Skip to content
Part 36 of 42 in the Series Da Magana by Matar J

Tun ina jiran jin motsinshi har bacci ya dauke ni, sosai na yi bacci hankali kwance.

Kiran sallahr asuba ne ya tashe ni.

Bayan na idar da azkhar na wuce kitchen.

Na shiga duba kayan abinci, babu wani abu na break fast Sai indomie da kwai

Zuciyata ta ba ni kawai in soya indomie din da kwai.

A nutse na dora ruwan zafi, yana tafasa na jefa indomie, bayan ta dahu na rika tsame ta ina sanya ta cikin danyen kwan da na fasa, wanda ya sha citta, tafarnuwa, tattasai da kuma albasa.

Cikin kankanin lokaci na gama hada komai, highland green tea na tafasa na juye a flask.

Wanda tsaraba ne daga Gembu, a Ngourage ake yin sa. Ganyen shayi ne mai inganci wanda yake dauke da magunguna masu tarin yawa.

Na kwashe kayan abincin na kai kan dining, kafin na gyare kitchen din tsaf, falo ma na kara gyare shi na kade kura, sannan na fesa freshener masu dadi.

Daga haka na wuce bedroom dina na yi wanka, na shirya cikin riga da siket na atamfa sosai dinkin ya yi min kyau.

Normal dauri na yi, na dawo falon don yin breakfast.

Ina cin abincin ina kuma taɓa wayata da haka na gama, ko da na gama din ma ban tashi ba, zamana na yi a wurin ina ci gaba da taɓe-taɓen wayata har 11am

Daidai lokacin ne kuma Ya Azeez ya fito sanye da riga shirt light brown mai dogon hannu, duk da ban taɓa ta ba na san za ta yi taushi

Wando kuma onion color ne haka ma takalmi, sosai ya yi kyau musamman yadda rigar ta fitar da kirar jikinsa.

A sace na yi masa wannan kallon, ba lallai ya san na kalle shi ba.

Kai tsaye dining din ya nufo, ya shiga bude kwanonin da ke kai.

“Me ye wannan?” ya yi tambayar a lokacin da ya bude warmer mai dauke da indomien da na soya

“Indomie ce.” na ba shi amsa da spoon ya gutsiri kaɗan hade da kai wa baki, bayan ya taune sai ya dauki wani plate din ya zuba hade da tsiyayar tea

Ya shiga yin break din sa a nutse lokaci zuwa lokaci kuma yana satar kallo na

Hakan ya sa na yi kamar ban san da zaman shi a wurin ba.

Wani lokacin maza kamar zuma suke sai da wuta, sai kuma kana ɗan share su.

Bayan ya gama ne tissue ya janyo hade da goge bakinsa, daga haka ya nufi kofar fita.

Har ya kai bakin kofar kuma na ji ya ce “Ke zo nan.”

Rufe bakinsa ya yi daidai da tashina zuwa inda yake.

“Ke ni za ki kalla ki ce ba kya sona.”

Jin maganar na yi kamar saukar aradu, ni dai ban yi ko makamanciyar wannan maganar da kowa ba

“Ko Aunty za ta yi miki karya ne?”

Maganarshi ta tabbatar min da Aunty ce ta fada, kuma na san trap ne.

Ban ce komai ba, amma na hade fuskata hade da zumbura baki, irin dai kamar da gaske na fada din

Yadda ya matso ne ya sanya ni saurin ja da baya, kar in ji ya kwaɗe ni, saboda shegen saurin hannu gare shi.

“Ke har kin isa ki ce ba kya so na? Ban taɓa samun wacce ta raina ni ba irin ki. Ba kya sona ko?”

Ban amsa ba sai kara tura bakina da na yi lokaci daya kuma Ina taunar karamin yatsana

“Dago kanki ki kalle ni.” ya daka min tsawa.

Kan na dago a hankali na kalle shi, lokaci daya kuma na kawar da kaina gefe

“Ki kalle ni na ce” ya kuma daka min tsawa

Yanzu kam kafe shi na yi da ido, a tsorace.

“Oya fada min, ko ki nuna abin da ya sa ba kya sona”

Kafin in amsa wayarshi ta shiga vibration alamun kira na shigowa.

Ina ganin hankalinshi ya tafi a a kan kiran, na kwasa da gudu zuwa daki hade da dannawa kofata key.

Sai da na tabbatar ya bar gidan sannan na fito.

*****

AZEEZ

Bayan ya yi parking a faefajiyar gidan wurin monkey ya nufa, ya ba shi abinci, kafin ya wuce wurin Aunty

Time da ya shiga yaro take shiryawa dalilin da ya sa ya nemi wuri yana kallon ta har ta gama

Bayan ta gama ne ta mika mishi yaron

“Ban iya dauka ba.” ya amsa ta cikin murmushi

“Ka koya kafin naku ya zo”

“Allah ji nake kamar zai, ɓurme”

Suka yi gajeruwar dariya a tare kafin ta ce “Me ya faru?”

