A hankali magana ta shiga kunnen ma fi yawan kusanci da Fatima, da yawansu Allah Ya kara suke mata, da fadin wai dama wana kambun maza ne, ka gama shan wahala dasu daga karshe su suka maka da kishiya.
Fatima kam ba ta san abin da yake faruwa ba, harkar gabanta kawai take yi, musamman yanzu da suka hada hannu da Ummi suna kasuwanci hijabai dinkakku da kuma dogayen riguna. A bangaren Mustapha kam ba ta da wani kuka in yanzu ta ce wash zai ce menene, idan bai magance ba, to tabbas baya da shi ne.
Maganar zuwa Maiduguri kuwa Hakimi ne da mutanensa biyu da kuma dangin Baban Mustapha mutum daya dangin Inna ma mutum daya suka je.
Kuma basu baro ba, sai da Blessing ta karbi musulunci hade da tsayar da ranar bikinsu watanni hudu masu zuwa
Sam Fatima ba ta san da zancen ba, koda wasa Mustapha bai fada mata ba ƴan’awanta ma babu wanda ya taba fada mata.
Abin da ya ishi Aunty Hauwa kenan, naka dai naka ne koda baya ba ka komai.
Har cikin ranta take jin, ina ma Blessing Hakimi ta yi sha’awar aure ba Mustapha ba.
Yau dai misalin karfe 11 na safe ta kira Fatima ta sanar mata tana son ganinta da yamma.
Gara kawai a yi ta, ta kuma kare, don barin kashi a ciki dai baya maganin yunwa.
Ba ta kawo komai da kiran Aunty Hauwa ba, don ba wannan ne karon farko da take mata hakan ba. Kuma idan ta je sai ta ga nothing serious.
Shi ya sa yau ma ba ta kawo komai ba, misalin karfe 4:30pm ta fito cikin saukakkar kwalliya goye da Hassan yayin da ta saba Husaini a kafadarta.
Kamshi mai dadi na fita a jikinsu.
Kallo daya dai za ka yi mata ka fahimci cewa daidai gwargwado hankalinta a kwance yake, kuma ana samun cima mai kyau.
Kamar ta shiga gidan Mama sai kuma ta fasa, kai tsaye ta shiga gidan Aunty Hauwa.
Tun a tsakar gidan yara suka karbe Husaini a hannunta, shi ya sa ta shiga da goyon Hassan kawai.
Sai da suka gaisa da Aunty Hauwar sannan ta aje Hassan kan kujera, da yake sun fara koyon zama.
Hira suke yi sosai wacce da yawanta a kan abin da ya shafe su ne.
Kafin daga bisani Aunty Hauwa ta kira sunanta.
Haka nan sai ta ji gabanta ya fadi, ba ta samu damar amsawa ba, Aunty Hauwa ta dora da “Don Allah ki yi hak’uri Fatima, sannan ki ba mara ɗa kunya don Allah.”
Still kallon Aunty Hauwar take yi ba tare da ta ce komai ba, amma bugawar da kirjinta yake yi ya tsananta.
“Ban san ta ina zan fara fada miki ba, amma ina son kin danne ki kuma cije, don Allah kar ki sanya damuwa a zuciyarki, kuma kar ki biye wa zuciyarki wajen yanke hukunci.”
Har zuwa lokacin dai Fatima ba ta ce komai ba, da alama kuma ba za ta ce din ba.
“Ba ku yi maganar komai da Mustapha?” ta yi tambayar ne kawai don neman hanyar fadin abin da take son fada amma ita kanta ta san Mustapha bai fadawa Fatima komai ba.
Girgiza kai ta yi, alamar a’a.
Aunty Hauwa ta nisa kadan sannan ta ce “Kar ki ga laifin shi, ki yi mishi kyakkyawar fahimta don Allah. Wlh Mustapha yana matuka sonki, kuma ba da son shi abun nan ya faru ba.”
Yanzu kam tagumi ta zuba da hannayenta du biyun tana kallon Aunty Hauwa.
“Mamar Blessing ta roki alfarma a kan Mustapha ya auri Blessing bayan ta musulunta, saboda ta yaba da dabi’unsa da kyawawan halayensa. Mustapha bai amince ba, shi ya sa ta zo wurin Hakimi. Kin san kuwa shi uba ne ga kowa.”
Fatima dai ko aya ba ta diga ba.
Aunty Hauwa ta ci gaba” Ina jin dai kwana sha shidda kenan dasu Hakimin suka je Maiduguri, Blessing ta muslunta, kuma an sanya ranar bikinsu da Mustapha watanni hudu masu zuwa. “
Ta dire maganar idanuwanta kafe a kan fuskar Fatima.
A lokacin Fatima ji ta yi kamar dai hankalinta ya gushe na wani lokaci, zuwa can kuma ya dawo, shi ya sa ta yi kokarin daidaita nutsuwarta.
Cikin nauyin baki ta ce” Allah Ya sanya alkairi. “
Cike da mamaki Aunty Hauwa ke kallon ta, ai ba ta tsammaci haka daga gare ta.
