Skip to content
Part 35 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Koda aka gama hidimar biki Blessing da Husaina gidan Mama suka ci gaba da zama, da yake sai sun yi sati sannan , kenan dai bayan biki da kwana biyar.

Saurin shiga rai na daya daga cikin baiwar da Allah Ya yi wa Blessing , idan dai har za ka yi zaman mintoci da ita sai ka ji ta shiga ranka, ana cewa yawan fara’a kansa mutum ya zama wawa wai, amma Blessing kyau take kara mata, tamkar dai yar kwallon kafar Brazil Geyse Ferreira.

Uwa uba ba girman kai, aikin gidan kaf sun karbe ita da Husaina, kuma da alama sun saba yin hakan dama, saboda akwai bambanci tsakanin wanda ya saba yin abu, da wanda kuma haye ya yi.

Wannan na matukar burge Mama, saboda ko lokacin da Fatima take budurwa aiki sai ta ga dama, tana ma mamakin yadda ta iya abinci a yanzu.

Haka ta sabu da ƴan’awan Fatima, haka nan suke burgeta gasu da yawa amma hakan bai hana sun samu ingantaccen ilmi ba, hadin kansu na burgeta, sai take jin ina ma tana daya daga cikinnsu.

Wani abu da yake kara ba Blessing mamaki shi ne yadda duk suka san yaran ƴan’uwansu, misali idan yaro ya shigo kai tsaye suke fadin sunan shi, kuma sun san yaron waye, a tunanin Blessing sai an rika jajen to wannan yaron waye, ko a rika tunanin ko ya ma sunan shi. saboda yawansu.

Don a kalla Mama na da jikokin sama da hamsin.

Yau Monday, kuma ranar Mustapha ya koma Abuja bayan ya sallami Blessing.

Misalin karfe hudu na yamma Fatima ta shiga gidan hade da sallama, gidan fes, babu wani tarkace, komai an kintsa shi inda ya kamata, a lokacin Blessing ce kawai kwance a kofar dakin Mama tana latsa wayarta. Da yake Husaina na gidan Aunty Ayyo can ta kwana.

Blessing ta mike zaune hade da amsa sallamar lokaci daya kuma gabanta yana luguden faduwar da ya zame mata kamar farilla duk lokacin da ta ji murya ko ta ga Fatiman.

Ta dan fadada murmushinta kadan sannan ta ce “Barka da yamma”

Ita ma ta kuma fadada fara’arta ba tare da ta amsa ba. Kila ba ta san me za ta ce ba.

Mama ta fito sanye da hijabi da alama sallah ta idar.

Gefen tabarmar ta zauna tana amsawa Mama maganar da take mata a kan Ziyad.

Kafin daga bisani ta gaishe ta, Maman ta dora da “Mustapha kuma an tafi?”

“Eh” ta amsa hade da jan bayanta zuwa jikin bango.

“To Allah Ya kiyaye masa hanya.”

“Amin.” ta kuma amsawa.

Sannan suka shiga hirar yanayin biki, hade da tattauna matsalolin da aka fuskanta da hanyar da za a magance ta saboda gaba.

Duk maganar Blessing sauraro kawai take yi, amma ba ta fahimta, sai dai abun yana burgeta, yadda ta ga Mama suna hira da Fatima cikin fahimta kuma a sake.

Blessing ta gama shirya abinci a gaban Fatima, cikin murmushinta ta ce “Momyn Ziyad ki ci abincinmu”

Cikin murmushi ta janye abincin gefe “Sai dai ko zuwa an jima yanzu kam na koshi.”

Ba tare da gazawa ba, Blessing ta kwashe kayan abincin ta mayar kitchen, sannan ta koma dakin Fatima wanda ya zama na ta ita Husaina a yanzu.

