Skip to content
Part 22 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Karon farko da Ya Azeez ya daukar min abu na ji zafi har da kuka, sai da na gamsar da kaina da kaina na yi kuka, sannan na mayar da akwakun a kan mirror, tare da addu’ar Allah Ya yanke mishi wannan hali na dauke-dauke da yake fama da shi.

Su Aunty basu dawo ba sai magariba, zuwa lokacin tuni na gama abinci, na kara gyara falon

Bayan ta natsa cikin daki ne na kai mata abinci, loma biyu kawai ta yi ta fara amai, halin da take ciki sai na fara jin haushin cikin, da kyar ta sha empty tea ya zauna.

Wanshekare Hammah ya canjawa Aunty sabon tv, na san kuma zai biya sarkokinta da Ya Azeez ya kwashe mata.

Aunty kam na jin jiki, faten tsaki (na masara) mai yakuwa shi kadai take iya ci ya zauna, haka nai ta fama da hidimarta, ga dog Shi ma sai Ina wurin tsare da shi yake cin abinci, idan har zan kai in juya to ba zai ci ba, ga kuma school mun koma, sai komai ya min yawa, Ya Azeez kam ban kara ganin shi gidan ba, dama kuma haka yake yi, da zarar ya kwashi abin da ya kwasa ba mai ƙara ganin shi sai kura ta lafa.

Juma’a da misalin karfe biyu na dare na rika jin haushin dog ba ƙaƙƙautawa

Da hanzarina na fito falo hade yaye labulen window da zan iya gano tsakar gida, ban ga komai ba, kuma har zuwa lokacin haushi yake ba karami ba.

Wannan ya sa na fita kai tsaye na doshi inda suke, da yake cage nasu yana ta ɗan bayan ginin Hammah ne, hakan ya sa na yi mummunan gani. Duk da an kashe wutar gidan.

Wasu mutane ne tsirara ko wannensu rike da koko a hannu yana wanka, kamar yadda hasken farin wata ya haskaminsu haka su ma ya haska musu ni, bangarena ban taba gani ko jin abin da ya ban tsoro ba irin wannan, gabadaya na rike ce, ni ban yi gaba ba, kuma ban yi baya ba, kirjina kuma wani irin bugu yake kamar ana buga gangar tauri.

Da hanzari na juya baya zuwa dakina, har zuwa lokacin jikina rawa yake yi, kuma ban daina ganin hoton abin da na gani yanzu a idona ba.

Koda wasa ban runtsa ba har asuba, zuwa lokacin kuwa wani irin ciwo kaina ke yi kamar zai fadi kasa, ga tsananin faduwar gaba, a haka na yi wa Aunty faten tsakinta na kai mata, ni kuma na hada empty tea na zauna kan dining a kokarina na tursasa kaina na ganin na karya, daidai lokacin na ji bugun kofa, gabana ya kara wata sabuwar faduwar, a haka na nufi kofar na bude.

Hammawa da ke tsaye ya ce “Zo ki ga Dog Anya lafiyarshi kalau kuwa?”

Tsakanin dire maganarshi da fitowa ta gabadaya zuwa inda dog yake ban san wanne ya riga wani ba, har da gudu nake hadawa ban damu da rashin takalmin da ban sanya ba.

Ina shiga na hango Dog kwance, ganina ya sanya shi kokarin tashi amma sai ya kasa, wannan ya kara rudar da ni, da kaina na rika tayar da shi, amma sai ya koma ragwaf ya kwanta.

Na mamutso shi jikina ina fadin “Dog ba ka da lafiya ne, ko an yi ma wani abun ne?”

Kallo na kawai yake yi, na juya gun monkey wanda Shi ma yanayinsa ya nuna jikinsa a mace yake na ce “monkey me ya samu dan’uwanka?”

Sai ya juya yana kallon Hammawa.

Na yi saurin kallon Hammawa ina fadin “Ko ka yi mishi wani abu ne?”

