Skip to content
Part 38 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tun daga wajen gida na fahimci cikin gidan a cike yake.

Saboda motaci ne a kalla sun kai guda bakwai jere a kofar gidan.

Dalilin da ya sa bamu samu damar shiga da tamu motar ba, mu ka samu wurin parking a waje muka karasa a kafa.

Farfajiyar gidan cike take da yara gami da manya, wasu yaran kuma suna wurin monkey suna tsokanarshi.

Kai tsaye wurin monkey muka tunkara, Ina jin yadda na ji rashin dadi a zuciyata gami da tsokanar da yaran ke mishi haka Ya Azeez din ma ya ji.

Tare muka shiga cikin kejin, yayin da monkey ke ta tsallen murnar ganinmu

“Ina jin zan je da shi wancan gidan” ya fada min da alamun rashin jin dadi a fuskarshi.

Kai na gyada alamun gamsuwa

Ya shiga kwance shi, ni kuma ina tsaye ina kallon su har ya gama kwance shin.

Yaran da ke wurin suka kwasa da gudu ganin Ya Azeez ya yo hanyar fita da monkey ni kuma Ina bin shi a baya.

Kamar an fisge monkey daga hannun shi haka ya kwace fit, ya bi wani yaro da gudu cikin mutane.

Wannan ya sa mata da yara ihu suna gudu.

Ni kuma na aje kayan da ke hannuna na bi bayan shi a guje hade kiran sunan shi.

Amma bai saurare ni ba, sai da ya yi tsalle a kan yaron nan ya kuma gantsara mishi cizo a kai, sannan ya yo kaina a guje.

Ganin yadda fuskata take a hade ina mishi masifa sai ya wuce wurin Ya Azeez a guje, suka fice daga gidan.

Daga baya ne nake jin wai yaron ya kwada mishi dutse a kai ne.

Sosai abun ya ban mamaki, dabbobi ma da irin nasu hankalin, wato ya rama kenan.

Lokacin da na shiga falon Aunty a cike yake da jama’a haka ma cikin dakin, ita kam ta ci kwalliya kamar ba ita ce ta haifi Ya Azeez ba, ta sha jan lalle ga kitso an watsa mata, ga wani bakin lace mai golden ta sha, Haba sai fita fes abun ta, yaro kam ya sha kaya ƴan ubansu yana cikin lallausan bargo.

Key ta miko min ta ce in bude dakin Ya Azeez in jira ta.

Haka na sakko da kayan hannuna zuwa dakin Ya Azeez.

Dakin kaya ne jibge a ciki, daga drinks da abinci a cikin take away, ga zannuwa pampers da kayan jarirai jibge a kan gado, na san kuma duk gifts din da aka tara mata ne

Na zauna gefe hade da daddaga kayan ina yaba kyawunsu

Daidai lokacin ta shigo hannunta sabe da Abdallah

Zamana na gyara lokacin da take dora min shi a kan cinya, ita kuma ta zauna a kan wata katuwar kula tare da fadin “Na gaji, kaina ma ciwo yake”

Na murmusa kadan ina kallon Abdallah kafin na ce “Hayaniya ce, ba ki saba ba”

Ledar da ke kusa da kafafuna ta janyo ta shiga fitar da kayan da ke ciki

“Ma Sha Allah! Kayan sun yi kyau sosai, daga waye.”

“Ya Azeez ne ya ce mu je SAN HUSSAIN in zaɓowa Abdallah”

Murmushi ta yi wanda ke nuna tsantsar farin cikinta kafin ta ce “Azeez dai ana ta kara hankali. Na gode sosai Allah Ya kara shirya shi.”

“Amin.”Na amsa kafin na ce” Aunty a ina yake samun kudin ne? “

Zamanta ta gyara sosai kafin ta ce” Babanshi ke ba shi, Sai kuma ana basu allowance duk sati a wurin training din da suka yi”

Na gyada kai alamun gamsuwa ba tare da na ce komai ba.

