Skip to content
Part 33 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Lokacin da suka shiga falon Aunty Hauwa cike yake da yan’uwa, ana yi wa amarya kwalliya, can wajen gidan kuwa kida ne ke tashi tare da hayaniyar mutane.

Kallo daya za ka yi wa Aliyana wacce ta koma Aliya a yanzu ka fahimci ita din kyakkyawa ce, doguwa ce mai dan jiki, kyakkyawan gashinta ya sauka har tsakiyar bayanta, yadda ya sirka da ja, sai ya karawa kyakkyawar zagayayyar fuskarta kyau.

Shadda ce a jikinta coffee color, kalar da ta haska farar fatar ta, da dankwalin shaddar ake nada mata goggoro, sai ta fito sosai ta yi kyau duk da kallo daya za ka yi mata ka fahimci kayan hayensu ta yi.

Fatima dai wuri ta samu ta zauna, tana kallon yadda ake ta gyare amaryar da kuma surutan mutane.

Ita kanta amaryar lokaci zuwa lokaci ta kan jefa kwayoyin idonta a kan Fatima, don yau ta fara ganinta, kuma sosai take kama da yan gidan su Jamil din, duk da hasken fatarta.

Sai misalin karfe biyar aka fito da amarya zuwa wurin da dinner.

Sosai Jamil ya yi kyau, shi ma a cikin shadda irin ta amaryar.

Karon farko da jikin Fatima ya saki, ta rika jin wani abu mara dadi a can kasan zuciyarta.

Musamman idan ta kalli yadda yake ta washe baki cikin ƴan’uwa alamun yana cikin farin ciki.

Misalin 6pm wurin ya ka came, hatta Fatima tuni ta sake, rawarta kawai take kwasa, abin da ya rika ba Jamil mamaki, zai iya rantsuwa a wurin babu wanda ya yi rawarta.

Shi ma sai ya rika jin ba dadi, ga ni yake dai kamar dai ba ta taba jin son shi ba, kamar yadda take fada din, nishadin da take ciki kadai, ya isa ya bayyanar masa da hakan.

Karfe takwas na dare aka tashi daga dinnern, kowa cike da farin ciki.

Fatima kam ba ta koma gida ba, sai 10pm, wata irin gajiya take ji kamar dai ta yi dambe da wasu katti, da kyar take daga kafarta tana ajiyewa.

Wanshekare ma da ta dawo haka nan dai ta wuni a gidan amma ba ta jin dadi, ko ina jikinta ciwo yake.

A ranar kuma Mustapha ya dawo dauke da babban albishir din cewa ya samu aiki, a matsayin registerer a wata court da ke Abuja. Har sun tabbatar mishi da idan har komai ya kammala zasu ba shi karamin gida da zai zauna.

Ba Fatima kadai ba, duk wani masoyinta ya taya ta murna da jin wannan labarin.

Labarin ma na daya daga cikin abin ya kori kaso hamsin cikin yawan gajiyar da take fama da ita.

Ranar Juma’a dubban mutane suka shaida daurin auran Jamil da Kuma Aliya a babban masallacin juma’ar garin.

Duk yadda Jamilu yake daukar abun nothing serious, sai ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki da annashuwa.

Kallo daya za ka mishi ka shaida hakan.

Bangaren Alhaji Musa aka gyarewa amarya, irin dakan daka shikar daka, tankaden bakin gadon nan. Fatamu kawai Allah Ya ba amarya da ango zaman lafiya

*******

Bayan bikin Jamil da sati daya Mustapha ya wuce Abuja domin kama aikinsa.

Ba Wannan ne lokaci na farko da Mustapha ke tafiya ya bar su ba, amma a wannan karon sai ta fi jin damuwa, da kuma yawan faduwar gaba, sosai take jin kamar dai za ta rasa wani abu, ko wani abu mara dadi zai faru da ita.

Haka nan take yawo, amma komai haushi yake ba ta. Ga ciwon jiki da kullum gaba yake ya kwaryar roro.

Yau Monday misalin karfe goma na safe suka fito gidan tare da Ummi.

Ummi dauke da Ziyad yayin da Fatima ke ta ka kafarta da kyar kamar wacce ta yi tsallen kwado. Tafe suke suna hira, da yawan hirar dai a kan Mustapha ne sai kuma auran Ummi da bai wuce wata biyu ba.

Ummi wucewa ta yi gidan Aunty Ayyo ita da Ziyad, yayin da Fatima ta wuce gida.