Ya yi saurin daga hannayenshi du biyun tare da fadin “Ni! Wallahi ban yi mishi komai ba, me zan yi mishi?”

Ganin kamar ina ɓatawa kaina lokaci ne ya sanya ni mikewa na kwasa da gudu zuwa apartment din mu, wayata na dauka na shiga kiran Ya Azeez amma bai daga ba, dama na san da wuya ya daga kila ma ko tashi a bacci bai yi ba.

Na kuma shekawa wajen dog, yadda na kara ganin jikin na shi ya sa na kuma shekowa da gudu na haura wurin Aunty.

Yadda na banko kofar ne ya sanya ta saurin tashi zaune daga kwance da take.

Sai kawai na fashe mata da kuka, a firgice ta ce “Me ya faru?”

Maimakon in amsa ta, kasa na zauna daɓar tare da kara sautin kukan, kamar an ce min an jima kadan zan mutu. wannan ya sa ta kara rudewa, ta shiga tambayata “Lafiya, me ya faru? Ki fada min mana.”

Cikin kuka na ce “Aunty don Allah ki zo mu kai dog asibiti ba shi da lafiya, kuma na kira wayar Ya Azeez bai daga ba”

Baki ta bude tare da jan tsoki ta ce “Yanzu duk wannan saboda kare ne Maryam, ba zan je ba, ya mutu mana”

Na kara fashewa da kuka ina mata magiya a kan ta taimaka don Allah ta kai mu asibitin.

Ba don ta so ba, ta dauko keyn mota rai a bace ta yi hanyar kofar fita, na bi bayan ta har zuwa lokacin kuma kuka nake yi sosai.

“Haka za ki je asibitin ba takalmi, ba hijab ba dankwali? Wlh Maryam ki shiga hankalinki, Allah zan fasa kai shi asibitin” cikin fada take yin magana yayin da take nuna ni da yatsanta

Da sauri na koma ciki na dauko wayata, hijab da takalmi, ni ce na kinkimo dog Har cikin motar, na zauna a back seat na rungume shi, ko nauyinshi ba na ji

Har zuwa lokacin kuka nake yi, shi kuma ya yi min zuru da ido yana kallona, na san da yana da baki kila zai fada min abin da ke damun shi, ko abin da aka yi mishi, kila ma ya kara da fada min magana da za ta dan kwantar min da hankali.

Tausayinshi ya kama ni, wasu sabbin hawaye suka kuma zubo min, na rika shafa gashin jikin sa cike da tausayawa, shi kuma ya kwantar da kanshi a kan kirjina , Aunty kuma fada kawai take yi, ni ban san ma abin da take cewa ba, na dai rage sautin kukana, saboda na fahimci kamar shi ke kara tunzura ta.

Bangare daya kuma ji nake sam ba ta tafiya, kamar in ce ta tsaya in sauka in tafi da kafafuna.

A haka dai muka isa hospital din, ban jira Aunty ba na kimkimi dog zuwa office din da mu ka ga likita wancan zuwan da mu ka yi, sosai dog yake da nauyi shi ya sa wajen hawa barandar da za ta sada ni da office din likitan na fadi, ban damu na ji ciwo ko ban ji ba, na kuma ciccibar dog na shiga office, na manta ma ana bin layi.

Ina shiga na zube dog a gaban likitan, cikin matsanancin kuka mai dauke da tashin hankali na ce “Don Allah ka duba min shi, ba ya da lafiya, don Allah kar ka bari ya mutu. Don Allah!” na karasa maganar cikin kuka mai nuna raunin da zuciyata take ciki.

Ya dauke idanunsa a kaina ya mayar kan dog, kafin ya daga bisani ya daga shi zuwa wani gado da ke cikin office din,sannan ya kira wasu nurses guda biyu suna taimaka mishi, ni kuma na koma kan kofar shiga office din ina hangensu, lokaci zuwa lokaci kuma Ina sharce hawayen da ke bin kuncina, da alama Aunty ba ta biyo ni ba, saboda ko mai kama da ita ban gani ba a kan barandar.

