Skip to content
Part 12 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Duk surutan da Aunty Bilki da Mustafa suke yi, Fatima na jin su, uffan ba ta ce ba.

Sosai abun ya ba Aunty Bilki mamaki, musamman da ta ce ta dora mata miya, ita za ta je wani gidan suna.

A nan ma Fatiman ba ta ce komai ba, har Aunty Bilki ta shirya ta fice.

Bayan fitarta ne Mustafa ta dube ta, kafin ya yi magana ta ce, “Ina wuni?”

“Akwai matsala ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a, har zuwa lokacin kuma ba ta kalle shi ba, illa wasa da take yi da yatsun hannunta.

“Fatima!” ya kira sunanta a hankali bayan shirin da ya ratsa wajen.

“Shekaranjiya kin zo min da wata magana a gidan Aunty Hauwa. Na yi tunanin kawai dai wasa kike yi, shi ya sa ban ce komai ba. Amma jiya still sai ga wasikarki da ke kara jaddada maganarki.” ya dan nisa kafin ya ci gaba.

“Maganar gaskiya Fatima kaina ya kasa dauka, ji nake yi kamar mafarki. Wannan abu ne sam da ba zai yiwu ba. Don Allah mu bar wannan maganar.”

“Ni na san zai yiwu, sai dai kawai ka ce ba za ka iya aurena ba, saboda kai ma kana min kallon mara hankali.”

Murmushi ya yi tare da gyara zaman shi “Hmmm! Fatima ke har yanzu yarinya ce, akwai kuruciya a tare da ke. Sam ba ki hango abin da na hango ba.”

“Me ka hango?” wannan karon ta dago kai haɗe da kallon sa.

Shiru ya kuma ratsa wajen kafin ya ce “Fatima ke ba sa’ar aurena ba ce gaskiya ta ko ina kin wuce da ajina.”

Sosai take kallon sa,  “Me kake nufi?”

“Ina nufin kin fi karfina.”

Duk da ba ta ce komai ba, ya fahimci karin bayani take jira daga gare shi.

“Ki dubi gidanku ki dubi namu, bambancin ma a bayyane yake. Sannan ki kalli gidajen da yan’uwanki mata suke aure. Kin san ni din idan aka hada da mazajen ƴan’uwanki, tamkar mai goge masu mota ne. Ni ma zan so ace ki auri mai dan abun hannu ba irina ba Fatima.”

” Hmmm! Wannan ba hujja ba ce Ya Mustafa, kawai dai kana neman hanyar kaucewa bukatata ne. ” cikin raunannar murya ta fadi hakan.

“To je ki ma abin da na fada ba hujja ba ce. To karatunki fa. Kaf yayyunki mata babu wacce ba ta yi karatun gaba da secondary ba, sannan suna aiki. Kina ganin Alhaji zai amince da maganar auranki a iya secondary school kuwa?”

“Ya Mustafa ni fa abu daya kawai na ce. Gobe ka je ka nemi aurena wajen Babana. Amma duk wani kalubale kuma wannan daga baya ne. Idan ka je ka tambayi aurena, Babana ya ce bai amince ba, sai ka kawo min wadannan maganganun.

Shiru ya yi cike da nazarin maganganunta, “Yanzun idan ya amince fa?”

“Shi kenan. Ko ba ka bukatar hakan?”

Kai ya girgiza alamun a’a.

“Za ka tura goben?”

Kai ya jijjiga alamar eh.

Shiru ya kuma ratsa falon, kafin ta Mike zuwa kitchen.

Ya jima zaune a falon,, hannayensa biyu rungume da habarsa.

Jin abun yake kamar almara, ya daga shekaranjiya zuwa ya Fatima ke son sanya shi a tsaka mai wuya.

Anya bai yi wauta ba kuwa da ya amsa bukatarta?

“Me ta isa ta yi min idan na bijire to?”  ya yi tambayar a zahiri tare da dage kafadunsa du biyun sama.

“Ba komai. Iyakaci dai ta daina yi min magana.” ya ba kansa amsa. Kafin ya kara dorawa da wata tambayar.

“To idan na san ba zan yi ba, me ya sa na amsa ta?”

Ya yi saurin kallon kofar falon, kamar Fatiman ce za ta shigo.

Ajiyar zuciya ya sauke, lokaci daya kuma ya fito da niyyar tafiya gida.

Kitchen din ya leka, zaune take da wuka a hannu, ta yi tagumi da hannunta guda daya, ta zubawa tukunyar da kan stove ido.

Ita kanta ji take yi kamar ta aikata kuskure, ko tana shirin aikata kuskuren.

Jikinta ya mutu tuɓis, kamar ta ce mishi a bar zancen tamkar yadda ya bukata tun farko.

