Skip to content
Part 26 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Har sai da aka yi bakwai sannan gidansu Fatima ya tsagaita da mutane, yan’uwanta sun yi rawar gani, don kuwa har aka yi bakwai din sau biyu suke kawo abinci kullum, safe da kuma yamma.

Alhaji kuwa har gida ya zo ya yi masu gaisuwa.

Cikin dakunan bangaren Fatima Ummi ta gyara daya zaman ta ya koma bangaren.

Dakin Inna kuwa basu taba komai ba, kullum su kan shiga su share su gyare shi tsab, tamkar dai Inna ta yi tafiya ne suna jiran dawowarta.

Sau tari ma a nan suke hirar rana da cin abinci, hatta baccin rana su kan yi a bangaren.

Dole Fatima ta kuma daukar girma ta dorawa kanta, ba wasu shekaru ta ba Ummi ba, amma yanzu kulawar Ummin ta dawo karkashin ta, dalilin da ya sa ta kuma danne zuciyarta hade da aro dabi’u na dattako ta dorawa kanta.

Tsawon shekaru uku ita da Ummi basu taba samun sabani irin na kanwar miji ba, tana girmamata shi ya sa ita take kara rike girmanta.

Ana saura sati daya addu’ar arba’in din Inna, sunan Mustapha ya fita zuwa Enugu don yin bautar kasa.

Bai tafi ba, sai da aka yi addu’ar arba’in din, sannan ya fara shirin tafiya.

Duk wani abu da ya san su Fatima zasu nema sai da ya tanada daidai iyawarsa, hatta magunguna irin na yau da gobe sai da ya siya ya ajiye.

Ba Fatima ba, hatta Ummi ji take yi kamar Mustapha ya fasa tafiyar, saboda yadda gidan zai kara yin shiru, su biyu kacal zasu rage, don Hana sai ta kwana biyu ma ba ta zo gidan ba, tana wajen Mama ko Goggunanta.

Da misalin karfe hudu Ummi ta yi shirin zuwa gidan koyon dinkin da take yi, don Fatima ta hada mata keken dinkinta wanda Baba ya siya mata lokacin da za ta yi aure, ta ma dauke keken zuwa dakin Ummin.

A kofa suka hadu da Mustapha yana shigowa, don haka ta amshi ledar da ke hannunsa suka shigo tare, sai da ta yi masa sannu da zuwa sannan ta fice.

Ya mayar da hankalinsa kan Fatima da take fitowa daga bedroom.

Tare suka zauna a kan kujera, lokaci daya kuma tana bude ledar da Ummi ta ajiye.

Takalmansa ne ya amso wurin wanki, tare suka yi dariya bayan ta dago kanta daga bude ledar, don ta san ya fahimci ta dauka wani abu ne mai dadi ciki.

“Allah na dauka soyayyar kaza ce.”

Ya kuma yin dariya kafin ya ce “Na sani ai.”

“Wani irin kwadayi nake ji sosai Ya Mustapha”

“Na sani, ki yi hakuri, abubuwan ne sun yi yawa, daga wannan sai wannan, yanzu kam ina kokarin sayen abun hakika ne, kin ga kin shiga wata na takwas fa.”

Sai da ta nisa sannan ta ce “kar ka damu, komai zai wuce, ban damu don ba ka yi min hakika ba, fatana dai kawai in haihu lafiya”

“Bana fatan ki haihu ba tare da na yi miki yanka ba, sha Allah hakan ma ba zai faru ba.”

Duk suka yi shiru, kafin ya mike a hankali zuwa inda take, hannayensa ya zuba a kan cinyarta, muryarsa ya kwanta.

“Ba sai kin fada ba, na sani kina jin wani iri saboda tafiyar da zan yi gobe, kawai dai kin dannewa ne don ba ni kwarin gwiwa, amma ki sani na fi ki damuwa, dole ce kawai za ta sanya ni barinku a wannan katon gidan, sannan a wannan yanayin da kike dauke da ciki. Ki ji a ranki cewa zan tafi ne, amma hankalina kaf yana wurinku, musamman ke, har yanzu ina jin cewa ni ban yi miki komai na kyautatawa ba, ke ce kullum kike min. Ga shi na kara miki dawainiyar Ummi, I’m sorry Ummu Hana, ban so hakan ta faru ba.”