Mama ta kalli kofar dakin sannan ta juyo kan Fatima, hankali ta ce” Wai me ya sa kike haka ne? “

Cike da rashin fahimta ita ma ta ce” Me nake yi? “

Sai da Mama ta bata rai sannan ta ce” Sam ba kya mu’amalantar yarinyar nan yadda ya kamata, kuma ko don yadda take girmama ni, take dawainiya da mijinki da yaranki kin rika sake mata”

Hannun Fatima rike da haba alamun mamaki ta ce “To me na yi mata kuma Mama?”

“Kin fi ni sani ai, tun da yarinyar nan ta zo ban taba ganin kun yi magana ko ta minti biyu ba. Sai kina wani dauke mata kai.”

Tabe baki ta yi kafin ta ce “Mama kina da son takalo rigima. To ni wane labari ko magana za mu yi, ban san ta ba ta sanni ba. Kuma akwai wata kyautatawa da ta wuce yadda take zaune gidan ubana, nan fa gidan ubana ne. Sannan ke din uwata ce, kuma kin kyautata mata, aiko na gama mata komai ko ta yarda ko kar ta yarda”

Mama da ta saki baki tana kallon ta, ta rufe bakin tare da fadin “Amma dai kin san wannan ba hali ne mai kyau ba, haka ma fa kika yi wa matar Jamilu, har ta gama zamanta ba na jin ko gaisuwa kun taba yi.”

“To ban iya turanci ba.” Fatima ta amsa kai tsaye “

” Ni na iya ne? “

” Amma ke ai kin iya maganar kurame.”

“Ki dai gyara halinki wlh, ba a san inda rana ke faduwa ba.”
Cewar Mama cikin alamun gargadi.

“Yo Mama rana kam a yamma take kwana, ni fa kawai rayuwata nake yi, yadda kuke ni ba haka nake ba, to me zai sa ace dole sai na yi…”

“Dakata.” Mama ta yi saurin katse ta.

“Tashi ki tafi, ni dama ba wasika na aika miki ki zo ba.”

Babu gaddama kuwa yunkura da kyar ta mike, ba ta ce komai ba ta fice daga gidan. Sai dai a zuciyarta ta ayyana ba ta kara zuwa gidan sai Blessing ta tafi.

Sai dai kuma wanshekare ranar talata Blessing da Husaina suka je gidan Fatiman.

A lokacin zaune take tana ware kayan da ta amso daga gidan wanki.

Ta amsa sallamarsu kamar dai kullum. Daga tsakar gidan har dakin babu inda yake da aibu.

Bayan sun gaisa duk sai suka yi shiru, kamar mintuna biyu Fatiman ta ce “Don Allah Husaina yi hak’uri ki zubo maku abinci a kitchen kin san tashin nawa.”

Duk suka yi murmushi, Husaina ta zubo taliya da sauce din da ta ji albasa hade ice fish.

Sosai abincin ya yi musu dadi, a hankali suke taba hira, wacce ma fi akasarin hirar a kan yadda al’adun Maiduguri suke ne yayin aure.

Sai kuma yadda Blessing ke ta yaba rayuwar Hausawa da kuma yadda al’adunsu ya burgeta.

A tunanin Fatima zasu kwana a gidanta ne amma misalin karfe goma suka koma gidan Mama.

Ita ma dole safiyar Laraba ta yi wa gidan Mama tsinke don ganin tafiyarsu Blee.

Misalin karfe 9am kuwa suka tafi cike da tsarabar da Fatima ba ta san ma ko ta mecece ba.

Ita ma sai yamma ta koma gida.

******

Bayan bikin Ummi da wata uku Fatima ta sako ƴan biyunta duk maza, haihuwar da ta zo mata da alkairai sosai, don ko haihuwar farinta ba ta samu alkairi haka ba.

Kila ko don Mustapha ta fara shigar manyan mutane, sosai ta samu kudi da kayan jirarai daga sabbin abokansa bugun Abuja.

Wannan karon Mamansu Blessing ce ta zo suna, dauke da akwatunanta biyu, daya na Fatima daya kuma na Babies.