“Abuja zan koma yau.”

“Ba za ka jira a yi suna ba?”

“Aunty ni din kamar mace, wane irin suna kuma zan jira a yi.”

“To!” Cewar Aunty hade da rike baki

“Amma me ya sa za ka tafi Abujar, ba ka ce sai nan da 1weeek za ku yi jarabawar ba”

“Ni ina son tafiya ne kawai”

“Saboda Maryam ko, ta yi ma wani abu ne?”

Ya ɓata rai sosai kafin ya ce “Saboda Allah ni yarinyar nan za ta ce ba ta so Aunty. Ki kalle ni fa, yanmata fa har fada suke a kaina, amma saboda raini ita ta ce ba ta sona. Ni ban ce ba na sonta ba sai ita. Kalle ta fa da wani tsawo kamar raƙuma”

“Kowa ya yi tsawo Azeez ai ya ci rabin kyau” Aunty ta cafe.


Can kasan ranta kuma dariya take yi da alama maganar ta zafe shi sosai, har ya kasa hadiye fushinshi.

“To yanzu da za ka tafi ka duba gidan babu abin da ita Maryam din ke bukata ko?”

“Kamar ya?” ya yi saurin tambaya

Gyara zama Aunty ta yi kafin ta ce “Haka ake aure Azeez, yanzu fa hidima ce ta hau kanka, duk wani abu da gida yake bukata kai za ka lura sannan kuma ka kawo”

“In kawo kuma, ina na ga kudin kawowar?”

Wannan karon kam Aunty ta kasa danne dariyarta, cikin dariyar ta ce “Nemo kudin za ka yi”

“Ina zan nemo su, ni fa ba za a tayar min da hankali ba gaskiya, haka kawai ban ce a yi min aure ba kuka tashi kuka yi min.”

“Kenan laifi mu ka yi ma?” Aunty ta tambaya da alamun mamaki

“Gaskiya! Gaskiya ni ba a kyauta min ba, ga shi yarinyar ma wai ba ta sona. Haba Aunty kin San yadda kalmar nan ke bata min rai.” ya yi maganar kamar zai yi kuka

“Azeez ba dadi ashe, kai ma fa ka ce ba ka sonta”

“Ni auran ne na ce ban so.”

Aunty ta saki dariya tana fadin “Ni Indo Aisha”

“Ku shirya ciyar da ita, ni gaskiya ba za a dora min nauyi ba. Ba zan yi ta wani sayen kayan abinci ba. Idan ta gaji da zama can ta dawo nan”

“A haka za a yi auran”

Bai amsa ba, Sai dai ya hade fuska.

“Allah Ya kyauta!” cewar Aunty

Hammah da ya shigo ya ce “Amin. Me ya faru ke da yaron na ki, na ga fuskarshi a hade?” ya karasa maganar yana kallon Azeez da ke zaune a kan bedside durowa.

“Wai Abuja zai koma yau.”

“Ba zai jira a yi sunan ba?” cewar Hammah da yake janyo stool din mirror ya zauna.

Duk suka yi shiru daga Aunty har Azeez din

Hammahn ya dora “Ka jira bayan an yi suna sai ka tafi, akwai maganar da nake son yi da ku kai ƴan’uwanka.”

Dukkansu dai babu wanda ya ce komai

“Me kika yi wa yaron nan ne Aisha?” cewar Hammah idanunsa a kan Aunty.

Dariya ta kwace mata kafin ta ce “Ba ga shi a zaune ba Hammah, ka tambaye shi”

“Ke za ki amsa min, wannan ɓacin ran ba a kan tafiya Abuja ba ne kawai. Me ya yi wa Maryam din?”

“Ko ya yi mata ma ban sani ba, kawai dai ya ce zai tafi, na ce to ya duba gidan ita Maryam ba ta bukatar komai ko, idan akwai abin da take bukata ya kamata ya siya kafin ya tafi”

Ya dauke idonsa da kan Aunty zuwa kan Azeez kafin ya ce “Me ye babu a gidan naku?”

“Ni ban sani ba” ya amsa rai bace

“Ya kamata ka sani Abdul’azeez, kai ma yanzu ka zama babban mutum, da zarar ka kasa sauke wani nauyi da ya hau kanka, mace za ta fara raina ka. Ka san babu abin ke kawo raini kusa tsakanin mata da miji kamar namiji ya kasa sauke nauyin shi a kanta.”

“Tun yaushe ta raina ni Hammah. Cewa take fa ba ta sona” Ya kuma fada a rai a matukar bace

Hammah ya shiga girgiza kai tare da fadin “Maryam ba za ta ce ba ta sonka ba Azeez, Sai dai idan ko wani abu ka yi mata mara dadi. Idan ma hakan ne ai akwai hanyoyin da za ka sanyata ta soka din, ita zuciya tana son mai kyautata mata ai”

“Yanzu ni fisabilillahi a ina zan rika samo kudin sayen kayan abinci da sauran sirgullanta Hammah. Ni fa ban shiryawa aure yanzu ba.”

