Ya zubawa kofar da suka bari a bude ido, kamar mai jiran shigowar wani, karar wayar hotel din da ke cikin dakinshi ya sanya shi zira hannu ya dauka
"Kofar dakinka a bude, ka sani ko ba ka sani ba?" aka fada mishi bayan ya daga
"Na sani." ya amsa hade da ake kan wayar.
Ba jimawa kuma ya ji muryar wani daga wajen kofa yana fadin "kana bukatar taimako ne?"
"Ja Min kofar" ya amsa a hankali hade da kwantawa rigingine kan gadon.
Wayarsa ya janyo hade da da lekawa media, ba karamin mamaki ya yi ba ganin yadda. . .