Gidan Mama ta sauka, mace mai dattako rikon addini ga kuma kwarjini, sosai Fatima ke girmamata don matar ta cika mata ido.

Suna ya kayatar inda yara suka ci sunan Hassan da Husaini.

Ana gobe Maman Blessing za ta tafi ta zo da wata magana mai girman gaske.

Lokacin da Hakimi ya samu Aunty Hauwa ya sanar mata, kuma ya ce ta sanar da Mama sosai abun ya girgizata.

Maimakon ma ta sanar din kamar yadda Hakimin ya umurta sai ta share maganar tsawon wata guda.

Shi ma Hakimin sai bai kara bi ta kan lamarin ba, musamman yadda ita ma Maman Blee ba ta kara tuntubarsa ba, duk kuwa da ta amshi lambar wayarsa don jin karin bayani daga gare shi.

Bangaren Fatima kuwa rayuwa take cikin farin ciki tare da yaranta, basu rasa komai ba, Mustapha kullum cikin kokarin basu kulawa yake yi, shi ya sa Fatima ta kara canjawa, ga jego ga kuma canjin rayuwa gabadaya

Ƴan biyunta basu da rigima sam, sannan Ziyad yana gidan Mama, Hana kam ta zama yar gidan Aunty Ummi.

Duk bayan sati biyu Mustapha ke zuwa, inda ya fadawa Fatima tana yin arba’in zasu wuce Abuja saboda an ba shi gida.

Ita ma sai ta ji tana son zuwa Abujar karon farko da za ta tafi wani gari bayan Kano da Katsina.

Lokacin da Fatima ta je yawon arba’in gidajen ƴan’awanta, sun yaba canjin da suka gani daga gare ta, don sosai ta canja, alamun jin dadi duk sun bayyana a jikinta.

Yaranta ma tubarakhallah sun yi kubul-kubul kamar ba ƴan biyu ba.

A lokacin da Fatima ke ta shirye-shiryen bin mijinta, a lokacin ne Aunty Hauwa ta zo wa Mama da wani batu, wanda ita Maman har cikin ranta ba ta ji dadinshi ba. Shi ya sa cike da kunar zuciya ta kalli Aunty Hauwa ta ce “Yanzu ke sai ki dubi tsabar idona, ki ce wai ana bukatar goyon bayana wajen yi wa Fatima kishiya, kuma idan an bar ki sai ki yarda zan bayar da goyon bayan?”

Cikin kwantar da murya Aunty Hauwa ta ce “Amma Mama ba tun yanzu ba ke uwa ce a wurin Mustapha, ba don yana auran Fatiman ba aike mai shige mishi gaba ce.”

“To da yake auranta fa? Idan har kawaici bai sanya Mustapha kin yi wa Fatima kishiya bai kamata ya sanyi shi neman goyon bayana wajen yi wa ƴata kishiya ba. To karya da ciwo mari da zafi, ni a fitar da ni a cikin wannan maganar. Ku je can ku yi ta d hakimin kamar yadda kuka faro ta a farko. “

” Mama” cikin sigar lallalashi Aunty Hauwa ta kira sunan “Wlh Mustapha bai ce yana son yarinyar nan ba, nagartarshi daga uwar har yarinyar suka gani, sannan mahaifiyar yarinyar nan ta roki alfarmar Mustapha ya auri ƴarta, ko don ceto yarinyar tata daga duhun take ciki zuwa haske. Ya kai wata biyu da ake ta nuku-nuku da maganar nan, kuma muna ta mata hanya-hanya. Idan yarinyar nan ta musulunta tare da gudunmuwarmu, muma muna da lada”

