Skip to content
Part 3 of 26 in the Series Da Magana by Matar J

“Maryam! Maryam!!” Haka Aunty ta shiga jero sunana lokaci daya kuma tana knocking kofar da karfi.

Cikin sanɗa na karaso wajen kofar, a hankali na murza key din tare da bude kofar, na ja baya hade da kallon Aunty wacce hannunta ke rike da wuka

“Ya ji miki ciwo?” ta yi tambayar idanunta na yawo a jikina.

Kai na girgiza alamar a’a

Shigowa ta yi dakin sosai, tana fadin “Oh ni Aishatu, Ya, zan yi da wannan yaro? Allah me na yi maka?”

Ta kai karshen maganar cikin sakin kuka, wannan ya tabbatar min da hankalinta sosai ya tashi.

“Aunty bai yi min komai ba.” na yi maganar hade da nuna mata hannayena, wai ko hankalinta zai dan kwanta.

Cikin muryar kuka ta ce “Maryam ba maganar yanzu nake yi ba, ina maganar nan gaba ne, kullum Azeez kara ƙiriricewa yake, zuciyarsa tana bushewa, yau Azeez ne da wuka, har yana ikirarin kashe wani, Maryam dole hankalina ya tashi.”

Gefen gadon na zaunar da ita, cikin sigar kwantar da hankali na ce” Don Allah Aunty ki daina daga hankalinki da yawa, kin san kina da BP. Addu’a za ki rika mishi Aunty. In Sha Allah zai shiryu.”

“Ke shaida ce Maryam Ina yi, har sanyawa nake a yi min, amma lamarin Azeez ba sauki, wlh yana matukar tayar min da hankali na irin rayuwar da Azeez ke yi Maryam.”

Shiru na yi, saboda yanzu ban san me zan ce mata ba, ko ba haka ba ma, ni har yanzu ba na cikin nutsuwata, har yanzu hankalina bai zauna daidai a jikina ba.

Ina kallon ta ta fice daga dakin tana share hawaye, da sauri na bi bayanta tare da dannawa kofata key. Ji nake kamar Azeez sa a yake nema, yadda na ga fuskarsa shimfide da bacin rai babu abin da ya zai hana shi ya burma min wukar hannunshi da ya kama ni. “Wai ni Allahna!” Na fada hade da zaro ido, hannayena du biyun dafe da kirjina.

Jiki a mace kuma na rika sauke hannuna daga kan kirjina saboda tuna halin da Aunty take ciki tana bukatar mai lallashinta a yanzu.

Aunty mutuniyar kirki ce, wacce abun ta bai rufe mata ido ba, mace mai faram-faram da son addini. Ba ita ce ƴar’uwata ba, amma na fi sakewa da ita fiye da Hammah wanda ya kasance yaya a wurin mahaifiyata uwa daya uba daya.

Tun daga lokacin da mahaifiyata ta rasu ina jss 3 rikona ya dawo hannun Aunty, ita ce ta ci gaba da kula da ni har na kammala secondary school, na zana jamb inda na cika makarantar koyan aikin jinya da ke Yola. Wannan shi ne zabin Aunty, kila ko don shi takaranta, ni dai tun da ta yi min sha’awar bangaren sai na ji Ina so, ko ba komai ni ma zan yi mata wani abu guda daya da take so.

Azeez shi ne ɗa daya tilo da ta mallaka, daidai gwargwado ya samu tarbiya, saboda Aunty ba ta cikin irin mutanen nan da kudi suke da sanya su, su sakalta yaro.

Lokacin da na zo na san Azeez mai kokarin zuwa makaranta, sannan mai dimbin baiwa a bangaren zane-zane, a wancan lokacin idan an ba ni Assignment din zane a bangaren biology, shi nake kawo mawa ya zana min, in Sha Allah kuwa sai na cinye, har ta kai ga idan ina note na zo wajen zane tsallakewa nake yi, Sai in ari littafin wacce ta yi zane in kawo mishi, ya zana min.

Lokacin da ya zana jamb, yana daya daga cikin daliban da suka samu points mai yawa, hakan ya sa Hammah ya ce zai kai shi Kasar waje ya yi karatu a bangaren zane-zane kamar yadda Ya Azeez din ke so.

