Skip to content
Part 31 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Sai da Mustapha ya yi sati biyu, sannan ya yi shirin komawa Enugu, ba Fatima ba, hatta Ziyad da yana da bakin magana tabbas da ya fadi cewa ya yi kewar Babanshi.

Mustapha mutum ne da idan har ka saba da shi, tabbas ka rasa shi tsawon wuni guda za ka ji ba dadi, shi ya sa a can ma Blessing sosai ta yi kewarsa, ranar da zai dawo sai ta ji kamar ranar Christmas din ta.

Tarba ta musamman ta shirya mishi da abinci masu dadi, wanda ta bata lokaci wajen girkawa.

Shi kansa sai ya ji duk wata kewar da ya taho da ita daga gida ta ragu da kaso talatin.

Bai taba gani matar da ba ta jin kiwar girki ba kamar Blessing, ita abinci baya mata wahala, idan dai ba ta yi ba to babu ne.

Ta iya kalolin abinci, da miya masu yawa, tun bai iya cin wani abun ba,, har ta koya mishi.

Yanzu kam ko me ta kwaɓa ci yake, idan har bai sabawa addini ba.

Safiyar lahadi da misalin karfe 9am ta shigo dakin, rungume da Bible cikin Kwalliya alamun daga church take. Don tun 7am take tafiya.

A lokacin Mustapha kwance yake suna musayar text message shi da Fatima, shi ya sa lokacin da yake amsa gaisuwar ta hankalinsa baya kanta.

Dalilin da ya sanyata zama a inda ta saba zama tana kallon sa.

Sai da ya gama tura sakon sannan ya juyo gare ta, yau shigar atamfa ta yi riga da siket sosai sun karbe ta, abu daya ne kawai yake hana masa ganin kyawon kwalliyarta, kitson attach din da take yi ko ta sanya kuma shi ne yake dakushe mata kyawonta a idanunsa. Sosai yake jin haushin abun, kawai dai yana dannewa ne, saboda ya san zaman na dan lokaci ne.

“I have a message for you?” ta yi maganar idanuwanta a kansa.

“Guess what?” ta kuma fada hade murmushi.

Ya yi dan shiru kafin ya ce “Na ba ki gari”

“So close your eyes”

Ya dan bata rai kadan “Please keep joke aside, just tell me”

Marairacewa ta yi “Please do it as i said please”

Ya lumshe matsakaitan idanuwansa, zuwa lokacin da ta ce “Open it”

Ya zubawa yar karamar jakar da ke hannunta ido, bayan ya bude idanun nasa.

“Guess from who?”

“From you.” ya ba ta amsa

Murmushi ta yi kafin ta ce “Is not from me, is from my sister Husaina.”

Ya yi saurin zaro ido alamun mamaki, lokaci daya kuma ya mika hannu ya karbi jakar,”Wowwww!” ya rika fada a lokacin da yake fito da abubuwan da ke cikin jakar.

Turare ne na maza masu kyau guda biyu, sai agogon hannu mai kyau na maza. A kalla ya tasar ma 10k, a lokacin kuwa 10k ba karamin kudi ba.

“kin je Maiduguri ne?”

“A’a, a Abuja muka hadu wurin Dady.”

“Na gode, don Allah ki taya ni godiya a gare ta. Amma wadannan kayan ai sun yi yawa, almost 20k+ fa”

“Ta ga za ta iya ne, ta ce kana da kirki, you’re very nice in ji ta.”

Suka yi dariya a tare lokacin da take kai karshen maganar.

Shi kansa Husaina na daya daga cikin matan da suka kwanta mishi, da ace zai kara aure, kuma kudinshi sun kai, to tabbas da ya jaraba sa’arshi a wurin Husaina. She’s very gentle and simplicity.

Shi ma hotunan guda hudu ya mika mata cikin envelope, hoto na farko Hana ce kadai, cikin shigar fara kal din riga yar kanti mai siririn hannu, an kame kanta da farin ribon da yarfin jar fulawa, kafarta ma cover shoe ne na mata fari mai kyau, shi ma akwai digon jar fulawa a sama.

Ta Yi kyau sosai, Blessing ta zubawa hoton ido hede murmushi kafin ta dago tare da fadin “She’s very – very beautiful than you, duk da tana kama da kai.”

Har cikin ransa ya ji dadin yabawar da ta yi wa Hana.

Yanzu kuwa Ziyad take kallo, dan lukuti cike da koshin lafiya, sanye da Light blue din riga yar kanti mai taushi da kuma blue black din wando, kafarsa sanye da takalma masu kyau na yara, yayin da ya tura hannunsa da ya dunkule cikin baki.

“Wannan kam is your photocopy”

“Really?” ya yi saurin tambaya cike da fara’a

“Ehen now” cewar Blessing tana kara duba hotunan.

“You love your wife so much, please help me with your love story” wannan lokacin matsakaitan idanuwanta ta zuba a kanshi.

Ya kuma kawata fuskarshi da murmushi kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya ce “Me ya sa kike son ji”

“just” ta ba shi amsa har zuwa lokacin ba ta janye idanunta a kan fuskarshi ba.

“Fatima ta yi min halacci ne kawai, ta aure ni a lokacin da ba ni da komai, kuma take zama da ni har yanzu da ban da komai. Amma kar ki yi tunanin mun yi wata soyayya ne, babu wannan tsakaninmu. Sai dai yanzu ina sonta fiye da yadda duk zan kwatanta miki.”

Zamanta ta gyara da fuskantarshi sosai” Ba kamar kan aiki ba? “

“Ina yi, primary teacher kam a wannan tafiyar ai sai a hankali. Musamman ni da nake da dawainiya a gabana, ina da kanwa fa, kuma bana zan aurar da ita, ta yi candy tun last year.”

