Skip to content
Part 19 of 26 in the Series Da Magana by Matar J

Garin Gembu, ni’imtaccen gari ne da yake mallakin jihar Taraba.

Gari ne da Allah Ya albarkace shi da ni’imomi kala-kala, kama daga kasar noma, kiwo da kuma tafkuna masu ban sha’awa.

Ma fi yawan mazauna garin Fulani ne, kyawawa, da basu da wani abinci da ya wuce fura, nono, dankali, piya da kuma ganyayyaki.

Wuro Malam ita ce rugarsu Aisha (Aunty) kaf zuriyarsu Aisha dangin mahaifinta bayan kiwo to sai malanta shi ne abin da suka iyawa na biyu.

Saboda duk yankin an san rugur wuro Malam wajen tsari, ko kazarsu ba a iya sata. Saboda tsari.

Aisha tana yar shekara biyar mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwa, wannan ya sa Aisha ta tashi cikin kishiyoyin Mamanta guda biyu, yayin da ta kasance ƴa daya tilo a ɗakin mahaifiyarta ba kanwa babu yaya.

Ba ta sha wahalar yan ubanci ba, kasancewar Baffa a tsaye yake, shi ya sa sam ba ta san wani abu ƴan ubanci ba.

Tana da shekaru sha uku ta sauke alqur’ani, a lokacin ne kuma kanwar mahaifinta Yafendo ta kawo kukanta wurin Baffa a kan tana son a ba ta Aisha, tun da ita ba ta taba haihuwa ba.

Baffa bai musa ba, ya ba ta Aisha sai dai da sharadin daga lokacin da ta dauke ta, zuwa ko wane lokaci zai iya yi mata aure.

Kasancewar mijin Yafendo irin Fulanin tashin nan ne da farko a garin Takun suka fara zama, a nan ne kuma Yafendo ta saka Aisha a makarantar boko, maganin kar ta zauna haka nan, ita kuma sai ta shiga gari tallar nono,

Shekararsu biyu a Takun suka karasa garin Yola da ke jihar Adamawa.

A nan Jauro ya samu aiki da gidan Lamidon Adamawa inda yake kula da shanun masarautar.

Yafendo kuma tana shiga gari tallar nono.

Aisha kuma na zuwa makaranta. Saboda da Aisha da Yafendon kowa yana gane dadin ilmin boko.

Idan ta ga Aisha na karanta abu da Hausa sai dadi ya kashe ta, ba ita kadai ba, ko Gembu suka kai ziyara Baffa yana jin dadin idan ya ga Aisha na rubutu kuma tana karantawa, duk wani abu da ya shafi boko idan tana gidan ita yake ba, idan ya ga ta warware sai ya ji dadi da farin ciki, shi ya sa bai damu da Aisha ta yi aure ba, ya ce a jira ta gama secondary, tun da tana gane karatun.

Tun da Yafendo ta gane roman da ke cikin kawo tallar nono 80 Units, Sai ta daina zuwa ko ina tallar nono sai unguwar, dan rukunin unguwar kowa ya santa ita ma ta san ma fi yawansu.

Maman Aisha haka suke kiran ta, a haka ne suka kulla kasuwanci ita da Hammah inda take kawo mishi nono da kuma manshanu. Har lambar wayarta gare shi, saboda idan yana son mai ko nono sai ya kira ta ya fada mata, ita ma idan an samu mai ko nono unexpected ta kan kira shi ta ji ko yana da bukata.

Hammah ke tsokanarta da za ta ba shi Aisha ya aura, dariya kawai Yafendo ke yi, wani lokaci ta tanka shi, wani lokaci kuma dariyar kawai take yi.

Watarana ranar Juma’a Hammah ya kira Yafendo a kan idan akwai manshanu yana bukata, Yafendo ta tabbatar mishi akwai sannan ta ce Aisha ce za ta kawo mishi saboda ita kasuwa za ta je sayen geron dakkere.

A lokacin har tsokanarta ya yi da “Yau amarya za ta zo gidan angonta”

Duk suka yi dariya.

Kasancewar Aisha ta san 80 units ba ta sha wahala ba wajen gano gidan Hammah.

Ba ranar ne ta fara shiga kyawawan gida ta sanadiyyar kai nono ko mai ba, amma sosai kyan gidan Hammah da tsarin shi ya tafi da ita, shi ya sa lokacin da ta tsinci kanta a farfajiyar gidan ta rika ware ido tana karewa ginin kallo, kafin daga bisani ta dire a cikin kejin da jimina ke kiwo, ba ta taba ganin jimina ba sai ranar, shi ya sa ta gyara tsayuwarta sosai, hannayenta dafe da ƙwaryar da ke bisa kanta tana kallon yadda jiminar ke ta zaƙam-zaƙam da wuya a cikin kejin.

Har sai da maigadi Kwada (Mahaifin Hammawa maigadi na yanzu) ya ce mata an ce ta shiga.

Ta rika tafiya tana waigen jiminar har ta taka enterest din Hammah,, wanda ya I daidai da faduwar gabanta.

Faduwar da ta kwashe duk wani kuzari nata, a haka ta karasa tangamemen falon, wanda yake zagaye da kujeru na alfarma sai sanyin ac.

Tana tunanin inda za ta nufa ta ji takun mutane alamun ana sakkowa daga matattakalar da ta ratsa falon.

Kafin ta dauke idonta Hammah ya bayyana cikin dakakkar blue din shadda, yayin da Aunty Adama ke bin bayan shi cikin kwalliya mai nuna cewar daula ta zauna mata..