Na yi murna sannan na ji ba dadi, saboda zan yi kewarshi, Ya Azeez yana daya daga cikin ƴan’uwan da nake matukar kauna, duk da ba wani shiri muke yi ba, amma kuma yana yi min duk abin da na ce ina so, ko na nuna ina so.

Ba jimawa aka samar mishi admission, aka kammala komai sai tafiya, sai dai wani abu da ya ba ni mamaki, daga Aunty, Hammah da kuma shi Ya Azeez ban kara jin wani ya yi zancen tafiyar ba, abun da ya ban, mamaki, musamman ma Ya Azeez da yake ta, ɗokin tafiyar.

Ni ce ma lokaci zuwa lokaci na kan tambayi Aunty in ce” Aunty wai Ya Azeez ya fasa tafiya karatun ne? “ba ta taba ba ni amsar wannan tambayar ba, Sai ma na ji wai an nemar mishi admission a Unimaid. Shi ma haka a kai ta shan ruwan tsuntsaye har dai aka samu ya tafi.

A can ma Maidugurin abun ƙi ya yi ga macuri, da ya cura sai ya wargaje, saboda Ya Azeez babu karatun da yake, sheke ayarshi kawai yake da abokanshi yaran masu kudi. Ba wai sheke aya ta shaye-shaye ko bin mata ba, kamar yadda wasu abokan na shi ke yi, a’a kawai shi sharholiyarshi yake yi, Ya ci mai kyau, ya sha mai kyau, ya kwanta a wuri mai kyau, ya sa mai kyau, ya hau mai kyau, babu test, babu Assignment, babu attending din class. Exam Sai Allah ya yi.

Kudi yake karba sosai a wurin Hammah da Aunty nan da nan zai ce ba shi da kudi, haka zasu tura mishi.

Babu wanda ya san halin da yake ciki sai da ya shekara daya. Sannan aka gano abin da ke faruwa, Hammah ya yi fada kamar zai ari baki, haka Aunty ma.

Daga lokacin suka rika sanya mishi ido sosai, saboda a can suka nemi mai lura da shige da ficenshi, irin sakamakon da suke karba ya sa dole Hammah ya cire shi, ya dawo da shi MAUTECH kusa da gida, to a nan ne fa har yanzu ake fafatawa, ba karamin kudi Hammah da Aunty ke kashewa a kan maganar makarantar Ya Azeez ba, amma exam kadai yake zuwa rubutawa, ita ma sai ya ga dama. To wani lokacin ma bai san ana exam din ba. Kuma har yanzu baiwar shi ta zane tana nan, kallo daya zai yi wa abu ya zana shi radau. Duk lokacin da ƴan zanen suka juyo mishi, ba karamin kudi yake samu ba, saboda yadda manyan-manyan mutane ke kawo mishi aiki. Baya yi wa yaku bayi zane, ko manyan ma sai ya ga dama.

Na sauke ajiyar zuciya mai dauke da murmushi a lokacin da na zo wannan gabar a tunanina.

Azeez mai aji ne, matashin saurayi wanda babu wata mace da ba za ta so ta mallake shi a matsayin miji ba, idan dai sura za ta kalla, nasaba da kuma masu gida rana.

Duk da ba dogo ba ne, amma kuma babu wanda zai kira shi da gajere kai tsaye. Chocolate colour, farin Aunty ya dakko da kuma bakin Hammah. Jikinsa a cike yake, yayin da alamar karfi ke bayyana ta kanta.

Dan gayu ne sosai, ban taba ganinshi da manyan kaya ba, Sai dai kanana latest masu zafi.

Da yawan takalmanshi kambas, ko wane kaya ya sanya za ka ga takalmi ya dace da kayan.

Yana da kyakkyawar sura, kominshi matsaikaci ne, idanuwa, hanci, gira da kuma baki, wannan zai nuna maka kominshi debowa ya rika yi daga wurin Aunty da kuma Hammah.

Sumarshi tana daya daga cikin abubuwan da ya fi kashewa kudi, ni kaina tana daya daga cikin abubuwan da ke jan, hankalina a jikinshi, kawai so nake inji hannuna a ciki ina yamutsata yadda nake so.