Ganin Fatima na kokarin goya Hassan ne Aunty Hauwa ta kira sunan ta.
Ta juyo ba tare da ta amsa ba
“Kina lafiya?”
“Eh. “
“Kin tabbatar? “
Kai ta dagawa Aunty Hauwar sannan ta ci gaba da gyara goyon Hassan.
Aunty Hauwa na kallon ta fice daga falon ba tare da ta ce komai ba, alama kowa ba shi da kuzarin magana don ita ma Aunty Hauwar ba ta ce komai ba.
A tsakar gida ta saba Husaini ta fice daga gidan.
A kofar gida ta tsaya tana kallon kofar gidansu, ina ma ace Alhaji na nan, da yanzu sai ta shiga ta fadi kanshi ta baje damuwarta amma yanzu duk inda za ta je ta yi kuka, ce mata za a yi Allah Ya kara. Musamman Mama korarta ma za ta yi, ta ce ba a gidan za ta yi kuka ba.
“Ko gidan Ya Bashir?” ta tambayi kanta, lokaci daya kuma tana kallon hanyar da za ta sadata da gidan Ya Bashir din.
“Kai a’a. Aunty Billy tsab za ta ba su Aunty Aisha labari.”
Da kanta ta ba kanta amsa, kafarta kawai ta rika jefawa, hankalinta baya jikinta, yayin da zuciyarta take a cushe.
A haka ta yi sallama gidan Ummi karo na biyu da ta zo gidan Ummin tun bayan auran ta.
Yankan dinki take yi, shigowar Fatima sai ta dakata tana fadin sannu da zuwa Aunty Fati.
Kwantar da Husaini ta yi a hankali don ya yi bacci.
A lokacin ne zuciyarta ta bude daga cunkushewar da ta yi.
Jagwab ta zauna kan kujera lokaci daya kuma ta sake kukan da take jin shi daga ko wane loko da sako na jikinta, wannan kuka na farko da take jin tabbas ta yi a lokacin da ya dace kuma a kan abin da ya dace.
Jikin Ummi na rawa ta karaso kusa da Fatima hade da dukawa cikin kosawa ta ce “Aunty Fatima me ye ya faru?”
Duk irin tambayoyin da Ummi ke mata ko daya ba ta amsa ba, kukanta kawai take yi, sai da ta ji kaso 80 cikin dari na cushewar zuciyarta ya zube, sannan ta mike hade da goya Hussain don yanzun kuma Hassan bacci yake yi.
“Aunty Fatima don Allah ki yi min magana.” cewar Ummi cikin marainiyar murya.
Sai da Fatima ta kuma dauke hawayen da suka sakko sannan ta ce “Yayanki aure zai yi.”
Tana gama fadin haka ta fice, yayin da Ummi ta tsaya kamar zane, da alama komai ya tsaya mata.
Fatima kam tafiya take tana kuka, kukan da ita kanta ma ta kasa gane na menene, ya fi kama da na tausayin kanta fiye da kishi.
Sai da ta karbi cajin wayarta sannan ta karasa gida.
Hussain ta kwantar kan kujera kafin ta dauro alwala.
Raka’ar ta daya Ummi ta shigo dauke da Hassan a bayanta.
Ita ma sai ta kwantar da shi ta dauro alwala.
Bayan ta idar da sallah ne ta dubi Fatima da take jan carbi. Tausayinta ya kamata sam ba ta cancanci wannan sakayyar daga yayanta ba, abun is too early.
“Aunty Fatima don Allah ki yi hak’uri ki yafewa Yayana”
Ba Ta daina jan carbin ba ta ce “Bai yi min komai ba Ummi.”
“Ya yi miki Aunty Fatima, ba ki cancanci wannan sakayyar daga gare shi.”
Shiru Fatima, ta san da zarar ta bude baki kukan da take boyewa zai bayyana.
Don haka sai wurin ya yi shiru har zuwa lokacin da Fatima ta ce “Alfarma daya za ki yi min?”
“Wacce?”
“Kar ki fadawa Yayanki mun yi wannan maganar, sannan don Allah idan ba shi ne ya tuntubeki da maganar ba, kar ki yi mishi”
Kai Ummi ta shiga jinjinawa, kafin daga bisani ta fashe da kuka.
Kuka take yi sosai, duk irin lallashin da Fatima take yi mata ba ta yi shiru ba, sai ma ta tashi ta fice daga gidan.
Wannan ya ba Fatima damar fashewa da na ta kukan.
Kiran Mustapha ya shigo, cikin sauri ta daidaita muryarta. Gab wayar za ta tsinke ta daga, ya amsa sallamarta yayin da yake nazarin muryarta.
Amma babu abin da ya gano, wannan ya ba shi mamaki sosai, don ya dauka yana rikici zasu sha.
Tun da Aunty Hauwa ta fada mishi yadda suka yi da Fatiman yake cikin fargaba. Ji yake kamar ya bar garin. Daurewa kawai ya yi wajen kiranta, amma ga mamakinsa ta basar kamar basu yi wata magana da Aunty Hauwa ba.