Mama da ta yi kasake tana sauraron Aunty sai ta dora “Ke! Kawai idan Mustapha zai yi auranshi ya yi kawai. Ita ma Fatiman Allah Ya kara mata Mustaphan nan da kadan ubanta ya fi shi, ai ga shi nan ta gama cin wuya da shi, lokacin da dadi ya zo zai kan ga ta wata. Ita kuma ba ta da komai sai Ƴaƴa.” yadda Mama ke ta, masifa kamar dai dama jira take yi, sai Aunty Hauwa ta mike cike da mutuwar jiki ta nufi kofa, gab za ta fita Mama ta ce” Kuma ki ji ni da kyau, idan har Fatima ta ce ta, gama zama da Mustapha to ta gama din wlh ba Hakimi ba ko sandar mulki ce ta zo nan gidan Fatima ba ta komawa. Munafukai kawai, yarinyar ta gama dawainiya da shi ku saka mata da kishiya.”

Aunty Hauwa dai uffan ba ta ce ba, ta fice daga gidan.

Ita kanta ba son wannan aure take yi ba, sai dai ya iya da abin da ya fi karfin wuta in ji kishiyar konan na.

Tun da Aunty Hauwa ta fita Mama ke masifa ita kadai, har ba ta ji shigowar Aunty Ayyo ba.

Sai da Aunty Ayyo ta ce “Wai Mama lafiya kike ta fada ke kadai?”

Ta juya hade da fasa shiga dakin da ta yi niyya, hannunta rike da Labule ta ce “Wata banzar magana ce Maman Zainab ta zo min da ita. Wai Mustapha zai auri kiristar Yarinyar nan da take zuwa nan.”

Aunty Ayyo ta saki baki cike da mamaki ta ce “Wai Mustapha dai mijin Fatima?”

“Fadi da ihu ki kara da wayyo Allah.”

Aunty Ayyo ta shiga tafa hannu cike da mamaki kafin ta ce “Kai jama’a! Namiji ɗan Mamanshi, shi ya sa ba a ba namiji amana idan dai a kan mace ne. To yanzu ita Fatiman ta sani?”

“Oho musu.” Cewar Mama a lokacin da take shigewa daki.

Aunty Ayyo ta biyo bayanta tana fadin “Mama kin ga dai abin da muke gujewa Fatima har ya zo ko?”

“To ba ta ce ba ta ji ba, ana ba ta tana kin karɓa, gani dai take yi Mustapha ya cika dari bisa dari.” Cewar Mama tana zama a kan kujera.

Aunty Ayyo ma ta zauna a kan kujerar, har lokacin fuskarta na nuna kaduwar labarin da ta ji

“Komai na Fatima ya kare a kan Mustapha. Karatun nan babu yadda ba mu yi ba, amma tai ta shiririta, sai haihuwa. Dama mun fada Mustapha yana jin kudi sun zauna mishi aure zai yi kuma mai zurfin karatu. Yanzu dai kam ina Fatima ina kishi da kanuri, mai digiri, yar masu kudi, haihuwar Abuja cikin daula, renon tsakiyar Maiduguri? “

” Ashe kin hango abin da na hango, amma Auntynku tana yi min wani lissafin banza da wofi. Ni dai idan har Fatima ta zo gidan nan a kan ta gama auran Mustapha to kuwa ba ta komawa.”

“A’a Mama yaran fa?”

“Ko ita ce ta haife duniya.”

Aunty Ayyo ta yi shiru cike da jimami “can kuma ta ce ni wlh na fi jin zafin yadda ta rika sayar da kayanta tana ba shi, yana hidimar karatunshi ita ba ta yi ba.”

“Ummm! Yanzu yaushe ake kudin kasa kuma gari ya tashi. Maganar karatu kuma Fatima ai sai dai a lahira. Amma ba dai a wannan duniyar ba. Yara hudu, ta ina za ta fara?” Mama ta fads cikin tabe baki

“Wlh fa.”

Haka dai su kai ta tattauna abin da suke gani babban kalubalene a wurin Fatima idan aka hadasu kishi da Blessing. Akwai tazara mai nisan gaske a tsakaninsu.

<< Daga Karshe 34Daga Karshe 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.