Abu na biyu da yake burgeni da shi, shi ne tafiyar shi, yadda yake yin ta da wani irin bouncing yana wani bubbudewa cike da mazantaka.

Akwai abubuwan burgewa sosai a tare da Ya Azeez, wanda ya sa da yawan ƴanmatan Family ke kawo mishi farmaki, duk da wasu sun san halinshi na sace-sace, amma bassa damuwa, su dai kawai ya so su.

Shi kuma kamar an shata mishi layi da mata, ba na jin a duniyarshi akwai mace da ke burge shi, kamar ma dai bai san akwai jinsin mata ba. Bai san wani abu soyayya ba, kamar dutse haka yake sam ba shi da shauki.

Shi dai ya yi wanka, ya sa kaya mai kyau, ya gyara sumarshi ya kuma hau mota mai kyau. Duk wani abu da ya shigo ya fi son a fara ganinshi a wurin shi. To shi kam ya samu wannan duniyarshi ta gama dadi.

A hankali na janyo kofar dakin na rufe bayan na fita, kai tsaye upstairs na dosa inda dakin Aunty yake.

Azeez

A harabar hotel din ya parker motarshi, cikin takunshi da ke jan hankalin ƴan mata ya nufi hanyar da za ta sada shi da dakinshi.

Har ya wuce, Sai kuma ya dawo hade da kwankwasa wata kofa.

Ba jimawa kofar ta bude Nasir ya leko daure da towel.

Wata harara Azeez ya aika mishi da ita sannan ya ja tsoki ya wuce zuwa kofar da ke gaba.

Key din da ke hannunsa ya saka tare murzawa, dakin gyare tsaf sai kamshi mai dadi, bisa gadon ya fada hade da jan dogon tsoki, sosai ya ji haushin yadda Maryam ta wargaza mishi budget.

“Shegiyar yarinya kawai.” ya fada hade mikewa zaune yana balle botiran rigar shi.

Nasir ya turo kofar hade da shigowa yana dariya.

“Dawa ta yi nama kuwa master?”

Ya kuma jan tsokin da ya zame masa jiki sannan ya ce “Ina fa! Yarinyar nan ce dai ta hade min kashi wlh, na so yau in farke ta.”

Da sauri Nasir ya ce “Ka farke wa? Maryam wai?”

“Yes. Shegiyar yarinya ta sanya min ido don ubanta, tana daya daga cikin dalilan da ke hana ni zuwa gida. Duk abin da nake yi idanunta na kaina.”

“No! No!! No!!!” Haka Nasir ya rika fada hade da girgiza kansa, kafin ya ce “Don’t ever try this please, you know how much I love her. Haba!”

“Kana son ta?” Azeez ya tambaye shi idanunsa kansa

“Yes.”

“Har mata nawa za ka so, ba ga wata can a daki ba.” Ya kai karshen maganar hade da mikewa yana zare wandonsa.

“Haba manta da waccan, do you think I will mary her. No I will not , Kawai tarayyar ta nan ce, in ba ta kudi ta ba ni farin ciki that’s all.”

Azeez bai yi magana ba illa tabe bakin da ya yi kawai ya nufi hanyar toilet.

“Madinah ta zo fa, har ma ta bayar da sako a ba ka.”

“me ta bayar?” Azeez ya yi saurin tambaya lokaci daya kuma yana baro hanyar shiga toilet, fatansa Allah Ya sa kudi ne, saboda wani agogo yake son saye da wasu kaya da yake son sanyawa a birthdayn da zasu yi jibi.

Dariya sosai Nasir ke yi kafin ya ce “Lallai yau kai ne da son jin sakon me Madina ta bar ma.”

“Dalla me ta bayar?”
Azeez ya kuma tambaya, bayan ya hade fuska.

Cikin dariya Nasir ya ce “Wlh dollars mutumina, kawai ka dan ba matar nan time ko kadan ne, wlh duk sai ka kara shiga gari fiye da yanzu. Tana sonka sosai, kuma ka ga akwai kaya a wajenta, takarar yar majalisa fa take yi, wlh ni na samu irin wannan haba, kawai zan bi yarima in sha kida abokina. “

“Dakko min kudin .” Cewar Azeez lokacin da yake zama gefen gadon.

