Skip to content
Part 16 of 26 in the Series Da Magana by Matar J

Tun daga lokacin da muka gama exam, duk yamma na kan fito da dog da monkey farfajiyar gidan. Donkey daure shi nake saboda barna, amma na kan sanya mishi igiya mai tsawo saboda ya sake. Shi kuwa dog na kan aje tabarma ko plastic chair Ina gadinshi, saboda yana da fada, idan har yana bude, ba kowa ne ke shigowa gidan kai tsaye ba, sai an yi mishi jagora.

Wani lokaci Aunty ta kan taya ni zaman, wani lokaci kuma ba ta fitowa, kamar yau ma da ni kadai ce a tsakar gidan zaune kan plastic chair misalin karfe biyar na yamma yayin da na mayar da hankalina kan Hammawa da yake wasa da monkey. Yanayin yadda suke wasan ne yake sanya ni nishadi, shi ya sa nake ta murmushi.

Horn din da aka yi ne ya sanya Hammawa tafiya wurin aikinshi, yayin da Dog ya mike zumbur daga kwanciyar da yake, ni kuma na zubawa gate din ido, fatana Allah Ya sa Ya Azeez ne, rabona da in sanya shi a ido mun shiga sati na uku kenan.

Na janye idona cike da takaicin ganin Aunty Adama, yayin da Dog ya fara yi mata gurnani, ganin ta fito sai ya zabura zuwa wajenta yana haushi.

Tsawar da na daka mishi ce ta sanya shi dakatawa, amma bai daina haushin ba, daga can ta ce “Riƙe shi mana Maryam na kawo ma biri abu ne”

Yadda ta yi maganar cikin taushi babu hantara sai abun ya ban mamaki, “Dog!” na kira sunan shi, ya waigo daga inda yake yana kallo na

“Come now, come” na fada hade da yafito shi da hannu, sai ya taho da alamun bai so kiran ba.

Ita kuma ta karaso inda monkey yake ta tsalle-tsallen shi ta jefe mishi ayaba.

Maimakon ya cafe kamar yadda yake mana, sai ya ki yin hakan, ya kafe ni da ido yana kallo na, kamar mai jiran umarnina.

Cike da mamaki ta ce “Kin ga abu kamar mutum, jira yake ki ba shi umarnin karba”

Duk muka yi dariya har da Hammawa da yake dan nesa damu yana kallon mu.

“Take it.” na fada ina nuna mishi ayabar da ke kasa.

Ya kalli ayabar, sannan ya kalle ni, ba tare da ya dauka ba.

“Ka dauka na ce” na kuma fada Ina nuna mishi ayabar.

Kamar mai shakku a kan abin da na fada, ya dauki ayabar a sanyaye amma bai ci ba.

Miko min ta hannunta ta yi tare da fadin “gwada ba shi da kanki mu gani”

Na karba tare da kiran sunan shi, tsakanin rufe bakina da hawanshi jikina ban san wanne ya riga wani ba.

Kasa na sauke shi, tare da mika mishi ayabar, da sauri ya amshe ya shiga barewa lokaci-lokaci kuma yana dago kanshi ya kalle ni, ya kuma kalli Aunty Adama, da ke tsaye cike da mamakin abin da ya yi.

Haka na rika mika mishi ayabar yana ci, ta karshen da na mika mishi, yana gama barewa sai ya jefawa Aunty Adama bawon.

Duk muka kwashe da dariya, ta dora da “Lallai ka iya godiya , daga na ji kanku, na ga mai kula da ku ya tafi ya bar ku”

Wani abu mara dadi ya soki zuciyata, Allah Ya sani na yi kewar Ya Azeez, kuma idan na kira layin shi baya tafiya.

Kun yi kewarshi ko? “Aunty Adama ta katse min tunani lokacin da take shafa kan Dog da yake kusa da ni.

” Yana can Dubai yana shan hutu, yaushe zai dawo ne? “ta yi tambayar lokacin da take kallo na.

A sanyaye na ce” Ban sani ba”

“Hala maganar makarantar ce ta taso?” ta kara tambaya ta.

Na kuma cewa “Ban sani ba”

“Okay, kodayake ma ai ba a can aka nemar mishi admission din ba, ko haka nan Hammah ya tura shi hutu”

Girgiza kai na yi a hankali, kafin in ce “sai dai ko Madina ce ta biya mishi”

Ta gyara tsayuwarta tare da fadin “Wai Aisha ba ta hango matsala a tarayyar Madina da Abdul’azeez ne?”

Mamaki ya kama ni yadda Aunty Adama ke hira da ni kamar wasu abokan sirri, cikin son boye laifin Aunty na ce “Ai ta ce auranshi za ta yi, kuma za ta yi mishi duk abin da yake so, ciki har da karatu da cika mishi duk wani burin shi”

Ta shiga jinjina kai alamar gamsuwa, sannan ta ce “To Allah Ya nuna mana lokacin.”

