Skip to content
Part 9 of 26 in the Series Da Magana by Matar J

Kamar ko wane lokaci 6pm na baro school, lokacin da na iso gida a nan kiran sallahr magriba.

Hakan bai hanani zuwa wurin Dog ba. Biscuit din da na sawo mishi na rika mika mishi yana ci daga hannuna.

Sai da ya cinye tas sannan na shafa bazagar din gashin jikinshi na ce “Je ka sha ruwa”

Ya dan yi kukansu na karnuka yana kallo na.

“Je ka sha ruwa Dog” na yi maganar hade da tura shi wajen ruwan.

Tsaye na yi ina kallon yadda yake shan ruwan da harshe.

Tsoron Allah Ya kama ni, irin wadannan bambancin dabi’ar kadai ya isa ya tabbatarwa da mutum akwai Allah.

Shan ruwa da harshe har a koshi, wasu dabbobin kuma bakin suke tsundumawa, wasu kuma Sha suke suna daga kai sama.

Wato shi yin kiwo, ilmi da basira yake kara wa mutum .

Da wannan tunanin na wuce zuwa kofar mu.

Aunty ce ta bude min kofar hade da tambaya ta “Ina kika tsaya ne? Kuma Ina ta kiran wayarki a kashe, in ji ko ba ki samu abun hawa ba ne, in zo in dakko ki.”

“Na samu, ina shigowa gida ana kiran magriba, na tsaya wajen Dog ne.”

“Wai waye ya kawo mana kare kuma, dazu ya ishe mu da kuka.”

“Ya Azeez ne ya kawo, shi ne ya ce na rika kular mishi da shi. Aunty kila ma yunwa yake ji, da kin ba shi abinci.” na karasa maganar a shagwabe.

“Ni zan tsaya ina kiwon kare? Ke dai da kika ga za ki iya Allah Ya taimaka. Shi Abdul’azeez din ya rasa abin da zai kawo miki kiwo sai kare. Kare fa.”

Dariya na yi kawai lokaci daya kuma na nufi dakina.

Kaya na fara cirewa na yi wanka tare da yin alwalar magriba.

Bayan na fito doguwar riga irin na robar nan na saka da hijab, don yin sallar magriba.

Bayan na idar kitchen na nufa, abinci na zubo, kafin na zauna a kan kujera, ina ci hade da kallon wani Philippines series film, Mai suna The General Daughter.

Knocking kofar da na ji ana yi ne, ya sanya ni nufar kofar.

Ya Azeez ne tare da wata mata, wacce ta rufe fuskarta da face mask.

“Sannunku da zuwa.” na yi maganar a kokarina na dauke idon matar daga kaina, kallona take kamar alkibla.

“Sit here, I’m coming” ya fada hade da nunawa matar daya daga cikin kujerun falon.

Ganin har lokacin idanunta a kaina suke, tamke fuska na yi tare da murguda mata baki, na shige dakina.

Ta window na ga sakkowar Aunty da Ya Azeez.

“Sannu da zuwa” cewar Aunty lokacin da ta shigo cikin falon sosai.

Ga mamakina sai na ga matar ta zame kasa, kamar za ta yi wa Aunty sujada tana gaishe ta. Yayin da Ya Azeez ya fice daga falon

Duk yadda Auntyn ta yi a kan ta koma saman kujera, ƙi ta yi.

“Maryam!” Aunty ta kwada min kira.

Na amsa tare da fitowa zuwa falon

“Kawo ma bakuwa ruwa”

Komai ban ce ba, na nufi kitchen, madaidaicin tire na dakko, tare da jero mata abubuwan motsa baki.

Bayan na aje ne na kuma nufar kofata. Ban rufe kofar ba, saboda gulma nake son yi, haka nan hankalina bai kwanta da matar ba

“Sunana Madina Kallabi, kila na san kina jin sunan” cewar matar lokacin da take janye face mask din da ke fuskarta. 

Madaukakin

Mamaki ya bayyana a kan fuskar Aunty yayin da take fadin “Sosai ina jin sunan, kuma Ina ganin ki a poster da gidajen TV, Lafiya dai ko, in ji dai ba wani abu Abdul’azeez din ya yi miki ba?”

Murmusawa ta yi tana fadin “Bai yi min komai ba Momy”

“Momy!” na maimaita abin da ta fada hannuna a kan haɓa”

“To da sauki. Bismillah ga ruwa nan” cewar Aunty tana nuna mata tiren da na ajiye.

Da wata irin munafukar kunya da na rasa dalilin yin ta, ta dauki ruwan ta sha kadan.

Shiru ya dan ratsa wajen kafin Aunty ta ce “Rankiyadade lafiya ko, kin yi shiru?”

