Skip to content
Part 24 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Ikon Allah!” cewar Aunty muryarta cike da madaukakin mamaki.

Ta dauke idanunta daga kallon kofar fita zuwa kofar dakina.

Muka hada ido, saboda tun lokacin da na fahimci Hammah ya fita na fito ni ma.

“Anya Hammah lafiya yake?” ta yi tambayar idanunta cikin nawa

Cike da mutuwar jiki na langabar da kai tare da watsa hannuwana alamun ni ma ban sani ba.

Duk mu ka yi shiru kafin ta taka zuwa stairs din da zai sada ta da dakinta

Ni ma cike da sanyi jiki na koma dakina.

Na kasa gane tsakanin mamaki da fargaba wanne maganar Hammah ta sanya ni

“Wai Bandi” na maimaita a hankali tare da daga idona ina kallon zanen hoton dog.

Na kurawa zanen ido har zuwa lokacin da ya fara canja min zuwa suffar wani katon mutum mummunan gaske, idanunshi jazur kamar an zuba mishi jini.

A guje na fice daga dakin yayin da zuciyata ke wani irin bugu, jikina sai rawa yake yi.

Daidai lokacin Aunty ke sakkowa daga stairs din dakin ta, kiran sunana da ta yi sai ya kara tsorata ni na zabura

Ta karasa sakkowa hade da kare min kallo tana fadin “Lafiya? Me ye a cikin dakin?”

Cikin muryar tsoro na ce “Ba komai”

“Are sure?” ta kuma tambayata har lokacin kare min kallo take

Kai na daga alama eh

Kofar dakin ta tura hade da shiga har cikin toilet din ta fito ta korafi

“Wasu malaman sun ce ba kyau aje hoto a daki, amma ke kin dakko hoton wani katon kare kin manna, ko shi ai ya isa ya ba ki tsoro.”

Ni dai komai ban ce ba, har ta wuce kitchen.

Wunin ranar a falo na yi shi, hatta wanka fakar idon Aunty na yi, na yi shi a dakin Ya Azeez.

Hatta bacci a falon na yi shi ba tare da sanin Aunty ba.

Na wayi gari Sam babu dadi, shi ya sa ban iya komai ba.

Sai da gari ya gama wayewa sosai ne na fito rike da abincin monkey da zummar kai mishi.

Saukata kan entrance din ya yi daidai da ganin wasu mutane tsirara ba fasali sun tun karo ni, ban san lokacin da na watsar da farin da ke hannuna na fasa kara ba, tare da juyawa da gudu.

Lokacin da na shiga falon ba kowa, shi ya sa na yi tsaye tsakiyar falon a tsora ce.

Ina ta tsaye a wurin na ji takun sakkowar Aunty cikin shirin fita.

Har ta sakko ban dauke idanuna daga kanta ba

“Are you alright?” cikin kulawa ta tambaye ni

Na janye idona a hankali daga kanta tare da gyada mata kai

“Ba za ki je school din ba, ko har yanzu jikin ne? Na ji kamar kin ce yau kuke komawa.”

Take na shiga lalubo abin da zai fisshe ni, tsakanin tafiya makaranta da kuma zama a gida.

Ni dai yanzu ba na son abin da zai hada ni da shiga dakina, kuma ba na fatan abin da zai rike ni a gida ni kadai

Ya fi ma in tafi makarantar tun da can akwai mutane.

Da wannan tunanin na yi shahadar ƙuda na fada dakina, bakina dauke da kalolin addu’a

A haka na yi wanka, amma ko alama ban wanke fuskata ba, saboda tsoro.

Shirin ma a falo na karasa shi, uffan dai Aunty ba ta ce min ba, cin abincinta kawai take yi.

Kadan na taba abincin muka fita.

“Waye ya zubar da wannan kuma, ba abincin Birin can ba ne?” ta yi tambayar lokacin da muka fita ta yi arba da kayan marmarin da na watsar a kasa.

Na shiga tattarewa ba tare na ce komai ba, ita din ma ba ta kara maganar ba, illa ta wuce wajen da motarta take.

Bayan na tsince fruit din, na kaiwa monkey, kafin nan mu ka wuce.

Ko a school din ma ban da kuzari, saboda idan na cika kallon mutum sai in ga yana canja min zuwa suffar daban.

Har na rika jin ina ma ban zo ba. Koda muka tashi ma dakyar na isa gida, inda Allah Ya taimake ni na samu Aunty ta dawo.