Hannu ta kai hade da dauke hawayen da suka gangaro mata, idan ta ce ba ta damu a kan tafiyar nan ba ta yi karya, kawai dai tana karfin hali ne kamar yadda ya fada, amma har wani zazzabi take ji. Ba ta taba jin damuwa don zai yi tafiya ba, irin wannan karon, kila ko don ba Inna ne oho.

“I’m so sorry.” Ya fada hade da share mata ragowar hawayen.

Ba za ta iya yin ko wace irin magana ba, ruwan hawayen kawai ta bari a matsayin amsar duk wata magana ta shi.

Shi kansa sai ya ji ina ma bai yi magana ba, ya yi shiru ya bar ta, kamar yadda ita ma ta yi shirun tun farko.

Ganin duk lallashin da yake mata hawayen ya ki tsayawa, sai ya shiga bedroom ya dakko mata hijab din ta.

“Ta shi mu fita.” ya yi maganar bayan ya daidaita zaman hijabin a jikinta.

Gidan Ya Bashir ya kai ta wurin Aunty Bilki, a can din kuwa sai ta warware, basu dawo gidan ba, sai bayan sallahr isha’i.

Asubar fari kuma Mustapha ya daga zuwa Kano, cike da kewar gida, Ummi da Fatima kuwa ba mai lallashin kowa, dukkansu kukansu suke sha, mutuwar Inna ta dawo masu sabuwa.

******

Tun su Fatima basu saba da rayuwar kadaicin ba, har suka saba.

Karfe goma Ummi ta tafi koyon dinki, Kasancewar ta kare makarantar secondary, Fatima kuma ta shiga kitchen.

Ranar da ta gaji da zaman gidan sai ta tafi gidan Mama, gidan Yayyunta mata, ko gidan Ya Bashir.

Waya kuwa kullum ne sai sun yi ta sau uku da Mustapha, safe, rana da kuma dare.

Yau ma da ta gaji da zaman gidan ita kadai, sai ta shirya zuwa gidan Mama.

Kasancewar karfe uku ne na rana, Mama kwance take tana taba baccin rana, yayin da Hana ke zaune gabanta ta na taba rigima.

Sallamar Fatima ba ta sanya ta yin shiru ba.

Mama ta amsa sallamar hade da rage karar rediyon da ke gaban ta.

“Wai Mama kina bacci kuma rediyo a kunne” ta fada a lokacin da take zama a kan kujera.

“Ina jin abin da suke cewa, taskar labarai nake jira.”

“Haka kike cewa kullum, kuma Allah na san bacci kike yi.” Fatima kuma fada lokaci daya kuma tana sauke hijabin ta.

Wannan karon tashi zaune Mama ta yi hade da murmushi “Ya kike jin Mustaphan?”

“Yana lafiya.”

“To ai haka ake so, ni ma nan yana kirana muna gaisawa. Ke kuma ya naki jikin, ranar Lami ta ce ta kira ki, wai kanki na ciwo”

“Na ji sauki, babu inda ke min ciwo yanzu.”

“To wannan kumburin kafafun fa, kin je asibiti dai ko?” cewar Mama hankalinta a kan kafafun Fatima.

“Eh na je, sun ce ba komai, wai nauyin ciki ne.”

“Gaskiya dai wannan karon cikin naki ya yi girma, ba kamar na Hana ba.”

Sai a lokacin Fatima ta kalli Hanan da take kananun kuka, kamar za ta ce wani abu kuma, sai ta fasa.

Kamar Mama ta shiga zuciyarta ta ce “Kin gan ta nan, wai lallai dole sai na rakata gidan Hauwa, kamar gidan bakonta ne.”

