Skip to content
Part 35 of 42 in the Series Da Magana by Matar J

Ya zubawa kofar da suka bari a bude ido, kamar mai jiran shigowar wani, karar wayar hotel din da ke cikin dakinshi ya sanya shi zira hannu ya dauka

“Kofar dakinka a bude, ka sani ko ba ka sani ba?” aka fada mishi bayan ya daga

“Na sani.” ya amsa hade da ake kan wayar.

Ba jimawa kuma ya ji muryar wani daga wajen kofa yana fadin “kana bukatar taimako ne?”

“Ja Min kofar” ya amsa a hankali hade da kwantawa rigingine kan gadon.

Wayarsa ya janyo hade da da lekawa media, ba karamin mamaki ya yi ba ganin yadda mediar ta dauka a kan maganar auranshi, bai san mutane na bibiyar lamarinshi haka ba sai a ranar.

Yadda mutane ke comment a kan son ganin matar da ya aura ba karamin mamaki ya ba shi ba. Ko me ye damuwarsu da matar shi oho

Comment na biyu da ya kara ba shi mamaki shi ne na masu fadin dole wacce ya aura kyakkyawa ce kuma yar masu kudi yar boko.

“Me ya sa suke wannan tunanin?”

Dole ne celebrity ya auri mai kyau kuma mai kudi.

Shi ma ai mutum ne kamar kowa, yanzu da ace sun ga Maryam Allah kadai ya san mutanen da zasu kushe ta. Saboda dai ya san ba mai kyan ba ce.

Akwai bukatar ya kara boye ta.

“To idan kuma kwatsam ta bayyana fa?”

Ya tambayi kansa, “Akwai matsala kenan” ya ba kansa amsa

Lokaci daya kuma ya mike hade da mayar da rigar shi.

Akwai bukatar ya je ya kara ganinta, ya tantance ya take ma, ya kyawunta, wane kalar kyau ne na yan Ethiopia da kullum Nasir ke kwatanta da shi?

Zai yi comparing din ta da sauran ƴanmatanshi ya ga ta ina suka bambanta.

Saboda da zarar sun fita kyau to tabbas za su yi mishi dariya, dama duk ya ga sakonninsu a dm bai dai bude ba ne, kuma ba ya jin ma zai bude.

Daga haka ya ja dakin lokaci daya kuma yana duba agogon hannunshi da ya nuna karfe biyar na yamma saura.

Ina tsaka da sanya turaren wuta na ji ana kwankwasa kofa, na nufi kofar hannuna rike da kaskon turaren saboda na dauka ko su Aunty Nafee ne

Ganinshi tsaye a kofar ba karamin kayar min da gaba ya yi ba

Na zuba mishi manyan idanuna cike da tsoro, kamar yadda shi ma yake kare min kallo sama da ƙasa.

Na yi saurin kai hannuna na rufe kaskon wutar, a tunanina hayaƙin ne ya hana shi wucewa, kuma shi ne dalilin da ya sa yake ta kallo na.

Da sauri na juya kitchen, a kokarina na adana hayaƙin

Wannan ya ba shi damar karewa bayana kallo har na shige kitchen din, kafin ya juya lokaci daya kuma yana tattara sakamakon da ya samun.

Ni kam kofar kitchen din na rufo bayan na fito, na haura saman Aunty ina tambayarta ko Ya Azeez ya shigo

“Bai shigo ba, zuwa ya yi?”

“Eh time din ina saka turaren wuta” na amsata

“Ya koma, ke ma kin san ba zai zauna ba. Ke ma ki matsa ki yi wanka ki tafi gida, tun da mijinki ya dawo”

Na langabe kai ba tare da na ce komai ba

Ita ma kuma ba ta kara magana ba, ta dai hade fuska alamun babu wasa

Na juya domin aiwatar da abin da ta ce

AZEEZ

Tuki yake a hankali yayin da zuciyarsa ke hasko masa Maryam cikin bakin siket tummy da farar shirt Wacce ta yi mata kamar stoking.

A tsawo kam ba ta da makusa, tsawonta bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba.

Duk da kanta a rufe yake da hula ya san tana da suma mai tsawo da kuma yawa, yanayin fatarsu iri daya ce, chocolate idanuntasun ɗan fi na shi girma, amma yanayin hancinsu iri daya, ku san komai na fuskarta yana yanayi da na shi.

Saboda yanayin ciwon da ta yi yanzu kam komai na halittarta bai fito ba, saboda har zuwa lokacin ba ta mayar da jikinta ba.

Ya ja numfashi a hankali, har ga Allah yana son ya ga a komai ya fi abokansa musamman Mubarak da suke zama kamar na kishiyoyi, baya san Mubarak ya yi mishi dariya a ko wane bangare.

Da wannan tunanin ya shiga farfajiyar hotel din.

Bayan ya Parker motar ya fito ya zauna a kan bodyn ta baya. Yana bin posts din da ake yi a kan maganar auran shi.

