Bismillahir-Rahmanir-Raheem
Garin Sandamu, Daura
Kangiwa junction, Fatima ce tsaye hannayenta rungume da atamfofin da ta karbo a gidan kawar mamanta. Sosai hankalinta yake a tashe, musamman idan ta daga kai ta kalli hadarin da ya hadu ya yi bakikkirin, a ko wane lokaci zai iya sakko da ruwa. Ganin ba ta samu mashin ba, ya sa ta fara takowa da kafa, har zuwa kan hanyar da ta fi Katsayal. Amma dai har zuwa lokacin ba ta samu abun hawa ba, ga ruwa ya fara sakkowa.
Ba ta da zabi da ya wuce kodai ta ci gaba. . .
Da kyau Hajiyatah 😍, muna jiran cigaba
Na gode