Burinta shi ne ta zama principal, nurse ko likitar mata. Idan ta yi aure yanzu anya burinta zai cika?

Tsayuwarsa ce ta sanyata juyawa tana kallon shi.

“Zan tafi, sai an jima.”

Bakinta ya yi mata nauyi, kai kawai ta daga alamar to.

*****

Juma’atu babbar rana, ranar da kan bida kan samu. In ji masu iya magana.

Gidan Alhaji Musa bai tsagaita da mutane ba, tun bayan isowarsa, sai misalin karfe takwas da rabi na dare.

A lokacin ne ya samu kebewa da Jamil, wanda yake yi masa bayani a kan wasu gonaki biyu da ake son Alhaji Musa din ya saya.

Shiru ya yi tare da nazari a kan batun sayen gonar. Yana shirin magana ne, Mama ta leko hade da sanar dasu ana sallama.

Jamil ne ya fita, jimawa kadan kuma ya dawo tare da sanar wa da Alhaji, masu sallamar.

Jin ko su waye ya sa ya ce, “Ah shigo dasu ciki da sauri.”

Bayan gaisuwa hade da taɓa hirarrakin yau da kullum, Malam Haruna ya ce, “Mu fa Alhaji da biyu muka zo, wai an jefi biri da rani.”

Tare suka yi dariyarsu ta manya Alhaji Musa ya ce, “To madalla. Menene biyun?”

“Yaronka Mustafa, tun da ai shi din ma Yaronka ne. Shi ne ya ga yarinyar gidan ka, kuma yake kwaɗayin auranta idan ba a yi mata miji ba.” Cewar Malam Salele.

Alhaji da ya ji maganar a ba za ta ya ce, “Wacce yarinya kenan Mustafan ke so?”

Su biyun suka kalli juna kafin Malam Haruna ya ce “Fatima. Kamar dai haka ne sunan.”

Alhaji dai ji yake yi kamar mafarki yake yi. Fatiman da ba taba maganar aure ba, kullum maganar ta a kan karatu ne. Anya kuwa Fatima ta shi kodai wata.

Wayarsa mai kira Samsung ya dauka, lokaci daya kuma ya kira Jamil, tare da, umurtar shi su zo tare da Fatima.

Fatima dama safa da marwa kawai take yi, yayin da kirjinta ya tsananta bugawa, tun lokacin da ta ga su Malam Haruna sun shigo.

Ji ta yi kamar ta tura su baya, sannan ta fada masu an fasa waccan maganar.

Kiran da Mama ta kwala mata ne, ya sanya ta, fitowa bayan ta zumbula dogon hijabin ta.

Jamil na gaba tana bin sa a baya suka shiga sashen Alhaji Lawal din.

Dukkansu a gefe suka rakube, yayin da kirjin Fatima ya cigaba da harbawa tamkar zai bula rigarta ya fito

“Fatima! Da saninki Yayanki Mustafa ya zo neman auranki.”

Jamil ya yi sauri dago kai, yana kallon Alhaji tamkar shi ne Fatiman.

“Tambayarki nake yi.” cewar Alhaji

Kai ta daga alamar Eh.

Jamil ya bi ta da kallon mamaki, kafin maganar Alhaji ta katse shi

“Kin amince da shi a matsayin miji.”

Wannan karon ma sai da ya maimaita tambayar, cikin bazata Fatima ta kuma daga kai alamar Eh.

“Shi kenan. Mustafa ni me zuwa ne ina ma mishi aure, ballantana kuma ya nema a wajena. Tun da Fatima ta amince da shi, to na ba shi ita. Kuma ni da kaina zan biya sadaki. Su je su kara daidaita kansu, sai mu tsayar da ranar daura aure.”

Jamil ji yake kamar ba a kan kafafunsa yake ba. Take kominsa ya tsaya da aiki na wucin gadi.

Kafin daga bisani ya mike tsaye, ba tare da ya cewa kowa komai ba, ya fice daga sitting room din.

Ita kanta Fatima ba ta yi tsammanin jin haka ba. Sai gabanta ya lillinka faduwa. Har sai da ta danne shi da hannunta na dama.

“Ta shi ki je.” ta tsinkayi muryar Alhaji yana fada.

Fadawa ta yi kan katifarta hade da fashewa da kuka. Kukan da ba ta san na menene ba.

Kuka take yi sosai kamar an aiko mata ta rasa iyayenta duka biyun.

Za ta iya cewa tun da ta zo duniya yau ce rana ta farko, da ta taba irin wannan kukan.

Jamil kuwa kofar gida ya fita. Tsaye ya yi tare da rike kugunsa. Jin abun yake kamar fadowar gini ko saukar ungulu.

Yaushe Fatima da Mustafa suka shirya wannan?

Wannan yana nufin ya rasa Fatima kenan?