Tun da na shigo take kare min kallo, Sai da na kusa shiga dakina ne ta ce

“Maryam zo nan”

Ba musu na juyo zuwa inda take

“Me yake damunki, cikin kwanaki kadan kin rame kin yi baƙi, me ye matsalar?” cike da kulawa gami da tausasa kalamai take min maganar

A sanyaye na ce “Ba komai”

Ba tare da ta dauke idanunta a kaina ba, ta ce “ko maganar Hammah ne a kan Bandi. Idan ita ce ki saki jikinki, ba zan bari a aura miki wanda ba kya so ba. Ballantana ma bai kara maganar ba.”

Hawayen da suka gangaro min dauke ba tare da na ce komai ba.

Haka ta rika lallalashina da maganganu masu kwantar da hankali.

Abin da ba ta sani ba shi ne, matsalata ta fi gaban Uncle Bandi, saboda ni na manta ma da batunshi, baccin da ban samu kadai ma ya ishe ni, bare kuma a juyo wajen batun rashin sakewa, ko kadan ba na son in kadaice ni kaɗai, kwanciyar hankalina kuma shi ne kar in matsa a kallon abu.

Ko tv na faye kallo sai in ga mutanen ciki suna canja min zuwa wata halitta daban.

Ita kanta Auntyn wani lokaci canja min take yi.

Dakina kam ya fi karfin zamana, Sai falo ko in faki ido in shiga dakin Ya Azeez in yi wanka ko wani abun.

Zuwa wurin monkey man sai da dabara, ko in kira Hammawa ya kwanto min shi.

Haka na rika rayuwa tsawon wata daya, kuma kullum abu gaba yake ba baya ba, amma ban fadawa kowa ba. Aunty dai kullum cikin tuhumata take ko tambayata a kan me yake damuna

Amsata dai ita ce ba komai.

Amma hatta school sai da na aske zuwan ta, na cewa Aunty ban lafiya , saboda idan na je duk ƴan makarantar canja min suke zuwa sifa irin ta Zombie.

Idan ta tafi aiki sai in fito wurin Hammawa, a nan nake zama, har ta dawo sannan in koma ciki.

Bacci kam sai rabi da rabi shi ma a falo da bulb a kunne, ni ce kawai na san tashin hankali da nake fuskanta, duk na susuce na yi baki na rame. Kallo daya za ka min ka tabbatar ba ni da lafiya.

Aunty kam sosai ina ganin damuwar canjina a kan fuskarta, ga lalurin ciki, wanda ba kowa ne ya san da shi ba.

Amma haka nan take bakin kokarinta wurin ganin na koma normal.

Kamar yanzu ma da muke zaune a falo, hannunta rike da waya tana nuna min wasu set na kayan jarirai da take son saye, dukkanmu hankalinmu yana kan hoton, aka kwankwasa kofa

“Waye? Shigo, kofar a bude take” Aunty ta fada lokaci a daya.

Na mayar da kallona zuwa kofar, inda Ya Azeez ya shigo kamar kullum sanye cikin kananan kayan da suka fitar da kyawunshi

Almost 1week rabon shi da gidan

Daga ni har Auntyn muka rika bin shi da kallo har zuwa lokacin da ya shigo cikin falon sosai.

Cike da tsokana Aunty ta ce “Har kun tashi daga zaman majalisar?”

“Wace majalisar?” Ya tambaya cike da rashin fahimta.

“Ta Nigeria mana, ko ba kai ne ka fanshi Madinan ba”

Duk yadda nake jin ba dadi, sai da na murmusa, abin da ya sanya na karɓi tukuicin harara daga wurin shi.

Ya zauna a hannun kujerar da ke kusa da Aunty tare da fadin “Ni yaushe rabona ma da ita.”

“Kun fasa auran kenan?”

Ya dan yi shiru hade da yin dariya kasa-kasa

“Da ka lallaba ka aure ta wlh, saboda ita ce daidai auranka, to idan ba ita ba Azeez wace mace za ta aure ka, kai ba karatu ba, ba aiki ba, ba kasuwa ba. Sai Shirme. Shirmen ma na banza da wofi.”

“Kai Aunty!” Ya fada hade da mikewa tsaye yana cusa hannunshi cikin aljihun wandonshi

“To karya na yi?”

Bai amsa ba ya juyo inda nake zaune tare da fadin “Wai ita wannan har yanzu ba ta da lafiyar?”

