"Ikon Allah!" cewar Aunty muryarta cike da madaukakin mamaki.
Ta dauke idanunta daga kallon kofar fita zuwa kofar dakina.
Muka hada ido, saboda tun lokacin da na fahimci Hammah ya fita na fito ni ma.
"Anya Hammah lafiya yake?" ta yi tambayar idanunta cikin nawa
Cike da mutuwar jiki na langabar da kai tare da watsa hannuwana alamun ni ma ban sani ba.
Duk mu ka yi shiru kafin ta taka zuwa stairs din da zai sada ta da dakinta
Ni ma cike da sanyi jiki na koma dakina.
Na kasa gane tsakanin mamaki da fargaba wanne maganar Hammah ta. . .