“But promise me ba za ka bugar min mata ba” cewar Nasir yana kallon Azeez.

“Dalla Malam kawo min kudi kar ka bata min rai da zancen wannan banzar yarinyar, ba ka, san yadda raina yake bace ba ne a kanta, haushi na daya da ban taba lafiyarta ba. Shegen gudu tsil-tsil kamar barewa, da wasu shegun siraran kafafunta.”

“Kai! Masoyiyar tawa kake ma wannan maganar banzar?”

“Nasir!” Azeez ya kira sunan da karfi.

Wannan ya sa Azeez mikewa ya nufi kofa yana dariya.

Ba jimawa ya dawo hannunsa rike da wata yar farar leda, a kan gadon suka zazzage bandir-bandir din kudin.

Cike da farin ciki Azeez ya kwashi bandir biyu ya yi celebrating dasu, sannan ya juya inda Nasir yake tsaye yana fadin “Akwai daukar wanka wurin Bithdayn Faruq jibi, ta yi kyautar nan a daidai.”

Nasir ya mele baki kafin ya ce “kai kam a yi wanka a ci abinci shi kenan.”

Azeez ya kai mishi duka, Nasir din ya kauce tare da fadin “Ni fa tun da ka ce min ba ka ganin kyan Maryam na daga ma kafa wlh, yarinya black beauty komai ya ji, yanzu ma kenan ina gaba ta kara gogewa.”

“Kar ka kara ambatar min sunan yarinyar nan, raina yana baci” cewar Azeez lokaci daya kuma ya nufi toilet din da ya fasa shiga dazu.

Daga cikin toilet din ya ce “Su Mubarak basu dawo ba?”

“Yes!” Nasir ya amsa shi lokacin da yake fita daga, dakin ba ki daya.

Su hudu ne click din su, dukkansu ƴaƴan manya, Nasir ƴaron tsohon gwamna ne na farko a zamanin mulkin farar hula. Shi kuma mayen mata ne, amma ba ya shan komai, shi dai kawai ya fi son ya rika jin mace a gefensa ko wane lokaci, musamman kyakkyawa. Shi ne yake jagorantan babban companyn maihaifinsa na madara, misalin tsaftataccen nono, youghurt masu kyau, ice-cream da sauran abubuwan da suka danganci madara.

Sai Anwar wanda ya kasance yaron Admiral din sojojin sama (airforce) shi ne kuma basu cika shiri da Azeez ba, saboda shaye-shayen shi, Azeez ya tsani abu mai fitar da hayaƙi, hayaƙin mai dadin shaƙa ko akasin haka. Shi kuma Anwar zai iya yin breakfast da taba ko shisha. Amma sam bai damu da mata ba, zai iya cinye rabin shekara bai nemi mace ba. Ta nan bangaren kawai suke shan inuwa daya da Azeez. Shi kuma yana aikin sojan sama ne kamar mahaifinsa, amma da yake yana da uwa a gindin murhu kullum dutynshi a office ne, bai taba fita duty waje ba, kuma 8am ne zuwa 2pm ya tashi, shi ya sa yake samun damar sheken ayarsa, amma kam bai faye wasa da aiki ba, amma Nasir zagaye kawai yake fita ya yi ya dawo.

Sai Mubarak shi kuma yaron wani hamshakin dankasuwar gwala-gwalai ne, kuma dan canji, ya mallaki manyan shaguna a babbar kasuwar jimeta, shi ya sa Mubarak kasuwanci kawai ya sani, akwai babbar supermarket din da Baban ya bude, sannan ya ba shi manager, wannan ya kara budewa Mubarak hanyar sharholiya, shi na shi halin kawai shi ne ya nunawa duniya shi fa dan masu kudi, duk a wurin biki ko birthdayn da ka ji an yi babbar kyautar da ta girgiza taro to Mubarak ne, shi ya sa duk macen da ya ce yana so kakarta ta yanke saƙa. Kuma shi ne abokin gasar Azeez, Mubark ya fi son a fara ganin abu a wajen shi, haka ma Azeez. Dukkansu irin karin maganar nan ta Hausawa Ni ko Ke kyawawa sun hada hanya. Mubarak bai cika mayar da hankali a kan neman mata ko shaye-shaye ba, ya fi mayar da hankali wajen neman daukaka da kuma cinye ko wace irin gasa. Wannan neman sunan shi ke hana shi samun lokacin mace ko shan wani abu.