Ita ce ta kuma cewa “Maryam aiki ya same ki fa, duk da ba na jin ki a kan Azeez, kin iya kula da shi, kin kuma iya zama da shi, amma sai kin kara dagewa, yanzu mijinki ne, kuma uban yaranki, dole ki yi kokari kina dora shi a kan daidai, ki kuma kara dagewa, Juriya da kuma hakuri. Sai addu’a. “

Na daga kai alamar na fahimta

“Ga abinci nan idan za ki ci, ni zan koma wurin jama’a “ta yi maganar hade da daukar Abdallah da ke kan cinyata

Ni kuma na dauki plate na zuba abinci hade da daukar minerals guda daya.

Bayan cikina ya dauka na shiga cikin ƴan’uwa, sunan kam ya yi dadi, ba dai wani kide-kide aka yi ba, amma an yi nishadi an hadu da ƴan’uwa

Zuwa magriba gidan ya koma shiru sai mu da ƴan Minchika

Har 10pm bai zo daukata ba, kuma an kira shi bai daga wayar ba

Ni kam na yi kwanciyata cikin ƴan’uwa

Washegari da sassafe ƴan Minchika suka wuce, ya rage sai ni da su Aunty Karima wadanda su ma suke shirin tafiya gobe

Misalin karfe goma na safe Hammah ya ce yana son ganinmu a falonshi

Ga mamakina sai na iske Ya Azeez zaune kusa da Hammah

Bayan mun zauna ne aka kara gajeruwar gaisuwa Hammah ya katse hirar tamu da fadin, “Ku ba ku gajiya da magana, kamar ba a gida daya kuka kwana ba. Bari mu yi abin da ya tara mu a nan.”

Sai muka kara nutsuwa, hade da tattara hankalinmu a kanshi.

“Dukkanku nan jinina ne, babu bare a cikinku, Maryam diyar kanwata ce ita ma ƴata ce duniya da lahira. Duk abin da ya shafe ku da ni ita ma ya shafe ta. Na zabi in tattauna da ku ne ko in fada muku abin da nake son fada a yanzu saboda ku hankalta. Kada ku kai kanku ga halaka saboda da duniya. “

Ya nisa kadan kafin ya ce” Kun san dai a kaf dangina bangaren uwa da na uba, babu wani shahararren mai kudi sai dai rufin asiri. To a haka na taso, na yi karatun allo a Maiduguri, ban yi nisa ba na dawo gida, na dan taba karatun boko shi ma na watsar saboda rashin abun karatun. Karshe na zo Mubi ina sana’ar tura ruwa, daga wannan sana’ar na koma dinki. Daga dinki na koma tsaron shago. Inda a nan ne labari ya fara canjawa… “

” Mutumin da nake wa tsaron shago babban maikudi, da ace zan kira sunanshi a yanzu za ku shaida zuriyarshi, tun da shi Allah Ya yi mishi rasuwa, amma ba wannan nake son ku sani ba. Bayan kasuwancinshi na zahiri, akwai kuma na badini wanda ba kowa ne ya sani ba. Shi ne safarar miyagun kwayoyi. A lokacin ban ga wata sana’a mai kawo kudi kusa gami da riba ba kamar ta.

Ya kan yi odarsu daga kasashen waje zuwa Nigeria, sannan ya rika rabawa abokan huldarsa

Ina daya daga cikin yaran shi da yake turawa kaiwa ko amso kudi duk lokacin da harka ta fada

Yadda ya amince mun ne ya sa ni ma nake fita da fita ta.

Duk lokacin da aka kawo kaya nike zuwa Lagos in taho dasu, daga can nake yagar nawa rabon

Cikin kankanen lokaci sai na fara dakuna kudi ni ma. Na nemo auran Adama ba jimawa aka sha biki.