Dama ta san ba lallai ta samu mutane a gidan ba, ilai kuwa sai Zainab kadai da take kwance kan tabarma a kofar daki tana sana’arta (karatun novel)

Sallamar Fatima ta sanya ta tashi zaune hade da amsa sallamar.

Cikin alamun gajiya ta zauna a kusa da Zainab din tana fadin “Ashe dai da gaske kin zo?”

“Yo ba dole ba, tun da ban zo biki ba jarabawa ta hana, ai dole in zo in ga zaman amarya da ango.”

Tabe baki Fatima ta yi kafin ta ce “To sannu uwarsu.”

Dariya Zainab ta saki sannan ta ce “Ina Hana?”

Kamar Fatima ba za ta amsa ta ba, sai kuma ta ce “Tana school. Ya exam din?”

“Alhamdulillahi! Finally dai na gama.”

“Na taya ki murna sosai. Allah Ya ciyar damu muma”

“To amin. Amma yanzu wane maganar makaranta Goggo Fati?”

Tana shirin ba ta amsa sawun takun fitowar su Jamil ya hana ta.

Dalilin da ya sanya su mayar da hankalinsu wajen.

Jamil dai sanye yake da t-shirt din jar riga da bakin wando, yayin da Aliya ta nade jikinta da sari, sosai ta yi kyau, musamman yadda ta gyara gashinta mai sirkin ja.

Fatima ce ta fara dauke kai daga kallonsu, yayin da kirjinta ke wani irin bugu.

Shi ma Jamil din zare hannunsa ya yi daga cikin na Aliya, tun da ya zo yau ne karon farko da suka hada ido.

Duk lokacin da ya ganta wani irin abu yake ji mai wahalar fassarawa.

Tabbas da ace mace na auran Maza biyu a lokaci daya, da a wannan karon ko min runtsi, sai ya tabbatar ya same ta.

Zainab ce kawai ta gaishe shi, sabanin Fatima da ta kwanta sosai a kan tabarmar, tana sauraron yadda Zainab ke gaisawa da Aliya cikin harshen turanci.

Shigewarsu dakin Mama ya sanya zainab ɗakawa Fatima duka a cinya “Wai kishi kike yi?”

Sosai maganar ta bata ranta, don haka a harzuke ta ce “Idan ban yi miki zagin Aunty Lami ba, Zainab ki ce ba ni ba ce.”

“To na ga ko gaisuwa ba ki kwasa ba.”

A harzuke ta kuma cewa “To fadarsu na je, nan fa gidan ubana ne.”

Cikin dariya Zainab ta ce “A bar hali a ci me Goggo Fati?”

“Dalla ma za ki dame ni, ni turanci na iya.”

Dariya Zainab ta kuma yi tare da fadin “Wai Ziyad fa?”

“Yana tare da Ummi”

“An kusa bikinta ko?”

“Sha Allah nan da wata biyu.”

“To Allah Ya kai mu.”

Fitowar Mama ya sa Fatima ba ta amsa ba, illa mika gaisuwarta da ta yi

Ta amsa tana tambayarta ya jikin

Fuskar Fatima ta dan canja kadan alamun rashin jin dadi “Har yanzu Mama, wlh da kyar nake daga kafafun.”

“Anya kuwa ba rawa kika yi a kan aljanu ba?” cewar Mama tana kallon Fatima.

Cikin dariya Zainab ta ce “Kai Mama.”

A lokacin Jamil ya fito, idanuwansa a kan kafafun Fatima da suke fari tas, kasancewar sauran jikinta ya fi fuskarta fari.

“Me ya samu kafar?” ya yi tambayar yana kallon Mama.

“Wai ciwo suke mata, tun ranar fa da aka yi dinnerr bikinku.”

“Ta sha magani?”

“Kin sha magani?” Mama ta mayar da tambayar a kan Fatima.

“Na sha.”

Bai ce komai ba ya nufi kofar fita.

A daidai lokacin ne kuma Aliya ita ma ta fito, sosai take son yin hira da Fatima amma babu fuskar yin hakan daga Fatiman.

Idan tana wurin duk sai ta ji ma ta tsargu.

Gefen tabarmar ta zauna a darare, tana sauraron maganar da Mama ke yi da Fatima duk da ba jin me suke fada take yi ba.

Hirar tasu ta fi armashi d Zainab, don Fatima uffan ba ta ce ba, sai ma ta tafi gidan Aunty Hauwa.

Dama Mama tsakaninta da Aliya sai maganar kurame, shi ya sa ma basu faye zama na tsawon lokaci ba, don mama ta dosa korafin ita fa ta gaji da nuni, ba za ta iya ba.