Kai ta kuma ajewa a kasa kamar tunkiya tana murmushi, kamar ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta ce “Ban san ya za ki dauki maganata ba, ko ki kalle ni, amma alfarma na zo nema a wajen ki”

“Ni din. “cewar Aunty tana nuna kanta

Kai Madina ta jijjiga alamun eh.

“To ina jin ki” cewar Aunty lokaci daya tana tattara hankalinta a kanta.

Kan ta kuma yin kasa da shi sannan ta ce “Ina son hada iri da ke ne, ina fatan za ki amince min?”

Cikin murmushi Aunty ta ce “me zai hana.”

Nisawa Madina ta kuma yi cike da jimamin abin da za ta fada ta ce “Ai ban san yadda za ki kalli abun ba, kila ki ji ya yi miki nauyi.” 

“Zan kalle shi da idon basira, ki tafi kanki tsaye ” cewar Aunty cike da alamun karfafa mata gwiwa.

Kila wannan ne ya sa kai tsaye ta ce “Abdul’azeez nake so, kuma so na gaskiya da amana, so na aure ba na shashanci ba.” idanunta zube a kan Aunty lokacin da ta kai karshen maganar tata.

Kila ba ni kadai da nake rabe ba, hatta Aunty maganar ta zo mata a bazata, saboda kai ta shiga jinjinawa alamun maganar ta yi mata girma bayan ta rufe bakinta da ta hangame, tun farkon maganar Madina

Madina ta dora da” Kin san dai matsayina a garin nan, takarar yar majalisa nake nema, kila wannan ya zame min abun kunya, Sai dai ban damu ba, idan har burina zai cika na auran Azeez. Zan iya aje wannan takarar saboda shi. Allah ne ya jarabce ni da shi, wlh ina son shi, son da ban taba yi ma wani dan adam ba. “ta kuma diga aya tana kallon Aunty wacce ta yi zugum alamun tunani

Tsawon wasu dakikai suna a shiru, kafin Aunty ta katse shirun da fadin” Ikon Allah! Wannan dai Abdul’azeez din ba wani ba?”

“Shi nake nufi, na san kin ji maganar gingirin, kamata ya yi ace yata nake nemawa auranshi ba ni ba, to yana iya, na san kila na yi abun kunya “

Kai Aunty ta kuma jinjinawa tare da fadin “Wannan ba abun kunya ba ne, ga ma’abota ilmi, saboda shugabanmu annabi Muhammad S. A. W da irin wannan auran ya fara, kuma aure ya yi albarka.”

“Na gode Mommy, ban yi tunanin wannan amsar daga gare ki ba” cewar Madina a ladabce

“To amma ba a nan gizo ke sakar ba” Aunty ta fada hade da gyara zamanta, har zuwa lokacin akwai alamun jikinta a mace yake gami da maganar Madina

“Menene?” da sauri Madina ta tambaya. 

“Kin ga Abdul’azeez, baya aiki baya kasuwa, in fact ko karatun ma bai gama ba, muna da abin da za mu yi mishi aure idan yana so, amma yau da gobe fa?” 

“Duk na san wannan, kuma a wurina ba matsala ba ce, ni nan zan dauki nauyin komai na auran, kuma na yi alkawarin zan kai Abdul’azeez duk kasar da yake so domin yin karatu, idan har kuka amince min na aure shi.” Cewar Madina da kwarin gwiwarta

Shiru Aunty ta yi kamar bazata ce komai ba, can kuma sai ta ce” Shi kenan, ki dan ba ni lokaci don Allah.”

Daga haka ta mike tare da kwada min kira, na amsa hade da fitowa

“Je ki duba mata Azeez a waje, ni zan yi sallah “

Ba ta jira amsa ta ba, ta fara hawan stairs din.

Idona na dauke daga kan Aunty na mayar kan Madina, wacce ta koma kan kujera ta zauna.

A shekaru ta tasarma arba’in, amma da yake akwai kudi da kuma gyara, Sai ka dauka, ba ta wuce 30 ba. Fara ce, amma ta hada da mai, ba ta jiki, Sai dai ko ina na jikin nata a cike yake. Fatar nan lukui alamun jin dadi ya bayyana.

“Maryam ko?” ta katse min tunanin da nake yi.

Kadan ta murmusa, hade da mikewa ta dafa kafadata daya “Na san kina son Azeez.”

Sautin murmushinta ya fita kadan “Ina ba ki shawara ki cire shi a ranki, saboda na riga ki, kuma na shirya mallakarshi ta ko wane fanni, da zarar na mallake shi, zan dauke shi daga idon irin ku zuwa wata kasa, inda za mu yi rayuwarmu peacefully babu barazanar irin ku.”

Komai ban ce mata ba, kunnuwana ne kawai suke sauraron ta

“Sai da na shirya tsab, sannan na fito, na san wadanda zasu iya ba ni matsala, kuma tuni na magance hakan. Je ki nemo min shi.”