“Kai ina!” ya yi maganar a zahiri tare da hade hannayensa du biyun ya matsa. Ji kake yi “Ƙaƙas! Ƙakas!! Ƙaƙas!!!”

A can gida kuwa bayan fitar su Malam Haruna cike da farin ciki, baya ce ta haihu.

Domin kuwa Mama tsalle ta yi gafe guda ta ce ba ta yadda da wannan auran ba. Fatima Jamil za ta aura ba Mustafa ba.

Shi dai Alhaji tun da ya fada mata hukuncin da ya yanke, bai kara tofa komai ba. Ita ce kawai inda take shiga, ba nan take fita ba. Har ta gaji ta fice zuwa dakin Fatima.

Kwance ta same ta, tana shesshekar kukan da ta yi.

Shigarta ya sa Fatiman ta mike daga kwancen da take, lokaci daya kuma tana kara goge hawayenta.

“Fatima. Ke ce kika ce Mustafa ya zo neman auranki?”

Kai ta daga alamar eh.

“Hmmm!” Mama ta fada cike da takaici kafin ta ce.

“To tun muna shaidar juna, ki ce masa ya janye maganar wannan auran. Saboda na riga na yi miki miji.”

“Ya Jamil Wai?” Fatima ta tambaya, kafin kuma Maman ta ba ta amsa ta dora

“Ai na fada miki bana son shi. Ba, zan aure shi ba Mama. Ni Mustafan nake so. Ba zan zama matar cushe ba.”

A zuciye Mama ta ce,

“Ni kike fadawa magana haka. Ke idan Jamilu ma ya aure ki ai taimakonki ya yi. Don wallahi a haka nan dai ba sidi ba sadada Jamilu ya fi karfinki.”

“To ai wannan dalilin ya sa na zabi Ya Mustafan, saboda Ya Jamil din ya fi karfina. Mama kullum fada kike yi Ya Jamilu dai ya fi karfina. To me ya sa kike damuwa da dole sai ya aure ni. Ki bar daidai karfina ya aure ni mana.”

“Fatima. Ni ce fa na haife ki, ni ba kawarki ko kishiyarki ba ce da zan rinka fada kina fada. To ina kara jaddada miki ba za ki auri Mustafa ba.”

“Ni kuma shi zan aura, ba zan auri wanda yake ganin aurena alfarma ya yi min ba.” cikin kuka Fatima ke magana.

Take Mama ta rufe ta da duka ta ko ina.

“Ni kike fadawa magana haka, don ubanki Mustafan fin Jamilun ya yi, to sai in ga yadda za ki auri Mustafan ai.”

Fatima ma bakin bai mutu fadi take

“Ni kuma wallahi sai dai a kashe ni, amma ni ba zan auri Ya Jamil ba da baya sona. Ya Mustafa zan aura.”

Kwakwazon da Fatima ke yi ne ya sanya Alhaji fitowa.

Sosai Mama ke jibgar Fatima tana fadin, “Yar banzar yarinya da ba ta ganin kowa da daraja. Ni za ki kwancewa zane a kasuwa? Rashin kunyarki ashe har ta kai haka, ina fada kina fada, to don ubanki sai dai ki nemi wata uwar amma ba ni ba, kuma wallah…”

“Kai! Kai!! Kai!!!” Alhaji ya daka masu tsawa.

“Ya isa haka da Allah. Me ye haka? A gidana Hajara? Baki za ki yi mata? Na ce baki za ki yi mata.”

Mama da ta dakata da dukan Fatima ta ce, “Bakin ma ai sai in yi mata, don tabbatar ni din uwarta ce.”

“To ba a nan gidan ba kuma. Fatima dai nine da ikon aurar da ita. Kuma na ba Mustafa ita. Da ace Jamilu yana son Fatima da ya yi magana kamar yadda Mustafa ya yi. Kamar yadda Fatima ta fada ke ce ke cusa mishi ita. Ni ma kuma ba zan goyi bayan a cusa mishi ita ya aura baya so ba. Ki bar yara su auri wadanda suke so.”

“Wallahi Alhaji shi ma Mustafan ba son shi take yi ba, kawai don ta bakanta min ne ta yi. Kuma ta je ai za ta ga… “

“Na ce miki idan kika yiwa yarinyar nan baki Hajara za ki ga bacin raina.”

Mama ba ta kuma cewa komai ba ta shige daki cike da bacin rai. Ji take yi dai kamar ta murde wuyan Fatiman.

“Wuce dakinki.” Cewar Alhaji lokaci daya kuma yana juyawa na shi bangaren.

Jamil da komai ya faru a kunnensa ya sauke ajiyar zuciya, haɗe da sosa tsakiyar kansa.

Fatima wata irin mace ce mai dagiya gami da kafiya a kan duk abin da ta sanya a gaba. Idan za a juya ta dambu ya taliya ba za ta canja ra’ayi ba.