Na amsa da “Amin”

Kudi ta ciro tare da dora min a kan cijyata “Ko za ki siyawa iyalanki abu”

“Na gode” na fada lokaci daya kuma Ina dauke kai daga barin kallon ta.

Sai da na tabbatar ta shige part din ta sannan na mike zuwa namu part din, kai tsaye dakin Aunty na wuce.

Sarkokinta take gyarawa da suke zube a cikin wani madaidaicin box, ganina ne ya sanyata dakatawa

“Me ya faru?”

Na zauna gefen ta cike da mutuwar jiki, ina ciza ƙaramin yatsana.

“Ina jin ki” ta fada tare da juyowa sosai tana kallo na.

“Aunty kin san Ya Azeez yana Dubai wai?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Na sani, kodayake ban jima da sani ba, Hammah ne ya sa aka binciko mishi, wai suna tare da Madina”

Gabana ya yi wata irin faduwa na ce “Madina Kuma?”

Cikin sanyi jiki ta ce “Eh.”

Duk mu ka yi shiru alamun kowa da abin da yake tunani.

Ta katse ahirun da fadin “Ina son kawo alakar Azeez da Madina ta hanyar daura musu aure, shi ne kawai mafita, tun kafin wani abu mara dadi ya faru. Dama ita ce daidai auran na shi, ya ci a sama kamar hancin gauta, idan ba ita din ba, to wace wawuya ce za ta auri Azeez da munanan halayen nan na shi. Bai san komai ba, sai ya saci kudi ya ci mai kyau ya sha mai kyau, ya hau mai kyau, ya kwanta a wuri mai kyau. Babu karatu babu kasuwa. “

” Aure kuma Aunty? “na fada kamar zan yi kuka.

” Shi ya fi Maryam, jiran su kawai nake su dawo, a tsayar da lokacin bikin.

Na yi shiru cikin jinjina kaina, ba tare da na san abin da zan ce ba, ganin ba ni da abun fada, mikewa na yi na fice, har na dauki hanyar dakina, sai kuma na tuna Dog da Monkey suna waje, dalilin da ya sanya ni nufar wajen, Monkey da ke zaune a kan kujerata gani na sai ya sauka kasa.

Jiki a mace na zauna yayin da zuciyata ke cunkushe, na kure tunanina ta hanyar neman hanyar da zan dakatar da auran Ya Azeez da Madina, ko kawai in fadawa Aunty ni ina son Ya Azeez kuma zan aure shi a haka?

Na yi shiru a wannan gabar tare da zurfafa tunanina, a zahiri na ce “Ba zan iya ba.”

Idan kuma ban yi hakan ba, ina ji Ina kuma gani za a daura auran Madina da Ya Azeez, wanda hakan zai iya sanadiyyar raina.

Ban san ina hawaye ba, sai da na ji lallausan hannun monkey a kan fuskata yana dauke min hawayen, yana dan kukansa alamun ya damu da kukan da nake yi, tausayin kaina ya kama ni, ji nake kamar ba ni da kowa sai monkey da yake share min hawaye a yanzu, rana ta farko da na ji kewar mahaifiyata, ji nake ina ma tana raye in je gare ta, ko ban fada mata matsalata ba, na gan ta zan ji sanyi.

Ina ma Ina da yar’uwa ko ɗan’uwa tabbas da na ta fi gare shi, canji wuri kawai nake nema kila na dan ji saukin abin da nake ji a zuciyata.

Ina da yayyu biyu mata amma duk sun rasu, yayin da mahaifiyata ta rasu a lokacin haihuwar kanwata, wacce a kalla na ba shekaru goma.

Ban sha wata wahala ba, a lokacin da na rasa mahaifiyata har zuwa lokacin da rikona ya dawo hannun Hammah, inda na samu kyakkyawar rayuwa ninkin ba ninkin wacce na baro a kauyenmu.

Kiran sallar magriba ya tashe ni, na mayar dasu Dog cikin keji, ni kuma na shige daki, kasancewar ba na sallah saman gadona na fada, na dora daga inda na tsaya, wato neman mafita.

Salma ta fado min a rai, da sauri na mike ina fadin “Yes. Salma ita za ta yi min wannan fadan , da zarar ta raba Madina da Ya Azeez, ni kuma zan raba ta da shi, amma Madina ta fi karfina a komai.

Na shiga searching din ta a Instagram har na lalubo account din ta, na shiga shafin nata ina kallon zafafan hotunan ta masu daga hankalin lafiyayyen namiji.

Shiru na yi ina kallon kamar zan yi kirari in dabawa kaina wuka, ta ya zan ba Salma dama a kan Azeez, macen da ta ku san hada komai, kyau, kudi, ilmi da kuma wayewa, anya ba kuskure nake kokarin tabkawa ba.

Na nisa kadan, kafin wata zuciyar ta karfafa min gwiwa a kan abin da nake son yi.