Yadda ya yi maganar ka rantse da Allah kuka zai yi.

Aunty ta cafe “To ba ga irin ta ba, da ace ka mayar da hankalinka a karatu da tuni ba kana da aikinka a hannu ba, da yanzu wannan auran ba zai dame ka ba, koda ace mace biyu aka aura ma lokaci daya. Ka tsaya shirmen banza da na wofi.”

“Shi kenan ya isa don Allah. Gaba muke son ci Aisha ba baya ba. Kana ji na ko Azeez” cewar Hammah idanunsa a kan Azeez din

Bai yi magana ba amma ya dago yana kallon Hammahn

“Ina so ka sani daga yanzu a nan da muke wannan maganar ka mayar da hankalinka wajen gina goben ka, ka ga dai nauyi ya kara hawa kanka nan gaba, kadan kai ma za ka fara aje yara. Ba za ka so yaranka su yi rayuwa kamar ta almajirai ba. Har yanzu lokaci bai kure maka ba, za ka iya zama duk abin da kake son zama matukar ka jajirce. Maryam ba ta da matsala ta san waye kai, ita ce kawai za ka zauna da ita cikin fahimtar juna. Ka daina kunci ka ji”

Kai ya daga alamar to.

Ko ba komai zuciyarsa ta rage zafin da take yi mishi a baya.

Amma yau kam tashi ya yi duniyarsa duk babu dadi, ji yake kamar ya yi dukan duk wanda ya hadu da shi a hanya.

“Ka je gidan ka tambayi me takw bukata, sai ta rubuto ka zo mu shiga kasuwar tare in taya ka cefanen. Yaro ya zama babban mutum”

Hammah ya fada cike da tsokana

Ya dan mumusa kadan hade da shafa kansa.

“Ta shi ka je maza. Don Allah Abdul’aziz ka shirya mayar da gidanka wurin kwanciyar hankali ba filin tashin hankali, bakin ciki da damuwa ba.”

Komai dai ba ce ba, ya nufi kofar fita.

Bayan fitarsa ne Hammah ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon Aunty sannan ya ce” Kamar ba mu yi wa yaron nan adalci ba Aisha, kalli yadda ya zama sam babu walwala a tare da shi. Gaskiya na fara jin rashin dadi.”

“Ba a yi mishi adalci ba, ko ba a yi wa yarinya adalci ba Hammah? Ai tashin hankali ya kare a kan macen da ta auri miji mara sana’a wanda ba shi da wata madafa. Ni kam Maryam nake tausayi ba Azeez ba wlh. “

Hammah ya dan murmusa kadan kafin ya ce” Ke da Azeez kam Aisha kamar ba yaronki ba”

“To ai gaskiya na fada.”

“Na ji. Me kuke bukata na hidimar suna?” ya canja akalar hirar tasu

“Ba wani abu sosai ba, ba taro zan yi ba.”

“Amma kin san ƴan Minchika duk sai sun zo, yadda kika ji ma ba ki haihun nan ba. Saboda haka ki zauna da su Karima ku lissafa abin da kuke bukata.” ya kai karshen maganar lokaci daya kuma yana nufar kofar.

*****

MARYAM

Kamar daga sama na ji horn din shigowar Ya Azeez, a guje na bar falo zuwa bedroom na danna key.

Kafin na dawo window hade da daga labule kadan yadda zan iya ganin shigowar shi.

Bai jima ba kuwa ya shigo kai tsaye ya wuce kitchen, bai jima a can din ba ma ya fito tare yo hanyar bedroom dina

Na ƙame ƙam gabana na faduwa, lokacin da ya buga kofar sai na ji kamar zuciyata ya buga.

Ya kwankwasa kofar a karo na biyu, sannan ne kuma na tunkari kofar gabana yana kara faduwa, na murza key din sannu a hankali na dan raɓe gefe bayan na bude kofar.

“Je ki kitchen da storeki rubuto min duk abin da kike bukata wanda ba ki da shi.” kai karshen maganar ta shi ta yi daidai da juyawar zuwa na shi dakin

“idan kin rubuto ki kawo min dakina.” ya kara fada daidai lokacin da ya isa bakin kofar.

Bayan na shiga kitchen na shiga bincikar abun da babu, doya, Irish, nama da kuma ɗanyun kayan miya ne babu.

Na rubuta kamar yadda ya ce, kafin na tafi kai mishi

Sai da ya amsa sallamata sannan na shiga

Ya rika bin rubutun nawa da kallo kafin ya ce “Shi kenan?”

Na jinjina kai alamar eh

“Je ki” ya fada daidai yana mikewa tsaye hade da cuss takardar cikin aljihu.

Ku san a tare muka fito, ya nufi kofar fita ni kuma na koma bedroom din.

<< Da Magana 35Da Magana 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×