Kallon sa kawai take yi, karon farko da ya taba fada mata wani abu daga rayuwarsa.

“Kana son aiki a Abuja? “

Yadda ta yi maganar babu alamun wasa, shi ya sa ya ce” zan yi farin ciki sosai da hakan. “

“Za ka iya nisa da Maman Hana kenan? ” wannan karon da alamun tsokana ta yi maganar.

Bai ba ta amsa ba, illa siririyar dariyar da ya yi.

“I’m serious, idan kana so zamu jaraba”

“Ina so mana”

“Just give me time”

Ta fada hade da mikewa.

Ya bi bayan ta da kallo har ta fice daga dakin.

Sai a lokacin yake ganin kamar ya yi wawanci da har ya fada mata wani abu da ya shafe shi.

Yana mamakin yadda yake sakin jiki da Blessing a duk lokacin da suke tare.

Lokuta da dama sai bayan sun rabu ne, yake ganin rashin dacewar wani abun a tare dasu.

Kamar shigowarta dakinsa, akwai da yawa da suka yi masa magana a kan hakan, amma ya kasa dakatar da ita, duk da ya san ba abu ne mai kyau ba ta bangaren addininsa da al’adarsa.

Abin da wasu basu sani ba game da Blessing, tana da taka – tsan-tsan, hade da kiyaye duk wani abu da ta san addinin is kama bai yadda da shi ba. Koda wasa ba ta taba wajen litattafan addininsa, haka wurin da ya ware don yin sallah.

Abin da ya fi burge sh da ita shi ne yadda take kiyaye mishi lokacin sallah. Ko bacci yake idan lokacin sallah ya yi ba ta kasa a gwiwa wajen tashin shi. Idan haka ake rayuwa tsakanin mabambanta addini tabbas da babu wani abu da zai kawo tashin hankali ko bangaranci.

Da wannan tunani ya mike don yin kwalema a dakin nashi.

******

Bangaren Fatima kuwa, komai yana tafiyar masu kamar dai ko wane lokaci idan Mustaphan baya nan.

Suna rayuwarsu cikin kula da juna ita da Ummi, kullum kara shakuwa da kuma kaunar juna suke yi, sosai Fatima ke jin dadin rayuwarta da Ummi, musamman yadda take kula da yaran, sunan kawai Fatima ta haife su ne, amma da yawan dawainiyarsu Ummi ce. Ba ita kadai ce ke jin dadin zaman nasu ba, ita kan ta Ummi tana alfahari da Ita, saboda ta hana mata kukan maraici, duk wani abu da uwa kan yi wa ƴa to Fatima na bakin kokarinta, komai ta samu na Ummi ne.

Yanzu haka ma dakin Ummi suke, Fatima zaune a gefen katifa rungume da Ziyad da yake fama da zazzabi.

Ummi kuma doguwar riga take dinkawa Hana da wasu ragowar kyallaye. Kasancewar yanzu hannunta ya fada.

Wayar Fatima ta yi kara Ummi ta mika mata, idonta a kan lambar da ke yawo a kan screen din, ba Ummi kadai ba, ita kan ta Fatima bin lambar ta yi da kallo, saboda ba ta saba ganin irin ta ba.

A tsorace ta daga, ga mamakinta sai ta ji muryar Jamil.

Gabanta ya yi wata irin faduwa, yayin da bakinta ya rufe kamar an sanya mata gum.

“Ba kya ji ne?” ya kuma ambata karo na ba adadi.

Ta janye idonta a kan Ummi wacce suke kallon kuda tun lokacin da ta daga kiran. Cikin yayyakewar murya ta ce “Ina ji yanzu”

Gajeruwar gaisuwa ta biyo baya kafin ya ce,

“Akwai wata matsalar ne?”

Cikin sauri ta ce “a’a”

Ya dan yi shiru kafin ya ce “Ki je wurin Aunty Hauwa ki karbi sako.”

Cikin sansanyar murya ta ce “To na gode, Allah Ya saka da alkairi.”

Maimakon ya amsa sai ya ce “A siyawa Hana duk abin da take so.”

Duk da baya kallon ta sai da ta dan murmusa, amma ba ta ce komai ba.

Shi ma bai damu da cewarta ba ya yanke wayar.

“Waye?” Ummi ta yi saurin tambaya

“Ya Jamil, kin ga Allah GafururrRahim ko Ummi, kila na samu kudin kai Ziyad asibiti. Bari in je gidan Aunty Hauwa yanzu, don ba zama wai an saci dan ɓarawo.”

Dariya kawai Ummi ta yi, sannan ta juya kan dinkinta.

Can kasan zuciyarta kuma wani so da kaunar Fatima na kara cika kirjinta.

Yayanta ya yi sa’ar mata, irin Fatima ake cewa matar rufin asiri, tun jiya Ziyad ke fama da zazzabi amma ta ki fadawa Mustapha, wai kar a daga mishi hankali kuma ta san bai da kudi.

Sai paracetamol na kwaya take ta jikawa tana dura mishi, ya yi amai har ya shiga uku.

Maganar Fatiman ce ta katse mata tunaninta.

“Wai har kin shirya?”

“To me zan jira?” Fatima ta amsa mata ta hanyar tambayarta ita ma

“Ashe ciwon ya dame miki har haka dama?”

Harara ta aika mata da ita kafin ta ce “Bai dame ni ba. Idan Aminun ya zo ki gaishe shi.”

“Zai ji.” Cikin dariya Ummi ta yi maganar, a lokacin Fatima ta kai soro.

<< Daga Karshe 30Daga Karshe 32 >>

1 thought on “Daga Karshe 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×