Cikin tsokana Hammah ke fadin “Amarya ta zo gidan angonta”

Aisha ta yi kasa da kai tana murmushi, yayin da Hammah ke taya ta, Aunty Adama kam da yake yaren marghi ce ba ta san me ya ce ba, ba komai take ji a fulatanci ba, kalma biyu kawai ta gane a maganar ta shi wato “Gorko, da kuma debbo” bayan nan ba ta fahimci komai ba.

Hammah ya kasa dauke idon shi a kan Aisha bai tsammanin haka take ba, kuma ya dauka karamar yarinya ce da ba ta wuce 10-11years ba

Sai ya ga kyakkyawar matashiyar budurwa kamar ita ce ta ce haka za a yi ta.

Tun daga wannan lokacin, Hammah bai kara samun nutsuwa ba, sai da ya je Gembu, ya yi fafutukar da iyayen Aisha suka karbi bukatarshi ta auran mishi diyarsu.

Daga lokacin da aka sanya lokacin auran Aisha da Hammah, ƴan zuga ke sintiri tsakanin Yafendo da kuma Aunty Adama.

Ita dai Aunty Adama jaddada mata ake yi lallai kar ta bari a auro mata yar cikin ta, yayin da Yafendo ake fada mata sai ta tashi tsaye, saboda Aunty Adama ba ta barin kishiya ta zauna, duk macen da Hammah ya auro sai Aunty Adama ta kore ta, Aisha ita ce mace ta biyar, kuma ta da Hammah ya aura Aunty Adama ta kora.

Kamar wasa da lokacin biki ya zo sai maganar ta shiriri ce har ya kai tsakanin Hammah da Yafendo babu wani wanda yake maganar auran. Sai can Baffa ne ke tuntubar su.

Jin babu wata gamsasshiyar magana ya sa ya ce su Yafendo su taho gida yana son ganinsu.

Zuwansu gidan ne ya ga fahimci an bi Malamai da bokaye ne wajen shiriritar da maganar auran.

Shi ma sai ya dukufa na shi aikin, cikin sati daya da zuwan Aisha sai ga Hammah har guda, bai kuma koma ba sai da auran Aishar a kansa.

Duk da ba kowa ne ya goyi bayan auran Aisha a dangi ba, saboda tsoron abin da ka je ya zo.

Amma Baffa ya karfafa musu gwiwa a kan Aisha ta fi karfin wulakanci a wurin Hammah bare kishiya.

Adama (Aunty Adama) auran saurayi da budurwa suka yi da Hammah tun ba shi da komai

Garinsu daya, kuma yare daya, inda ta haifa mishi yara biyar duk mata.

Karima ita ce ta farko, wacce a Abuja take aure, Zubainatu ta biyu, ita kuma tana Maiduguri, daga nan sai Nafisa ita kuma a Yobe take aure, Sai Nazeefa wacce take aure a Kaduna, Huzaima ita ce autarta ita ma a Abuja take aure, dukkansu da yaransu.

Aunty Adama tana da zafin kishi, shi ya sa ba ta taba barin wata mace ta zauna da Hammah lafiya ba, duk wacce ta yi wata uku a gidan tabbas ta ciri tuta.

Sai Aisha ce kawai ta karya wannan tarihin.

Kamar yadda Baffa ya fada Hammah bai taba yi wa Aisha wani abu na wulakanci ba, komai ta bida tana samu, saboda a gidanshi ta karasa secondary, ta yi karatun nursing bai taba gazawa ta nan fannin ba.

Abu daya ne bai shiga tsakaninsu shi ne mu’amala ta aure har ta shekara hudu a gidan Hammah bai taba kusantarta ba, Sai watarana kwatsam ya dawo gidan da rana ya iske ta kitchen tana aikin abinci, a nan ya kusance ta, kuma a ranar ne aka samu cikin Abdul’azeez.

Cikin da aka sha gwagwarmaya wajen rainon shi, tun daga lokacin da Aunty Adama ta farga da samuwarshi.
Haka suka rika fafata kishi a karkashin kasa, don ma ba ta shigar da yaranta a kishin nasu ba, kowa ba dai sa shiga harkarta kuma basu rainata ba.

Ba kunya ko tsoro Adama ta ce yaron da za ta haifa sai ta ji dama ba ta haife shi ba, saboda ba za ta taba amfana da shi ba. Sannan ta kara jaddada mata ko a mafarkinta ba za ta kara hada shimfida da Hammah ba.

Ku san duk abin da Aunty Adama ta fada sai da suka faru, domin ga dai Abdul’azeez nan kullum cikin takaicinshi take, ya ki makaranta ya ki kasuwa, ga sata kamar bera. Abu daya ne bai yi shi ne neman matan banza.

Sun yi maganin har sun gaji sun zubawa sarautar Allah ido.

Kuma tun daga wannan lokacin Hammah bai kara kusantarta ba, sai yau din nan, ji take kamar wani mafarki, saboda ta fitar da rai da irin wannan ranar a jerin ranakun da suka rage mata

Ba ta taba fadawa kowa wannan sirrin nata ba, kuma ba ta jin za ta iya fada ma wani, addu’a kawai take yi, duk lokacin da ta je Hajji ko Umrah, a kan Allah Ya kawo mata karshen abun, fatan Allah Ya sa yau ce ranar karshen damuwarta a wannan bangaren.

Ajiyar zuciya ta sauke hade da tashi ta isa wurin kofarta ta murza key da Bismillahi, kafin ta wuce toilet don tsarkake kanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Da Magana 18Da Magana 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×