Bayan Watanni
Lahadi 5:00PM
Duk hayaniyar da yaran ke yi da kuma iyayensu Mama na jin su, uffan ba ta ce ba.
Sosai ranta bace yake a kan abin da yake shirin faruwa.
Kan dole ta yi mubaya'a ba don tana so ba, amma Jamilu da auran ba'indiya, ko mafarkinta bai taba kawo mata wannan ba.
Duk wata hidima da ake yi, Aunty Hauwa ce ke yi, ko yanzun ma ita ta yo gayyar ƴan'uwanta don tarar Jamil din da kuma ba'indiyar shi, da suke isowa yau domin daura masu aure ranar Juma. . .