Duk surutan da Aunty Bilki da Mustafa suke yi, Fatima na jin su, uffan ba ta ce ba.
Sosai abun ya ba Aunty Bilki mamaki, musamman da ta ce ta dora mata miya, ita za ta je wani gidan suna.
A nan ma Fatiman ba ta ce komai ba, har Aunty Bilki ta shirya ta fice.
Bayan fitarta ne Mustafa ta dube ta, kafin ya yi magana ta ce, "Ina wuni?"
"Akwai matsala ne?"
Kai ta girgiza alamar a'a, har zuwa lokacin kuma ba ta kalle shi ba, illa wasa da take yi da yatsun hannunta.
"Fatima!" ya kira. . .