Ta kai karshen maganar yayin da take zama a inda ta tashi.

Jiki a sabule na nufi kofar, ni kaina yau na tabbatar son Ya Azeez nake yi, daga lokacin da su Aunty suke tattaunawa da Madina zuwa yanzu da Madina ta kara tabbatar min da za ta auri Ya Azeez hankalina a tashe yake, yayin da zuciyata ke wani irin zafi, idanuna ma bishi – bishi nake gani. Ni ban san yadda zan iya fasalta yadda nake ji ba, duk yadda zan fasalta zan ji na rage wani abun. 

Tun daga ranar da na duro kafata a gidan Allah Ya jarabce ni da son Ya Azeez, komai na shi ni burgeni yake, shi ya sa nake sadaukar da kaina, wajen yi mishi abin da zai ji dadi, duk da ba zan iya gane yana ji ko baya jin ba, amma ban taba gajiyawa wajen yi mishi hidima ba. 

Duk lokacin da ya aikata ba daidai ba, na ji Aunty na gwada tana juyewa a kan shi, Sai in ji kamar zan fasa ihu. Tun ba Hammah ba, wanda yake gwada mishi kwanji ko ya kai shi station a dan sassamashi. Wannan kuma shi ne karshen tashin hankalina saboda duk ranar da zare ya zarga a, tsakanin Hammah da Ya Azeez har policestation to ranar cin abinci da bacci sun kaurace min har sai na ga ya dawo. 

Shi ya sa nake matukar boye laifinshi a kaina, idan zai kashe ni in dawo duniya a tambaye ni Azeez ne ya kashe ni zan ce ba shi ba ne. Kullum soyayyar shi kara girma take yi a zuciyata

Haka na rinka jan kafa har wurin Dog, saboda na san baya wuce wurin.

Tsugunne yake gaban kwanon da ake sanyawa Dog din abinci, madara ce yake tsiyaya mishi, Dog din yana lashewa.

A sabule na karasa dab da su, tsaye na yi ina kallon su ba tare da na ce komai ba.

Sai da ya gama ne ya ce “Anything?”

Ajiyar zuciya na sauke a hankali tare da warware hannuna da na dora a kan kirjina na ce “Aunty ta ce ka zo ku tafi.”

“OK” ya fada lokacin da yake wanke wurin shan ruwan Dog ya sanya mishi wani.

“Ki rika wanke mishi wurin cin abincin shi, duk lokacin da za ki sanya mishi wani”

Kai na daga alamar to lokaci daya kuma na dafa mishi baya.

Kai tsaye dakin Aunty muka wuce, zaune take kan sallaya da alama idar da sallahrta kenan.

Shigowarmu ya sanyata mayar da hankalinta a kanmu. Ya Azeez ta kafe da ido, har sai da ya yi dariya mai sauti, lokaci daya kuma yana shafa tarin bakar sumarsa, dariyar da ta kara mishi kyau sosai, shi ba miskili ba ne, amma bai faye yawan surutu ko dariya ba, ko wane lokaci fuskarsa a hade kamar kullum dai cikin bacin rai yake. Shi ya sa idan ya yi dariya ko murmushi sai ya canja, wani kyawu na musamman ya bayyana.

Kai ta girgiza cike da jimami ta ce “Azeez me kake fadawa matar nan ne ta ce tana son auren ka?”

Hannayensa ya mayar cikin aljihun wandonsa ya ce “Nothing. Ni da ko wurinta ma ba na zuwa, ita ce take zuwa wurina” yadda yanayinsa ya canja, zai sa ka fahimci gaskiyarsa ya fada.

Riƙe da haba Aunty ta kuma da gasken ” kana sonta?”

Shiru ya dan yi kafin ya ce “I don’t know.” ya kuma nisawa alamun ya yi nisa cikin tunani tare fadin “Kai! I don’t know.”

Aunty ta kuma tattare hankalinta a kanshi sosai “Amma kana ganin ba matsala?” 

Ya kuma yin wani shirun kafin ya ce “I don’t know.”

Nisawa Aunty ta kuma yi sannan ta ce”Ku je. Allah Ya yi mana zabi ma fi alkairi.”

Ni dai a zuciyata na amsa shi kuma ban sani ba, ya amsa ko bai amsa ba.

“Maryam wai ina wayarki? “Aunty ta tambaye ni idanunta kafe a kaina

Sai a lokacin na tuna da batun waya, tun da na dawo hankalina bai kai kanta ba.

“A gida na bar ta da zan tafi school, kuma da na dawo ban duba ta ba tukun. “

“Azeez na gidan kika bar wayar ki, bayan kin san kofarki ba rufuwa take ba, Allah Ya sa bai dauke ta ba”

“Amin” na amsa jiki a mace.

Zamanta ta gyara, tare da fuskantata, alamun magana mai muhimmanci.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Da Magana 8Da Magana 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×