Murmushi Fatima ta yi, ba tare da ta ce komai ba.

“Kin ji an kawo kudin auran Zainab ko?”

“Eh na ji. Allah Ya tabbatar da alkairi.”

“Amin” Mama ta amsa.

Hira su kai ta yi, sai gab magariba Fatima ta koma gida.

******

Tana kan sallaya, Ummi na cin tuwo ita da Hana da yake yau Hanan ta ga dama ta biyo ta, wayarta da ke gefen Ummi ta yi kara, ta dauka ma Mustapha ne, amma ga mamakinta sai ta ga Zainab ce.

Sai da suka gaisa sannan Zainab din ke fada mata Alhajinsu yana medical center Katsina, daga ganin likita sa kuma aka ba shi gado, amma da sauki sosai.

Fatima ba ta wani damu sosai ba, don dama ya saba zuwa ganin likitan saboda yana fama da sugar, kuma ba wannan ne karon farko da aka ba shi gado ba, daga ganin likitan.

Ta kira shi dai ta yi mishi sannu, da safe da ta kira gida, sai Mama ta shaida mata ai tun asuba suka dauki hanyar Katsina, saboda tana fama da kanta ne, basu yi mata magana ba.

Sai kawai ta yi masu Allah ya kiyaye hanya ta ci gaba da hidimar gidanta.

Koda suka isa can din ma sai da suka hada ta da Alhajin kuma akwai alamun jikin nasa da sauki.

Ranar da ya cika kwanaki uku ne ta ji, ta damu, so take gano shi, amma kuma ba ta da kudin mota, sannan ta san ma Mustapha baya dasu dai a yanzu, tun da wata ya yi nisa.

Amma da abun ta kwana ta kuma tashi da shi, har sai da Ummi ta fahimci wani abu na damun ta.

“Ina son zuwa dubo Alhaji ne Ummi, an ce yana ta tambaya ta” Fatima ta ba ta amsa a lokacin da Ummi ta matsa mata da tambaya.

“To ki tambayi Yaya mana.”

“Ba shi da kudi, kuma bana son tayar mishi da hankali. Kin ga bai wani jima da tafiya ba, duk kudin wurin sa ya yi mana sayayyar abinci dasu”

Kafin su kara magana wayar Fatima ta hau kara, ganin Zainab sai ta daga da sauri

“Yaushe za ki zo?”

“Ina son zuwa ni ma.” Fatima ta ba ta amsa

“Ki samo account no in tura miki dubu uku, gobe ki taso”

“Jikin Alhajin ne?”

“A’a kawai dai yana ta tambayar kina ina.”

“Shi kenan na gode Zainab.”

Ummi ce ta nemo mata account No, Zainab ta tura kudin, aka ciro mata.

Don haka ta kira Mustapha ta fada mishi komai, ya yi mata addu’ar sauka lafiya.

Lokacin da ta fito, Hana ko bacci ba ta tashi ba, amma ba ta da matsala da wannan, don dama komai na Hana Ummi ce ke yi, muddin Hana na gidan.

Karfe sha daya a medical center ta yi mata, kaf yan’uwanta suna wajen, ita ce kawai babu, sai da ta gaishe su hade da yi masu ya mai jiki, sannan ta shiga dakin da Alhaji yake kwance, ganin yana bacci sai ta fito zuwa barandar ita ma ta zauna.

Duk hirar da suke yi uffan ba ta ce ba, haka ko ruwa bai ga bakinta ba, sai ma ta ji hayaniyar tasu duk ta dame ta, dalilin da ya sanyata matsawa can nesa dasu ta kwanta. Tana kallon yadda ƴan’uwa maza da mata na nesa da na kusa suke ta tururuwa zuwa duba Alhajin.

Tana sallahr azhar Aunty Sadiya take shaida mata ya tashi a baccin. Don haka tana idar wa ta nufi dakin.

Tun da ta shigo yake kallon ta, ta dauka yana jin jiki sosai, sai ta ga sabanin haka, don da kanshi ya, tashi zaune, hade da fadawa Mama ta ba ta kujera ta zauna.