Na kasa jurewa na isa gadon da Dog ke kwance, cikin karyayyar zuciya na ce “Don Allah me ya same shi?”

Likitan ya juyo yana kallo na, kafin ya ce “An yi mishi allurar guba ne.”

Ido bude baki bude na ce “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! To akwai sauki kuwa?”

Ya ɗan yi shiru kamar ba zai amsa ni ba, sai kuma ya ce “Mun ba shi duk taimakon da ya kamata mu ba shi, sai dai mu jira abin da Allah zai yi, saboda gubar ta jima a jikin shi”

Yanzu kam shiru na yi cike da tashin hankali, kamar ba na office din, kuma ban san abin da nake tunani ba.

Vibration din wayata ne ya dawo da ni cikin hankalina

Ganin Ya Azeez da sauri na daga, daga can ya ce “Me ye faru na ga kiran ki?”

Dama kamar jira nake sai na fashe da kuka, cikin kukan ne na ce “Ya Azeez dog ba shi da lafiya?”

Cikin sauri ya ce “Me ya same shi?”

Cikin kuka na ce “Likita ya ce wai allurar guba aka yi mishi”

“Oh my God!” Ya fada cike da tashin hankali kafin ya ce “Kuna asibiti kenan?”

“eh” na amsa hade da dauke hawayena

“I’m coming”

Bai jira cewa ta ba, ya yanke kiran.

Na matsa sosai kusa da Dog na rike kafarshi ta gaba, Sai ya bude ido yana kallo na, na duka a saitin fuskarshi ina shafa gashinshi, a hankali na ce “I’m very sorry dog, za ka warke Sha Allah, mu koma gida mu ci gaba da rayuwarmu. Kuma Allah Ya saka maka, idan kana da hakki a kan wanda ya yi ma wannan abun Allah Ya bi ma.”

Ya lumshe ido a hankali na dago daga duken da nake jin an turo kofa, Ya Azeez ne a hanzarce ya mikawa likitan hannu, sannan suka kara so wurin inda muke, yana yi wa Ya Azeez bayanin abin da ke damun dog, tare da fada mishi matakin da suka dauka, da kuma abin da suke fata.

Ya karaso sosai wurin dog tare da shafa gashin shi yana kiran sunan sa, ya bude ido kadan, Sai ya yi kissing din goshin shi hade da fadin “Sorry, wish you quick recovery”

Rufe bakinshi ya yi daidai da fitowar kumfa a bakin dog, haka kumfar ta rika fitowa Ya Azeez na sarewa da tissue, yayin da damuwa take dankare a kan fuskarshi, likitan kuma karfafa mana gwiwa kawai yake wai sha Allah zai warware.

A hankali ya rika motsa kafafunshi, idanun ma dakyar yake bude su, ni da Ya Azeez ban san wa ya fi wani shiga damuwa ba, Ya Azeez kam cewa Doctor yake don Allah kar ya bar dog ya mutu, saboda duk wasu alamun mutuwa sun bayyana a gare shi. Ni dai kukan ma kasa yin shi na yi.

Haka ya rika mimmikewa a gadon yana wani irin kuka mai ban tausayi, ni da Ya Azeez muka rirrikeshi tare da shafa gashin shi, dakyar yake bude ido ya kalle mu.

lokacin da na tabbatar rai ya yi nisa da gangar jikin Dog wasu hawaye masu zafi suka sauko min, ba hawayen mutuwar dog kawai nake fitarwa ba, har da na yadda aka zare ranshi, Annabi S. A. W ya yi gaskiya, dama ya ce babu abin da ya kai fitar rai zafi, na kara gasgatawa da yadda aka zare ran dog, baki bude yayin da idanunsa suke kafe suna kallon sama, kafar shi ta gaba guda daya a cikin tafin hannuna da kanshi ya dora kafar, ni kuma na rika murza mishi ita a hankali, ya kan bude baki dakyar kamar mai son yin magana amma ya gagara yi. Dabba ma kenan ina ga mutum kuma.