Shi ya sa bayan wata daya da biki Jamil ya tasa ba’indiyarshi suka koma kasarsu

*******

Wasa-wasa jikin Fatima ya ki dadi, dole Mustapha ya dawo gida, sun je asibiti har scanning an yi, amma ba a ga komai a kafarta ba, ga shi kuma kullum ciwa gaba yake ba baya ba.

Yanzu kam hatta zaman gidan sai ta ce ba ta so, wai ta fi son ta dan fita waje ko a kai ta gida.

Gida take zuwa ta wuni sai dare Mustapha yake zuwa su tafi gida, amma a daddafe take kai safiya, wani lokaci ko karyawa a gidan Mama take yin ta.

Karshe dai dole Mustapha ya hakura ta koma gida, Mama ta ce maganin gargajiya za a nemar mata, wannan kam aikin aljanu ne.

Lokaci daya Fatima ta canja, za ta iya wuni ba tare da ta ce komai ba, Sam ba ta son hayaniya, idan hayaniya ta cika yawa sai ta ji kanta yana juyawa, shi ya sa Mama ba ta bari yara su taru a gidan kamar da.

Sosai canjin ya damu ƴan’uwanta, an je asibiti amma ko wane gwaji baya nuna wani sakamako.

Hankalin kowa a tashe tun ba Mustapha ba, da duk sati yana hanya ba, kuma idan ya zo sai ta ce wai wari yake mata, wannan ne ya kara tayar da hankalin mutane, suna fadin lallai jifanta aka yi ko kuma dai aljanu ne ke son raba su.

Kan dole aka yaye Ziyad, Ummi ce ke dawainiya da shi a gidan Aunty Hauwa, Hana kam dama ita yar gidan kowa ce.

Yadda Jamil ke jin Mama cikin damuwa kullum a kan ciwon Fatima, shi ma sai ya kasa nutsuwa, dole ya taho gida.

Kasancewar cikin dare ya iso, sai da safe ne ma Fatima ta san ya zo.

A lokacin da ya shigo dakin Koko da kosai take sha, don duk wannan ciwon bai hana ta cin abinci ba, cin abinci take yi kamar ba gobe, shi ya sa Mama kullum tana gaban murhu, asubar farko ta dama mata koko.

Dalilin da ya sa ta murje ta yi fes da ita a zaune. ( To ba ta dagawa bare ta aje) , hatta ruwan wanka kai mata ake yi. Ƴan’uwanta karɓa-karɓa suke yi na jinyanta.

Sam Jamil bai yi tunanin zai ganta haka ba, ya dauka zai same ta fiyau a gado, sai ga ta him ta hada jikinta abun ta.

Ya yi tsaye a kan kofar yana kallon ta, da kuma karantar yanayin jikin nata.

“Sannu da zuwa” ta fada a hankali ba tare da ta dakata daga shan kokon ba.

Kallon ta kawai yake yi, saboda tsawon zaman shi a lokacin bikinshi, bakin ta da na shi basu hadu ba.

Maimakon ya amsa gaisuwar sai ya ce mata “Tashi tsaye”

Sai da ta dan mata lokaci sannan ta tashi da kyar.

“Yi tafiya”

Nan ma da kyar ta rika cira kafafunta tana ajiyewa, har ta kai karshen dakin ta dawo inda take.

Yanzu kam gefen gadon ta zauna, fuska a hade.

“Tun yaushe ba ki ga period dinki ba?”

Ware idanuwanta ta yi a kan fuskarshi,

“Uhum!” ya karfafa maganar tashi hade da dage girarsa du biyun.

“ai ni ba na period idan ina shayarwa” ta amsa tambayar hade turo baki.

“Dakko matafinki mu je asibiti” ya yi maganar lokaci daya kuma ya juya zuwa waje.

Shiru ta yi gabanta na tsananta faduwa, kamar ta ce ba za ta je ba, sai kuma ta kwallawa Mama kira a kan ta zo ta kama ta.

Haka suka lallaba har wurin motar, sai da Fatima ta daidaita sosai sannan Mama ta koma gida.

A can asibiti kuwa da farko jinin Fatima aka fara diba, daga nan suka wuce scanning room, suka shiga wurin likitan kashi, kamar dai kullum ya ce babu wata matsala a kashinta.

Abin da Jamil yake zargi shi ne ya tabbata, wato dai Fatima ciki gare ta har wata biyar, kuma scanning din da aka yi ya nuna ƴan biyu ne.

Matar J✍🏻

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 32Daga Karshe 34 >>

1 thought on “Daga Karshe 33”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×