Sallama na yi mata, kafin in ce “Sunana Maryam, ni kanwar Done AZ ce, Idan ba damuwa ina son ganin ki, ko kira ni a wannan Lambar” na aje mata no ta, tare da addu’ar Allah Ya sa ta bude sakona.

Ta gyara zaman wayar da ke kunnen ta tare da fadin “Kina ji na ko Gana, wato yaron can kashin arziki ne da shi, idan na toshe wannan kofa sai wannan ta balle, ni da nake son ganin shi a gantale, ina zan bari ya auri Madina, don haka duk yadda za a yi a shata musu layi tsakanin shi da wannan Madinar a raba alakarsu Gana.”

Daga can bangaren Gana ta ce” Sai da na ce miki a daukewa yaron nan sha’awa kika ƙi yarda ai. “

Aunty Adama ta nisa tare da fadin” Idan aka dauke mishi sha’awa ai an toshe wata hanyar alfashar, ai kawai a kyale shi haka, yay ta neman matanshi amma ban da Madina”

“To ai shi kenan. Waccan maganar kuma da mu ka yi da ke, ya ce wai wata ce ta kwashe duwatsun nan, amma ya kasa ganin fuskar ta, sai dai ki kwantar da hankalinki, aikin da aka binne a kasa shi bai baci ba, don haka har yanzu babu wata matsala”

Aunty Adama ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce “Alhamdulillah! Na ji dadin wannan magana. Zuwa safe za mu yi magana”

“To Allah Ya kai mu.”

“Amin” cewar Aunty Adama haɗe da yanke wayar.

Bacci bai jima da daukata ba na ji haushin dog, wannan ya sa na mike da kyar hade da zuwa window na yaye laluben ina kallon farfajiyar gidan.

Cike da mamaki nake kallon mutanen da suke tsakar gidan tamu, sanye cikin babbar riga da rawani, yayin da Hammah ya yi musu jagora zuwa dakin da yake shiga ya dade, sannan ya yi wanka a tsakar gida.

Daga inda nake tsaye nake jiyo gununsu kamar karatu, kamar kuma wani abu daban ba karatu ba.

Basu fito dakin ba, sai da aka fara kiran sallar farko, kai tsaye motocin biyun da ke fake a tsakar gidan suka shiga, sannan suka fice, har zuwa lokacin kuma dog bai fasa haushi ba, kamar zai balle cage din ya fito.

Haka na koma dakina, toilet na wuce tare da dauro alwalar asuba.

Ina idar da sallahr na wuce kitchen, saboda yau Hammah a dakin Aunty yake, tare muka gama komai da Aunty muka gyare falon haɗe da turare shi, kamshi mai dadi ya rika fita.

Misalin karfe tara na jiyo muryar Hammah a falon, wannan ya sa na fito domin gaishe shi, ya amsa hankalinsa a kan matarsa, na koma daki, na zuciyata cike da mamakinshi, kalle shi cikin shiga ta kamala, babu wanda zai ce yana aikata wani abu ba daidai ba, ni kam na ciwa kaina alwashin sai na ga abin da ke cikin dakin can, koda zan mutu.

Tare suka fita da Aunty, gidan ya rage ba kowa sai ni kadai, saboda na san Aunty Adama ma ta dade da fita.

Kudin da Aunty Adama ta ba ni jiya na dakko 2k na tafi wurin Hammawa.

Plastic chair na Ja hade da zama bayan na gaishe shi.

Cikin tsokana ya ce “Yaranki suna kuka ba ki je wurinsu ba”

Dariya na yi tare da kallon dog wanda yake ta haushi yana kallo na. Sannan na ce “Yunwa yake ji”

“Ba sai a ba shi abinci ba.”

Na dauke idona daga kallon dog, na maido shi kan Hammawa tare da fadin “Dalilin da ya sa kenan na fito, don Allah ka je kan round din Ribado square ka samo mishi ko kayan ciki ne” na kai karshen maganar tare da mika mishi kudin da ke hannuna.

“Amma za ki zauna a nan ba”

Na daga kai sama alamar eh.

Sannan na ce “Wai maganar me Hammah yake yi ne a kan Dog Hammawa, na ji kwanaki can yana ma magana kuma na ga yau ma kamar ya yi ma” haka nan na bugi ruwan cikinsa na ce ya yi mishi magana yau.

Ya ɗan canja fuska zuwa rashin jin dadi kafin ya ce “kin san dog dinkun nan da haushi idan ya ga Hammah ko bakuwar fuska, shi kuma abun baya mishi dadi, jiya kuma da dare ya yi baki, shi ne dog ya yi ta haushi yana damunsu, ya ce idan Yallaboi Azeez ya dawo in ce mishi ya dauke karenshi daga gidan idan yana son shi.”

Kai na shiga jinjinawa alamun na fahimci abin da yake nufi, kafin na ba shi umarnin tafiya.

Sai da na tabbatar ya tafi, sannan na mike zuwa gate na sanya sakata, kafin na dauki plastic Chair da na zauna zuwa windown dakin sirrin Hammah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Da Magana 15Da Magana 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×