Skip to content
Part 32 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Bayan Watanni

Lahadi 5:00PM

Duk hayaniyar da yaran ke yi da kuma iyayensu Mama na jin su, uffan ba ta ce ba.

Sosai ranta bace yake a kan abin da yake shirin faruwa.

Kan dole ta yi mubaya’a ba don tana so ba, amma Jamilu da auran ba’indiya, ko mafarkinta bai taba kawo mata wannan ba.

Duk wata hidima da ake yi, Aunty Hauwa ce ke yi, ko yanzun ma ita ta yo gayyar ƴan’uwanta don tarar Jamil din da kuma ba’indiyar shi, da suke isowa yau domin daura masu aure ranar Juma’a.

Fatima ce kawai da zuriyarta babu, ita ma kuma suna hidimar karbar kayan lefen Ummi ne da iyayen Aminu zasu kawo.

Koda yake a bangaren Fatima sara ne aka yi a kan gaba, ba ta san me ya sa ba, amma haka nan ba ta jin za ta zo ta zauna, zaman jiran isowar Jamil da matar da zai aura.

Rashin sanin dalilin hakan ne ma ya sa ta hana Hana zuwa, bare kuma Ziyad da yanzu ma yake koyon tafiya.

Duk wani ma abu da ake na bikin Jamil din ba ta taba cewa komai ba. Anko ma Aunty Lami ce ta yi mata.

Misalin karfe biyu aka kawo lefen Ummi, tabbas Aminu ya yi rawar gani, bai basu kunya ba, sai dai su yi fatan Allah Ya sa suma su fita kunyarsa.

Gidan Fatima bai tsagaita da mutane ba sai magariba.

Zuwa lokacin kuwa ta gaji tubus, sai Ummi ce ta ci gaba da tattare gidan.

Tana kan sallaya bayan ta idar da sallahr isha’i Mustapha ya shigo.

Ziyad ya fara dauka da yake kwance gaba Fatima yana rigima “Me ya same shi?”

“Haka nan kawai.”

“Ba wani nan, ke dai kawai kin hana shi abincin shi” cewar Mustapha a lokacin da yake zama gefen gado yana ci gaba da lallashin Ziyad.

Shiru Fatima ta yi ba ta amsa ba, har zuwa lokacin da ya kuma cewa “Wai me ye damuwarki ne, da za ki rika hana yaro shan nono.”

Ganin yadda ya karasa maganar rai a bace ne ta ce “Abban Hana ba za ka gane ya nake ji ba, wlh yadda ka san yaron nan yana sukar jinina haka nake ji. Ni na fara tunanin yaye shi ma”

“Duka yaron watanshi nawa da za ki yaye shi?”

“Sha biyar.” ta amsa bayan ta kawar da idonta daga kallon fuskarshi da ta kicin-kicin.

“Sai ki yaye mu gani”

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, amma ta mika hannu zuwa wurin Ziyad wanda dama hakan yake jira.

Shiru ya ratsa dakin har zuwa lokacin da Hana ta shigo. Suka ci gaba da surutu da Abbanta.

Daga karshe ma suka koma falo inda ta shirya mishi abincin dare.

Sai da Ziyad ya yi bacci, sannan ta dawo falon, a lokacin ma Hana kokarin yin baccin take yi.

“Ba ki da lafiya ne?” ya tambaye ta, ganin yanayin ta kamar ba mai lafiyar ba.

A gajiye ta ce “Ga ni nan dai, kawai dai na gaji ne” ta karasa maganar hade da zama kan kujera

Cike da kulawa ya ce “Za ki gaji kam, don kin yi kokari sosai, Allah Ya, saka miki da alkairi. Na gode miki, na kuma godewa Allah da Ya ba ni ke a matsayin mata. Fatana a kullum Ya ba ni abin da zan yi maku.”

“Amin.” ta amsa a hankali.

Ya ɗora da “Jamil fa ya iso”

“Sannun shi da isowa.”

Yadda ta amsa cikin halin ko in kula sai ya murmusa

“Har yanzu kuna fadan ne?”

Ita ma murmushin ta yi “Ko kadan.”

“Yaushe za ka je Abuja interview din?” Ta canja hirar tasu.

“kila in tafi talata, na san dai sha Allah ba zan kai juma’a ba. Idan na dawo aka yo bikin Jamilu, Lahadi sai in wuce Enugu, mu je mu karkare in dawo gida, don dama na gaji da Enugun nan.”

“To Allah duk ya amince, Allah kuma ya sa a dace.”