Ya Azeez kam dukewa ya yi gaban gadon, ba kuka yake yi ba, amma abin da yake ji gara ya yi kukan, wani abu mai zafi gami da tukiki ne ke mishi yawo a kirjin shi.

Ya tuna lokacin da ya dakko dog, tun yana yaro aka kashe uwarshi, shi kuma ganin baya samun kulawa sai ya dakko shi, da farko a otel ya fara aje shi, kafin daga bisani ya kai shi gidan Madina, sai kuma ya dakko shi daga gidan Madinan ya kawo shi gida, wani irin so yake mishi, ko me yake yi hankalinsa na a wurin dog, akwai wata shakuwa ta musamman a tsakaninsu, wanda yake kiwon kare ne kawai zai fahimci yadda yake ji a yanzu .

Ni kam kuka nake yi sosai, kamar dai an ce min Aunty ta rasu, daga karshe ma waje na fita na zauna gefen baranda na rika kuka kamar shi ne abin da ya kawo ni asibitin.

Ina tsaka da kukan ne na ga Ya Azeez ya fito rungume da dog, daga yadda yake tafiya za ka fahimci ba lafiya yake ba, kafin in isa gare shi har ya shiga mota ya yi mata key.

Wannan ya sa na nufi inda Aunty ta parker tata motar.

Ta rika bina da kallo kamar ranar ta fara gani na.

Na isa wurin ta, kallon da take min sai ya kara raunana min zuciyata, na kifa kaina a marfin motar tare da fashewa da kuka, kuka mai nuna cewa akwai kunci a zuciyata.

“Ya aka yi kuma?” Ta tambaye ni cike da kosawa,

Cikin shesshekar kuka na ce “Dog din ya mutu”

Zumbur na ga Aunty ta yi, hade da fitowa daga motar tana fadin “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Subhnallah”

Mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki, ai sai zuciyata ta kara narkewa na kuma kara fashewa da wani sabon kukan.

Ta zagayo inda nake tare da rungumoni jikinta cikin sigar lallashi hade da jimami take fadin “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Wlh ban san mutuwa zai yi ba, da gaske na ji mutuwarshi Allah Ya ba ku ladan kiwon da kuka yi mishi, tabbas babu dadi, ki yi hak’uri kin ji”

Kuka nake yi sosai, yayin da duk maganar Aunty daya ke kara narkar min da zuciya, da kanta ta sakani cikin mota tana tambayar “Yana ina yanzu?”

Cikin kuka na ce “Ya Azeez ya fita da shi.”

“Yaushe Azeez din ya zo?”

“Ba jimawa” na kuma amsa ta cikin kuka.

Shiru ta yi alamun jimami, kafin “ta ce waye zai yi wa Dog allurar guba?”

“Ban sani ba ni ma” na amsata hade da share hawayena

“Ko waye ya yi mishi haka Allah ya saka mishi, gaskiya ya cuceku, ni kaina kuma ban ji dadi ba. Allah Ya tona asirin ko waye”

“Amin” na amsa cikin kuka.

<< Da Magana 21Da Magana 23 >>

1 thought on “Da Magana 22”

  1. Ina lada a kiwon kare kam? Ai sai dai zunubi, Allah ya yafe musu da masu kiwon kare irin su, ya yafe mana kura-kuren mu wanda muka sani da wanda bamu sani ba kuma. Amma ba wani fa’ida a ajiye kare a gida indai ba gadi zai yi maka ba. Ni ba abinda yake bani takaici a zamanin nan irin yanda aka yi normalising ajiye kare a gida, ‘ya’yan musulmi su rika rungume kare abin kyama, so disgusting.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×