Bai jima da zama ba motar Nasir ta shigo, kallo daya ya yi mata tare da dauke kanshi zuwa gefe, har zuwa lokacin da Nasir ya karaso inda yake ya zauna kusa da shi yana fadin “Ango ka sha kamshi, ka ga yadda media ta rude a kan batun auranka kuwa, crush naka sai damunmu suke yi, wlh ka shammaci mutane ciki har damu, ban taba tunanin kai ne za ka fara aure a cikinmu ba” Nasir ya karasa maganar lokaci daya kuma yana janyo wayarshi da ke cikin aljihu.

“Kana da matsala” Azeez ya fada a hankali kamar baya son maganar

“Wai wace mai sa’ar ce wannan, kowa sai tambaya yake?”

“Ba dai za ka kyale ni ba ko Nasir.”

Cikin dariya Nasir ya ce “Kodai auran dole aka yi ma ne wai, duk ba ka farin ciki”

“Na dole ne.” Azeez ya amsa kai tsaye.

“To me ye na jin haushi kai da ba ka san so ba dama.”

Harara kawai ya aika mishi ba tare da ya ce komai ba.

Nasir ya ɗora da “Wani auran dolen ma fa taimakon mutum kawai aka yi. Sannan akwai matan da idan aka yi ma auran dole dasu taimakonka aka yi, ka ga kamar Maryam. Wlh da gudu zan yi biyayya.”

Azeez ya dan yi shiru yana nazarin maganarshi kafin ya ce “Me ya sa za ka yi biyayya?”

Nasir ya gyara zama tare da fadin “Kai a yadda nake din nan haka Allah ya ba ni Maryam a matsayin mata ai ni ya sallame ni”

Karon farko da Azeez ya yi dariya mai sauti, fararan hakoransa suka bayyana.

Daidai lokacin kuma Anwar ya shigo, Nasir kuma ya ci gaba da cewa “Allah ba wasa nake yi ba, yarinya kalar ƴan Ethiopia, yo wannan ta samu hutu habawa…”ya kai karshen maganar hade da mikawa Azeez wayarshi yana fadin” Kalle ta fa don Allah. “

Azeez ya karbi wayar hade da zubawa hoton Maryam ido, wanda kallo daya ya gane Nasir ya dauki hoton ne ranar da suka yi Adamawa connect.

Ya danna delete, hade da shiga cikin wayar yana dubawa ko akwai saura, Sai dai bai samu ba, hankalin Nasir baya wurin, yana kan Anwar da yake tsokanarsu da “Kowa ya daka rawarku ya rasa turmin daka tashi, har kun shirya?”

“Ba dole ba, upcoming ango ne fa”

Anwar ya gyara tsayuwqrshi yana fadin “Ka ga yadda zancen auran nan ke yamutsa hazo a media kuwa? Kai wasu mutanen akwai dorawa kai wahala”

“Ni basu damuna kamar masu kirana, Salma ta kirani ya fi dari biyu har da kukanta. Madina Kuma murna ta taya mu, amma ta ciki na ciki” cewar Nasir a lokacin da yake karbar wayarsa a hannun Azeez ya tura aljihu.

“Yaushe za mu je wurin amarya ne ango?”Anwar ya tambaya

” Ba ta nan ai, idan ta dawo zan fada muku dole. And I’m very sorry, wlh ba da sanina aka daura aurannan ba yadda kuka ji haka ni ma na ji. “
Cewar Azeez kamar ba ya so.

” Allah Ya tabbatar da alkairi “Anwar ya fada

Nasir ya ce” Amin “

Sai kuma suka kwashe da dariya suna kallon Azeez tare da fadin” Ango!Ango!! Ango!!! “

Ya ja dogon tsoki hade da mikewa ya nufi hanyar dakinshi

*****

MARYAM

Duk fadan Aunty sai da na yi sallahr magriba sannan na dauki handbag dita da niyyar tafiya

Fuskata a hade, haka ma ta Auntyn take a hade, saboda so ta yi in yi magriba a gida.

Kudin Keken da ta ajiye min na dauka hade da dukawa na sumbaci Babyn da ke hannunta

“Na tafi”

“Allah Ya tsare” ta amsa min fuska a daure

Kamar in leka su Aunty Karima sai dai na san zasu matsa min da tsokana ne, shi ya sa asirna rufe na fita hade da tare mai keke

Yana ajiye ni a kofar gate kiran Aunty na shigowa

“Kin isa?” ta tambaya bayan na daga

“Eh.” na amsa

Ba ta ce komai ba ta kashe wayar.

Ni kuma na shige gidan bayan na bude gate.

Na yi tsaye a tsakiyar falon ba tare da sanin abun da zan yi ba.

Sai kuma na rika bin ko wane lungu da sakon na gidan ina dubawa, wani wurin kuma in kakkabe kurar da ya yi.

Kiran sallahr isha’i ya dakatar da ni, na yi alwala hade da yin sallah

Bayan na idar na hada tea na debo cincin cikin bowl na nufi tsakiyar gadona na zauna na rika daukar cincin din ina hadawa da tea,lokaci daya kuma ina leka lungunan social media da ake ta tayar da kura a kan maganar auranmu, wani abun sosai yake ban dariya, wani mamaki wani kuma ya ban haushi.