“Amin” shi ma ya amsa lokaci daya kuma ya mike yana fada mata ta kira Ummi ta dauki Hana tun da ta yi bacci. Shi zai dan watsa ruwa.

Maimakon ta kira Ummi din kamar yadda ya bukata, sai ta kinkimi Hanan zuwa dakin Ummin. A lokacin Ummi karatun novel take yi.

Fatima karbi novel din hade da karanta sunan bayan ta kwantar da Hana.

“Wanene Sanadi” ta kara maimaita sunan a, zahiri.

“idan kin gama ina so.”

Kai Ummi ta daga hade da karbar littafin daga hannun ta. “Aunty Zulaihat Kagara ta iya novel sosai.”

“Hada da Aunty Fauza” cewar Fatima lokacin da take mikewa zuwa kofa.

Lokacin da ta shiga dakin, Mustapha shirin bacci yake yi, ita ma, sai ta wuce toilet don watsa ruwa.

*****

Laraba 4:00PM

Sai da ta gama kammala komai hade da gyara ko ina na gidan, kafin ta saka dogon light onion color din hijab din ta, da ya sha guga.

Ziyad ta dora kan kujera hade da sanya masa takalmansa masu igiya (kitos) bakake masu kyau.

Rike da hannunsa ta fito gidan bayan ta karanta addu’ar fita.

Ji take ina ma ba a sandamu take aure ba, tabbas da ba ta zo bikin Jamil ba, amma yanzu kam dolenta ta je.

Ta so sai ranar daurin aure, amma kuma Mustapha ya ce dole ta je wurin dinner da ake yi yau, ya jaddada mata hakan kamar karatun hadda kafin ya tafi Abuja dazu.

Tun daga kofar gida ta fahimci ashe abun Azeemun ne, kofar gidansu da na hakimi cike yake da mutane, maza da mata manya da yara, ko wanne cikin kwalliya.

Lokacin da ta shiga gidan ma ba kowa ne ya lura da zuwan ta ba, saboda mutane, shi ya sa kawai ta zarce dakin Mama.

Ta yi sa a kuwa Maman ce kadai a cikin bedroom, da alama wani abu take nema.

Jin alamun an shigo ne ya sanya ta saurin juyowa, ganin Fatima sai ta hade fuska hade da ci gaba da abin da take yi.

“Ina wuni Mama?”

“Ban sani ba.” A fada ce Mama ta amsa, kafin ta juyo sosai hade da nuna Fatima da yatsa.

“ki fita idona in rufe, wato ke sai yau kike zuwa ko? Ace tun zuwan yaron nan ga baki ga hanci amma ba ki zo gidan nan ba sai yau?”

Zumbura baki ta yi kafin ta ce “Mama ni ma fa kin san hidima muke yi a gidanmu.”

“To sannu Amara! Bakin hali ne dai kar ki daina, haka kawai kin dauki kiyayya kin dorawa bawan Allah, bai ci miki ba, bai sha miki ba.”

Shiru Fatima ta yi, hakan ya sa Mama ci gaba “Shi kuma da yake bai san me son shi ba, ya bi ya damu da lamarinki, tun da ya zo yake tambayar ki.”

Tabe baki ta yi, irin ko jikkntan nan, abin da ya kara tunzura Mama ta ce

“Dan halak dai ba mance alkairi. Ko iya yadda ya tsaya a kanki lokacin da ba ki da lafiya ya ci ace ke din nan kin yi mishi kara, tare da boye kiyayyar da kike masa.”

“Mama!”, Fatima ta kira ta cikin muryar Kosawa da fadan da take mata

“Har yanzu dai kina nan a kan Ya Jamil, amma idan ba haka ba me na yi fisabilillahi?”

Cike da haushi Mama ta jefa mata wata jaka, “ga shi nan, duk da abun arziƙi bai gaji kare ba”

A hankali ta ce “Yaushe ma na gama da gorin yi min magani ake yi”

“Me kika ce?”

Sai da tura baki sannan ta ce “Ba komai”

Wani marfin kwano Mama ta dauka hade jefo ma tashi, cikin sa a kuwa ta same ta a hannu, saboda yadda ta kare dukan.

Da sauri ta mike da zummar yin waje, suka ci karo da Aunty Lami da ta shigo.

Hakan ya sa Fatima dakatawa fuska a kyabe

“Mi ya hwaru kuma?”