Yadda harka ke kara bude mishi haka ni ma take kara bude min

Watarana ya ba ni sako zuwa wata jiha, kudi ne ne zunzurutu har miliyan daya na karbo mishi. A lokacin miliyan daya ba karamin kudi ba.

Tun da na shigo layin nake cin karo da mutane, kafin daga bisani na ji cewar Allah Ya yi mishi rasuwa

Sosai mutuwarshi ta girgiza ni, saboda lafiya ƙalau muka rabu da safe.

Zuciyata ta rika fada min in ba iyalanshi kudin, wata zuciyar kuma na hana ni, kasancewar babu wanda ya san ya aike ni daga Allah sai sai ni din da kuma shi.

Yadda na ga ana facaka da kudi a wurin zaman makoki ya kara karfafa min gwiwar rike kudin nan

Bayan addu’ar bakwai ni ma na bude nawa harkokin tun da na ga yadda ake yi.

Harkar ce ta rika hadani da mutane daban-daban masu halayya daban-daban.

Kullum idona kara budewa yake yi.

Kudi suka rika shigo min, na shiga yin aure-aure, Sai dai matan basu zama, sun jima wata uku su fita.

Muna cikin kasuwancinmu sai gwamnati ta huro mana wuta, ta shiga dode duk wata kofa da muke amfani da ita

Har mutum biyu aka kama cikin abokanmu, aka yi musu daurin rai da rai

Wannan ya ɗan tsorata mu, mu ka rika ja baya hade da neman mafita.

Wajen neman mafitar ne na kuma haduwa da wasu gungun, wanda su nasu kudin ganye ne

Wannan harkar kam akwai kawo kudi duk da ita ma akwai hadari.

Shi ya sa ina yin ta ina kuma neman canji

Sai na kara haduwa da wata kungiyar.

Kun san Hausawa sun ce wai shege shi ya san makwancin shege

Duk irin halin da kake aikatawa, Sai ka ga Allah na ta hada ka da masu irin wannan halin.

Nasu tsarin ya fi kwanta min, duk da su sabawa Allah ne ƙarara.

Ban taɓa kashe wani ba kam, amma na shiga kungiyar asiri, wacce ita ta haɓaka min arzikina fiye da tunaninku

Ni da kaina ban san iya adadin abin da na mallaka ba.

Na sa aka rufe min bakin kowa hade da dauke hankalin duk wani da zai sanya min ido

Shi ya sa nake abuna hankali kwance. Kafin Maryam ta fara bibiyata.

Daga lokacin da na ga ta yi nisa wajen bibiyata sai na sanya aka yi mata turen aljanu hade da rike mata kurwa, aka bude mata ido ta rika gane-gane. Kullum ciwo ba sauki”

Yana kaiwa nan na yi saurin dago ido ina kallon Aunty, ita ma ashe ni din take kallo.

Maganarshi ce ta kuma janye hankalina zuwa kanshi “Ni ne nan na kashe karen Abdul’azeez allurar guba na sanya aka yi mishi, saboda yadda yake kokarin tona min asiri tun kafin Maryam ta san halin da nake ciki.

Watarana ina bacci sai na yi mafarkin wani abokin huldarmu ya rasu, amma ni ban san ya rasu din ba

Sai dai kawai na hadu da mutane dauke da gawa, shi ne nake tambayarsu wanene.

Sai suka ce min wanene, har ma suka sauke makarar zuwa kasa, ni kuma na yaye likafanin da aka lullubeshi.

Sai naga jikinshi baƙiƙƙirin duk ya mokade, hakoran shi sun fito zako-zako, gashin kansa ya nade kamar ya kone a gashin

Sai na saki likafanin jikina ya yi sanyi, su kuma suka dauki gawar zuwa makabarta

Ina tsaye a wurin sai ga wani mutum ya zo wucewa ya ce min “Wancan abokin naka ya ci haramun ne. Shi ne tsokarshi ta kone sai kashi.”

