuce.

Ta sauke ajiyar zuciya haɗe da numfasawa a hankali. A fili kuma ta ce” Allah Ya Kyauta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Da Magana 12Da Magana 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×