Daga Fatima har Mama babu wanda ya amsa, sai huci kowa ke yi

Har sai da ta kara maimaita tambayar, sannan cike da zafi Mama ta ce “Kin wannan yarinyar (ta nuna Fatima da ya tsa) wato ba na jin za ta yi hankali. Tun da an ce idan mace ta haihu ba ta yi hankali ba, to ba za ta yi ba. Yanzu ace yarinyar tun Lahadi da dan’uwanta ya iso gidan nan ba ta leko ba sai yau, yau din ma yanzu. Kuma ta zo tana min rashin kunya don ubanta. Ni kawai ta tafi ma ban so, tun da ita ma gidanta hidima ake yi, ai ba tun yau ba na san Mustapha ya fi Jamilu, tun da kiri-kiri ta zabe shi a kan Jamilun.”

Cikin kwantar da murya Aunty Lami ta ce” Kayya! Mama kin san wacece Fatima, don Allah ki rika hakuri kawai kina mata addu’a, tun da haka Allah ya ba ki ita.”

Kwafa Mama ta yi, cike da takaici ta kuma cewa” Kin ga fa kaya ne yaron ya siyowa Hana da Ziyad, amma sai cewa ta yi, wai ta amsa a yi mata gori, to Uban waye zai mata Gorin? “

Aunty Lami ta juya wurin Fatima alamun neman karin bayani.

Cikin kuka Fatima ta ce” Aunty Mama idan dai a kan Ya Jamil ne, to ni dai ban taba yin daidai ba, komai na yi sai ta ce dai ba haka ba. Yanzu don Ya Jamil ya yi min magani don ban da lafiya, ina ba laifi ba ne.”

“Ki ba ta hakuri da Allah, tun da kuma kin san ya take a kan Jamil din ki rika kiyayewa mana.”

Mama dai tuni ta fita zuwa falo, cike da haushin Fatima.

Aunty Lami ta kuma gyara tsayuwarta, cikin muryar nasiha ta ce “Fatima Mama mahaihiyarki ce, bai kamata tana hwada kina hwada ba. Idan da kuruciya ce yanzu kuma ya zama hauka, ke ma haihuwa kike baza ki so a yi miki yadda kike mata ba. Ki daina kin ji.”

Cikin shesshekar kuka ta ce “Aunty raina yana matukar kuna idan na ga ko wane lokaci a kan Ya Jamil ne Mama ke min fada, kuma ban san me ya sa ta fi jin zafina fiye da kowa a kan Ya Jamil. Yanzu idan da shi ne ake sabgata bai zo ba, wlh ba ta fara mishi da fada, karshe ma kare shi za ta rika yi, ta ce bai yi laifi ba. Yanzu wadancan kayan idan na karɓa, ku san ko wane lokaci idan na yi ba daidai ba Mama sai ta ce nan har abu kaza, ya siya min amma ga shi nan ina yin kaza.”

“Ikon Allah! To wannan abu kam ko kishi ne? To je ki dai ki ba ta hakuri, ki wuce gidan hakimi ana dinner.”

Kai ta daga alamar to, a daidai lokacin Mama ta kuma shigo rike da Ziyad da yake kukan neman uwarshi.

Yana ganin Fatiman kuwa sai ya kwace ya nufi wajen ta.

“Mama! “

Fatima ta kira sunan a hankali.

Kin amsawa ta yi kamar yadda ba ta kalle ta ba.

“Ayyah Mama! Don Allah ki yi hakuri, ke ce sai ki yi ta nuna kin fi son Ya Jamil a kaina.”

“Ki yi hakuri don Allah Mama” Aunty Lami ma ta fada cike da rarrashi.

“Na yi” cewar Mama cikin nuna rashin muhimmantar da abun.

“Mama don Allah ki yi hakuri, ke ce fa idon gani na. Da gaske ba na son kina fifita Ya Jamil a kaina. Amma tun da na fahimci kin for son shi, sha Allah ba zan sake damuwa ba.”

“Ni duk ina sonku.”

“Amma ba kamar shi ba.”

“Idan ma hakan ne ai na fada miki dalilina”

“To kin ji ko Aunty Lami”

Dariya Aunty Lami ta yi hade da ficewa daga dakin, sai a lokacin Mama ta ce “Ina Hana din?

“Suna islamiya, na ce idan an tashi su taho nan.”

Shigowar Aunty Ayyo da Aunty Sadiya ya, San ya su yin shiru, sama-sama suka gaisa, suka janye Fatiman zuwa gidan Hakami.

Matar J✍🏻

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 31Daga Karshe 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×