Wani kuma ya kan sanya ni in ji kamar ban kai matsayin zama matar Ya Azeez ba, musamman yadda na ga mata wayayyu kyawawa suna son shi.

Abin da kuma ke sanyaya min rai shi ne yadda ake yawan fadin alkairi Ya Azeez fiye da sharrinsa. Abin da aka fi fada a kanshi mai muni shi ne girman kai.

Wasu kuma sai suna kare shi, wai girmama kai ne, ba girman kai ba.

Kiran Aunty ya dakatar da ni, na yi saurin dagawa

“Azeez ya dawo gidan nan?”

Na yi saurin sauke wayar hade da duba lokaci 8:32pm na ce “Bai shigo ba.”

“OK” ta amsa hade da yanke kiran.

Ni kuma na dasa daga inda na tsaya.

*****

AZEEZ

Zaune yake a tsakiyar gadonshi yayin da sanyin Ac ya ratsa dakin, hankalin kaf yana a kan ball din da ake haskawa a tv.

Wayar shi da ke gefe ta shiga vibration, da sauri ya daga saboda ganin sunan Aunty “Ka koma Abujan ne?” ta fara tambaya

“A’a.” ya amsa lokacin da yake rage karar tv din

“To kana ina, ko kana gidanku na gado?”

Ya ɓata rai kamar yana kusa da ita.

“Ba ka ji ba?” ta kuma fada jin bai amsata ba

“To ai naga gidan duk mutane”

“Ai dama ban ce ka zo nan ba, amma ka tashi ka wuce gidanka, saboda tun magriba na ce Maryam ta koma, kuma ba za ka bar min yarinya ta kwana a wannan gidan ita kadai ba”

Baki ya bude sosai ba tare da ya ce komai ba

“Ko ba ka ji ba?”

“Aunty to a dawo nan mana.”

“Je ka dawo min da ita, da auranta ba za ta zauna a nan ba”

Ya yi shiru cike da takaici

“Ka tashi ka wuce gida, idan ba haka ba, zan zo har hotel din in same ka, ka san dai zan iya.”

“Zan je” Bai jira cewarta ba ya yanke kiran cike da jin haushinta

“Mtswww! (ya ja tsoki) tun da yarinyar nan ta zo gidan nan take takura min.”
Ya fada a bayyane cikin takaici, duk sai ya ji kallon ball din ma ba dadi, zaune kurum yake amma bai san me ake yi ba, har aka gama ma bai lura ba sai daga baya.

Rai ba dadi ya dauki key din motarshi laptop da kuma wayoyinshi ya fice daga dakin bayan ya rufe.

Karfe 9:15pm na yi shirin bacci kiran Aunty ya kuma yi shigowa

“Ya dawo?” Abin da ta fada kenan.

Na girgiza kai kamar ina gabanta tare da fadin “A’a, bai dawo ba, kin kira shi a waya ne?”

Ba ta amsa min tambayar ba ta yanke kiran.

Tana yanke kiran ta kuma kiran Ya Azeez

“Aunty ga ni a kofar gida, fa, ina shirin shiga.” ya amsata cike a kosawa tun kafin ta ce wani abu.

“Saura ka rika hantararta, kuma ranka ya baci, tun da ita ma ba sonka take ba, dole aka yi mata” tana gama fadin hakan ta yanke kiran.

Bin wayar ya yi da kallo maganar Aunty na mishi yawo a kwakwalwa, ya jima a haka kafin ya shiga da motar sosai cikin gidan ya rufe gate.

Ni dama ban yi baccin ba, tun da na ji karar motar shi na zauna dirshan ina jiran shigowarshi.

Ko ba komai dai na san ba ni kadai zan kwana a gidan ba.

Ina jin yadda ya shigar da key ya bude kofar falon.

Tsaye ya yi yana kallon falon da ya sha kayan gyara kamar na wata yar shugaban kasa.

Gaskiya ne mace ita ce gida, a da kafin a hada falon bai yi kyan haka ba.

Har sai ya ji sha’awar kawo abokanshi. Musamman yadda dakin ke tashi kamshi mai dadi.

Daga nan dakinshi ya wuce,saboda tun kafin ya tafi Abuja Hammah ya nuna mishi komai na gidan, Sai dai lokacin ba a zuba komai na Kwalliya ba. shi ma an zuba mishi duk wasu kaya da dakin namiji dan gayu kuma dangata yake nema.

Shi da kansa ya san wannan ɗakin ya fi na otel din da ya baro ba ma hadi.

Sai ya ji zuciyarsa ta ɗan rage zafin da take yi, a duniyarshi yana son jin dadi.

Kayansa ya cire ya fada toilet ya yi wanka, ya yi shafa’i da wutri ya bi lafiyar gadonshi.

<< Da Magana 34Da Magana 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×