Azeez shi ne kawai bai yin aiki a cikinsu, karatun ma bai gama ba sai shiririta, amma kuma dukkansu basu nuna mishi komai, har lokacin yana rike da kambun sai dai su gani a wajensa su kwaikwaya, Mubarak har mamakin inda Azeez ke sanin shigowar sabon abu yake yi, Sai dai kawai su gan shi a wajensa, kafin daga bisani ya fara trending.

Abin da basu sani ba, Azeez mayen internet ne, ya san lungu da sako na cikinta, a nan yake samun abun ya yi, da alama ma har sun san shi, wani lokaci su kan fara yi mishi tallar abu tun bai fito ba, shi kuma zai yi booking, shi ya sa yana daya daga cikin mutanen da suke fara siyen abun ya yi. Wani lokaci sai abu ya yi shekera a hannunsa sannan a fara ganin shi a kasuwa. Wannan ya sa Mubarak ke jin haushin Azeez sosai. Ya fi son ace shi ne ko wane lokaci yake zuwa da sabon abu a click din nasu. Sannan Azeez na daya daga cikin wanda ya fi farin jinin mata a click din nasu, wannan kuma baiwar Nasir take ba haushi, saboda shi ne mayen mata, duk da wani lokaci ta kan dan taba Mubarak da yake son ganin ya fi kowa ta ko wane bangare.

Wani abu da basu sani dangane da Azeez ba, shi ne batun satarshi, saboda bai taba daukar musu ko murfin biro ba, shi satarshi kawai a gida ne, ba ruwan shi da abu ko na bako ne to zai dauka. Amma a waje idan zai kwana cikin kudi baya dauka.

Dukkansu suna da permanent daki a babban hotel din cikin garin, da ace za a kara bude wani hotel din wanda ya fi wannan tsada zasu kara zuwa su kama daki, ko wane hotel su kan kama daki hudu ne a jere.

Amma hakan bai hana su kwana a gida ranar da suka yi marmarin hakan, sannan su kan ziyarci juna, saboda iyayensu sun san da zaman abotar tasu. Wannan kenan.

Aunty Adama

Zaune take a kayataccen falonta da ya sha kudi, mace mai matsakaicin tsawo da matsakaici yar ƙiba, fatar nan ta sha maya-maya da dole suka canjata zuwa fara.

Kanenta Bandi ne a kasa yana cin jalouf din shinkafa da wake da kifi.

Bayan ya taune abincin bakinsa ne ya ce “Aunty Adama please, don Allah ki shige min gaba, da gaske ina son yarinyar nan, kin ga yau da na ganta da kayan nursing school din nan, wlh na ji kamar in sace ta zuwa gidana.”

Tabe baki ta yi sannan ta ce “Please count me out a wannan maganar, basu shiga harkata ni ma ba na shiga tasu.”

“Shi ya sa na ce ki yi wa Hammah magana, ita Aisha ina ruwanta, me ta hada da yarinyar?”

Shiru Aunty Adama ta yi, kamar ba za ta yi magana ba, Sai kuma ta ce “Ta reni yarinyar tsawon shekaru biyar ka ce me ye na ta a ciki.”

Bandi ya aje spoon hannunsa sannan ya ce “To sai me don ta rena ta? Ba ita ce ke da hakkin aurar da ita ba ai.”

“Bandi!” Aunty ta kira sunan shi

“Da gaske fa” cewar Bandin da kwarin gwiwarsa.

“Go and meet Hammah by yourself. Lokacin da ya ce zai dakko yarinyar nan, ce mishi na yi ba dakina ba, saboda ba ma shiri da uwarta kafin ta rasu, yanzu kuma sai in je mishi da batun kanena na son auranta. No! Just go and meet him.”

“I will. Amma dai ki tabbatar kina bayana, ba na son wani ya zo ya min kafar baya.”

Aunty ba ta ce komai ba, har zuwa lokacin da Bandin ya mike hade da, ficewa daga falon.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Da Magana 2Da Magana 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×