Ita ma ta juyo da kallon ta zuwa sashena tare da fadin “Uhmm! Ai ni lamarin Maryam ma tsoro yake ba ni, ka ganta nan kullum jiya iyau, duk ta bi ta bushe, makarantarma yanzu almost 1month ba ta je ba”

“To me ke damunta?” Ya tambaya idanunsa a kaina

“Ita ta sani” Aunty ta ba shi amsa

“Ke me ke damunki?” ya juyo da tambayoyin zuwa kaina

Na aje kai a kasa ban ce mishi komai ba

Sai Aunty ce ta ce “Ni ina expecting a kan maganar Bandi ne, saboda tun da Hammah ya ce zai ba wa Bandin ita ba ta kara lafiya ba”

Tabe baki ya yi kafin ya ce “Ni hado min nono idan akwai, idan kuma za ki iya” ya kai karshen maganar hade da nufar sashenshi. Aunty kuma ta mayar da hankalinta a kan wayarta

Kamar zan fadi haka na shiga kitchen na hado mishi nono da dakkere, na wuce Aunty a falon zuwa dakinshi.

Wani abu da Ya Azeez ke kiyayewa shi ne tsiraici, zan iya rantsewa tun da na zo gidan ban taba ganin shi da gajeren wando ba

Vest ma ba ko wane lokaci ba, idan kuwa har zai zauna da vest, to za ka samu wandon jikinshi dogo ne ko kuma ya wuce gwiwa.

Yanzu din ma zaune yake a gefen gado yana taba wayar shi, ba na jin tun da ya shigo dakin ya taba wani abu ko ya cire wani abu daga jikinshi.

Shigowata ce ta sanya shi dago kai yana kallo na.

Na yi saurin runtse idona, na kuma bude su a kanshi, still bai canja min daga yadda nake kallon shi ba a lokacin da na shigo

Cup din na yar a kasa hade da zunduma ihu na juya baya da gudu.

Tsakanin shi da Aunty ban san waye ya riga kawo min dauki ba.

Domin dai kafin in isa falo Aunty ta shigo corridorn, shi ma kafin in fita daga corridorn ya fito

Sai suka sanya ni a tsakiya, jikina sai rawa yake yi ina kuka.

“Me ka yi mata?” shi ne abin da Aunty ta fara tambaya

“Ban yi mata komai ba, tambayarta ga ta nan” ya amsa da yanayin kamar ya tsorata

“Me ya yi miki?”

Na girgiza kai alamar ba komai.

Takowa ta yi sosai zuwa inda nake, cikin fushi ta ce “Za ki fada min abin da ya miki ko sai na ci uban ki”

Cikin kara sautin kukana na ce “Bai yi min komai ba”

“Karya kike yi, za ki fada min ko sai na dauke fuskarki da mari?”

Ta kuma fada tana kara matsowa kusa da ni

Na rika ja baya cikin kuka ina fadin

“Wlh bai yi min komai ba.”

Cikin fada Aunty ta ce “Wlh Maryam zan ci ubanki, wannan abun na ki ya ishe ni. Just tell me me yake damun ki.” ta kai karshen maganar tana kara matsowa kusa da ni

Sai kawai na fashe da kuka sosai, ba na son kara tayar mata da hankali, musamman a yanayin da take ciki na yau lafiya gobe babu, don ma mace ce jajirtatta.

Wata tsawar ta kuma daka min” Za ki fada min ko sai na sanya Azeez din ya zane min ke”

Ganin yadda take matso ni, sai na ruga bayan Ya Azeez na buya ina kuka.

“Please Aunty, zan tambaye ta da kaina, just go”

Cewar Ya Azeez cikin tausasa murya

Ba ta ce komai ba haka kuma ba ta tafin ba sai wajen after 5mns sannan ta juya a fusace.

Ya juyi sosai muna fuskantar juna, zuwa lokacin kuma na dan rage sautin kukana.

Hannuna ya rike zuwa dakinshi, ya zaunar da ni gefen gado, shi kuma ya tsaya a kaina. Har lokacin ban daina gunshekin kuka ba.

“Oya tell me exactly what’s wrong with you”

Ban amsa ba, amma ina ta kukana

“Ni fa ba lallashin ki zan yi ba, ke ma kin san ban iya ba, me ye matsalar ki” ya kuma idanunshi a kaina.

Ban amsa sai dai na rage sautin kukana sosai.

Center table ya janyo ya zauna ya fuskantata tare da fadin ina jin ki.

“Tsoro ake ba ni.” na yi maganar a hankali

“Kamar ya?” Ya a tambaye ni da alamun rashin fahimta.

A hankali na warware mishi abin da nake gani da yadda mutane suke canja min zuwa zombie. Na rufe da fadin
“Dazu ma da na kawo ma nono gani na yi ka canja min kamanni shi ya sa na tsorata”

Ido ya kwakkwalo hade da mikewa tsaye a zumbur, cikin murya mai kama da tsoro-tsaro, mamaki-mamaki ya ce

“Kai!”

<< Da Magana 23Da Magana 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×