“Ya jikin Alhaji”

“Akwai sauki sosai Fatima, ai ina ta tambayarki, sai ace min ba ki zo ba.”

Shiru ta yi hade da murmushi.

“Ba ki da kudin mota ko?”

Nan ma murmushin ta yi hade da sadda kanta kasa.

Ya gyara zama sosai, ta yadda ita kawai za ta rika jin me yake fada.

“Ki yi hakuri kin ji, a duk cikin yarana ke kawai nake tausayi, amma in Sha Allah komai zai wuce. Ke dai ki yi ta hakuri, ki rike mijinki hannu biyu-biyu, sannan duk runtsi ki yi kokarin cika burinki kin ji.”

Kai ta daga hade da share hawayen da suka sakko mata, ka’ida ne idan Alhaji zai yi mata irin wannan fadan sai ta yi kuka, zuciyarta ce take karyewa.

” Kin san da za ki yi aure na ba ki saniya ko? “

Kai ta daga alamar eh.

” To ta haihu, yanzu haka ma ciki ne da ita, don haka koda lokacin ni ba ni da halin daukar nauyin karatunki saboda yau da gobe, ki sayar da dan da ta haifa sha Allah zai kusa gama miki hidimar karatunki. “

Kai ta kuma dagawa alamar gamsuwa, har zuwa lokacin kuka take yi.

” Ina amarya ta?”

” Tana gida wurin Ummi ” ta fada a hankali.

Sai ya yi murmushi sannan ya ce” Da alama zan sake ta, tun da ba ta iya zuwa jinya ba”

Duk da hawayen da ke bin fuskarta, hakan bai hana ta murmusawa ba

“Ki zama mai juriya kin ji, bawan da Allah ya damu da shi, shi yake jarabawa.”

Nan ma kan ta kuma dagawa.

Shigowar yan dubiya har da Zainab shi ya sanya ta tashi zuwa waje.

Bayan Zainab din ta fito suka dan kebe.

“Kwana za ki yi?”

“A’a zan bi Ya Bashir na baro gida ba kowa.”

“Ikon Allah! Su Goggo Fati an zama manya, har an fara cewa an bar gida ba kowa, ashe zan ga wannan ranar”
Zainab ta fada rike da haba.

Duka Fatiman ta kai mata kafin ta ce “To yi min wulakanci, ke ma ai saura kadan.”

“Allah duk kin canja, kin wani zama mai hankali.”

“Ashe da hauka nake yi.”

“To kadan ya hana.”

Duka ta kuma kai wa Zainab din, suna dariya a tare.

“Na taya ki murna da samun aiki, saura mu.”cewar Fatima.

” Na gode. Ke ma ina yi miki fatan alkairi “

” Na gode. “

Labarin yaushe gamo suke yi, kafin Aunty Hauwa ta kira Fatiman a kan zasu tafi.

Sai da ta kuma komawa dakin Alhaji ta yi mishi sallama, shi kuma ya rika jaddada mata tai ta hakuri.

Dalilin da yasa su Aunty Lami fadin wai sai Fatima kawai ya damu da ita.

Shi kuma ya fada masu ta fisu rauni ne a wannan lokacin.

Kayan kwalam Zainab ta bayar a kaiwa Hana da kayan kitso hade da takalma kafa biyu masu kyau.

A mota ma su Aunty Hauwa ne kawai ke hirarsu, ita dai sai ta mayar da hankalinta a kallon hanya kamar wacce aka ce ta kirga yawan bishiyoyin da suke wucewa.

Fadin gajiyar da ta yi ma bata lokaci ne, tamkar a kasa ta je, ta kuma dawo a kasa.

Da kyar ta yi sallahr isha’i, a kan sallayar bacci ya dauke ta, ko jiran kiran Mustapha ba ta yi ba.

<< Daga Karshe 25Daga Karshe 27 >>

3 thoughts on “Daga Karshe 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.