Yana gama fada min haka ya wuce, ni kuma na farka, ban kara komawa bacci ba har gari ya waye.

Wajen karfe goma na safe aka kira ni a waya, abokin nan nawa ya yi gobara ya kone kurmus, kwatankwancin yadda na gan shi a mafarki haka na gan shi a, zahiri lokacin da na je jana’iza

Tun daga lokacin na tsorata, ko bacci ba na iya yi, na fara tunanin tuba, saboda kaf dukiyata ba ta halak ba ce. Ban ji dadin yadda na ci da ku da haram ba, na shayar da ku da haram, na ba ku ilmi da haram, na yi muku suttura da haram.

Don haka ku ci gaba da rokon Allah gafara, ni ma ko nema min gafara a kan ayyukan da na aikata ba daidai ba, saboda kawai in samu kudi

Hakika ina cikin nadama hade da daukar alkawarin ba zan kara komawa inda n baro ba

Kuma na tattare duk wata dukiya tawa zan bayar da ita.

Zan koma in sayar da gonarmu ta gado, in nemi wata sana’ar da kudin halak.

Na fada muku wannan ne saboda ku sani a yanzu ni ba ni da komai, Sai gida da kuma mota ta, sannan na aje mana abincin da za mu ci. Shi ma hakan ya faru ne bayan doguwar tattaunawa da mu ka yi da Malamai”

Falon ya yi tsit bayan da Hammah ya yi shiru kowa da abin da yake tunani, tsawon lokaci babu wanda ya ce komai, sai Aunty Karima ce ta katse shirun da fadin.

“Zan dan yi magana.”

“Muna sauraronki.” Hammah ya amsata, bayan shi babu wanda ya ce komai

Ta kara tattara nutsuwarta wuri daya kafin ta ce “Ni alfarma zan roka wurin Aunty.”

Da sauri Aunty ta dago tare da fadin “Ni kuma?”

Jinjina kai Aunty Karima ta yi kafin ta ce “Ina rokon alfarmar ki yafewa mahaifiyata ne a kan abubuwan da ta yi miki, na san kin sa ta cutar da ke, idan kuma ba ki sani ba yau zan fada miki.

Rashin shiga dakinki da Hammah ba ya yi, ita ce ta raba ku, sace-sacen da Azeez ke yi da rashin son karatu ita ce ta yi mishi asiri. Yanzu haka akwai asirin da ta yiwa Abdallah, aka sanya shi a cikin kwalba. Sai dai kuma malaminta ta tabbatar mata da an tono kwalbar. Shi ne ta je ya canjo mata wani, bayan ya yi mata aikin ne a kan hanyarta ta dawowa Allah Ya yi mata rasuwa. Don Allah Aunty da ke da Azeez ku yafe mata, kullum da abun nake kwana, ban san halin da take a can ba. Yanzu haka kawarta Gana da suke zuwa tare ansar maganin ta haukace.”cikin kuka Aunty Karima ta karasa maganar.

Falon ya kuwyin tsit, Sai Aunty ce ta ce” Ba komai na yafe mata, Allah Ya yafe mu ba ki daya.

Yanzu kam gabadaya muka hada baki wajen fadin “Amin”

Shiru ya kuma ratsa falon kafin Hammah ya ce “Shi kenan za ku iya tafiya, Sai dai kafin nan ina son ku zauna lafiya da Aisha ke Karima. Yanzu dai ba ku da wata uwa sai ita. Ke kuma Aisha ga amana nan na ba ki, da raina ko ba raina ki zama uwa a gare su.”

A sanyaye Aunty ta ce “Allah Ya ba ni iko”

“Amin” mu ka kuma amsawa a tare

Shirun da ya yi yawa ne Hammah ya ce “Mu tashi idan babu mai wata magana.”

Kamar dama  jira muke, , duk muka yi waje kowa jiki babu laka.

<< Da Magana 37Da Magana 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×