Idan ta ce yes, to tana nufin yes din, haka idan ta ce No, to No din take nufi. Ba kuwa karamin abu ne, zai sanya ta sauka akan Yes da No din ba.

Ko kadan ba ta bari a danne mata hakkinta, idan dai a man hakkinta ne to kowa ma za ta iya gogawa da shi.

Gaskiya kuwa kamar littafi, komai girman mutum ya fada ba daidai ba, kafin ya dire za ta nuna alamar abin da ya fada ko ya yi ba fa daidai ba ne.

Shi ya sa ake ce mata mara kunya. Ya san kuwa ko gidajen sama zasu dawo kasa, na kasa su koma sama, tun da ta ce ba ta auran shi tabbas ba za ta aure shin ba.

To ina ma sauran fada an cire ido, Alhaji ya riga ya buge bakin tsanya da tabarya. Dole ya hakura, tare da kwantarwa da Mama hankali, kada ta sanadiyyar shi wani abu mara dadi ya faru a family din.

Da wannan tunanin ya shiga cikin gidan. Tamkar bai san komai ba haka fuskar shi ta nuna.

Mama da ke zaune kan kujera zuciyarta na tafasa, ta amsa sallamar shi da kyar.

“Lafiya Mama?” Jamil ya tambaya daidai yana zama kan kujera.

“Hmmm! Ni da wannan yar banzar yarinyar. Wato yarinyar nan ni za ta watsawa kasa a ido.”

“Wace ce?”

“Fatima.”

“Me ta yi?” ya kuma tambaya

“Wai Mustafa yarinyar nan ta turo ya tambayi auranta.”

“To karatun fa?”

“Oho mata, ta karatun take yi don ubanta, auran ne kawai a gabanta. Ban san lokacin da yaran nan suka shirya haka ba. Kuma wallahi ni na san Fatima ta yi ne don ta bata min rai. Kuma za ta ga bacin ran nawa. Don idan har ta tsaya a kan bakanta wallahi cokalina bai zuwa dakin ta. Sannan duk wasu sabgoginta ta cire ni a ciki.”

Jamil ya sauke ajiyar zuciya, cikin karfin hali ya ce, “Haba Mama, don Allah ki daina fadin haka. Kin san halin Fatima fa…”

“Ai shi ya sa ta raina kowa, take ganin kowa bai isa ya sanyata ko ya hana ta ba, amma a wannan karon wallahi idan dai sunana Zuwaira Fatima za ta yaba ayarta zaki. “

“Mama komai da zai faru da Fatima Allah ya riga ya tsara mata shi, bi kawai take yi.”

” To ni ma Allah ya riga ya gama tsara min abin da zan yi mata ai. Aiwatawar kawai zan yi. Kuma don ubanta muddin ba ta janye wannan kudurin ba, wallahi sai dai ta nemi wata uwar da wani gidan amma ba wannan ba. Ai uban nata zai tafi jibi idan Allah ya kai mu.”

Murmushin yake Jamil ya yi kafin ya ce, “Abi komai a sannu don Allah Mama.”

“Kai Fatima fa ba tun yau ta raina ni ba. Kuma wancan taurin kan nata mai kama da na arnan farko zan gyara mata shi wallahi. Da ni take labari. Ana nema mata dadi tana shirme. Duk hakkilon da nake yi ba don ita nake yin sa ba.”

“Don Allah Mama ki bar maganar nan, tun da Alhaji ya riga ya yanke hukunci ki yi mata addu’a. Allah ya sa haka shi ne ma fi alkairi agaremu baki daya.”

Ƙala Mama ba ta  ce ba. Shi ma sai fice daga dakin.

Da ace Mama ta san ya yake ji, to da shi ta rika ba hakuri, ba shi ne zai ba ta.

Lokuta da dama ya kan zauna ya ware lokaci, yana tsara irin rayuwar da zai yi da Fatima idan ya aure ta.

Tuni ya yi zero mine na shi, na ba shi da mata sai Fatima. Ashe shi ne ya yi kidan shi ya yi rawar shi. Fatan shi kawai shi ne Allah ya sa haka shi ne ma fi alkairi a tsakaninsu.

Fatima ta yi mishi mummunar fahimta, tun da yake bai taba kinta ba, kawai dai shi haka yake. Amma ya yi wa kansa alkawari kafin lokacin auran ta, zai sanar da ita bai taba ƙinta ba.

Bangaren Fatima kuwa, tun tana jin motsi da hayaniyar mutane har bacci ya dauke ta.

Abin da ta sani dai kawai shi ne ba za ta taba canja ra’ayi ba, sai idan shi Mustafan ne ya ce bai yi.

<< Daga Karshe 11Daga Karshe 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.