Shi ma sai ya basar din ya ce “Ina twins dina?”
Murmushin karfin hali ta yi sannan ta ce “Duk sun yi bacci”
“Saura mamansu kenan”
“Eh.” ta amsash a hankali.
“Akwai wata matsala ne a gidan?”
Kamar yana kallon ta shiga girgiza kai, sannan ta ce “Babu komai”
“Zan yi sallah” ta yi saurin fada tun kafin ya dakko wani zancen.
“OK to”
Ba tare da ta ce komai ba, ta yanke kiran.
Cilli ta yi da wayar hade da fashewa da Kuka, nan ma ta yi mai isarta, sannan ta canjo alwala.
Kwanciya ta yi kan sallayar bayan ta idar da sallah, yunwa take ji amma bakinta very test less.
Sosai take tausayin kanta, babu inda za ta je a danne mata zuciya, wannan abun Allah kara ne ya same ta. Ta rasa da wanne za ta ji, maganar kishin, ko yadda ƴan’uwanta zasu yi mata dariya, ko kuma dai yadda ta jawo Mustapha ta lullubeshi da bargo, shi kuma ya ja ta cikin tsakiyar kasuwa ya yi mata tsirara, ko kuma dai rashin karatu mai zurfi, yanzu za a hada ta kishi da mai digiri.
Kai karshen wannan tunanin nata ya yi daidai da zirarowar hawayenta masu dumi.
Haka ta rika tsiyayar da hawayen har bacci ya dauke ta.
Misalin 12:49am kukan Hassan ya tashe ta, sai a lokacin ta tuna ashe ko madararsu ma ba ta basu ba.
Ta dauke da sauri don kar ya fado, ta fitar da nono ta ba shi, sai da tabbatar ya koshi har ya koma bacci, sannan ta dakko madarar ta hada saboda Hussaini yana ta motse-motse.
Shi ma sai da tabbatar ya koshi sannan ta kwantar shi, zuwa lokacin 1:30am daidai, maimakon ta kwanta sai ta dauro alwala ta kai kukanta wajen mai duka, musamman a kan abin da zuciyarta ta fi rinjaya.
Lokacin da gari zai waye sosai ta ji zuciyarta ta rage wancan nauyi, tana tsaka da aikin gida kiran Mustapha ya shigo, kamar ta share saboda a yanzu idan akwai fuskar da ta tsani gani ta shi ce, idan akwai amon muryar da ke bata mata rai tashi ce.
Amma so take ta ga iya gudun ruwan shi, dalilin da ya sanyata sai ta kanta ta kuma daga kiran.
Suka gaisa hade da tambayarta yara, ta tabbatar mishi kowa lafiya, shiru ya ratsa wayoyin jira yake ya ji ko za ta ce wani abu amma ta yi shiru, tun jiya da Aunty Hauwa ta ce sun yi maganar zuciyarshi take a tsinke, amma har yanzu Fatima ta ki tanka lamarin ta bar shi cikin fargaba da tashin hankali. Har kiran Aunty Hauwa ya yi, yana kara tabbatar da sun yi maganar kodai ta rufe shi ne, ta kuma tabbatar mishi da bakinta bakin Fatima haka suka yi magana.
Jin shirun ya yi yawa sai Fatima ta ce “Idan ba komai aiki nake yi.”
Sai a Lokacin ya tuna ashe waya suke yi.
Cikin daburcewa ya ce ba komai, sai ta yanke kiran hade da jefar da wayar kasa. Wani abu ya tsaya mata a kirji, dole tana shara tana kuka ko ta samu ya wuce.
Misalin karfe tara na safe sai ga Aunty Hauwa, a lokacin Fatima wankin kayan su Hassan take yi, su kuma suna cikin kekensu na zama suna wasa.
Ta amsa sallamar hade da kirkiro fara’a.
Aunty Hauwa ta zauna a kan tabarmar da ta gani shimfide a kofar daki, tana amsa gaisuwar Fatima cike da mamakin yadda ta ganta tamkar dai babu abin da ke damunta. Ba Ta san lokacin da ta ce”Anya Fatima akwai ko zuciya a kirjinka? “
Ta dakata da wankin tana kallon Aunty” Me ya faru? “
Aunty Hauwa ta sauke hannun ta da ta rike habarta da shi ta ce” Ni fa jiya ko baccin kirki ban yi ba, kosawa na yi gari ya waye, hankalina tana wajenki, amma ke na ganki ras abunki, ko a jikinki wai an tsunkuli kakkausa.”
Murmushin karfin hali kawai ta yi ba tare da ta ce kanzil ba.
“Dama zuwa na yi in ga halin da kike ciki, hankalina ya kasa kwanciya. “
“Ina lafiya Aunty. “
“Wai an ya kuwa kin ji abin da na fada miki jiya? “
Wannan karon sai da sautin dariyarta ya fita. “Na ji mana, ba cewa kika yi, an tsayar da lokacin bikin Ya Mustapha da Blessing ba?”
“Haka kuwa na ce, amma shi ne kike zaune ko jikinki Fatima kina wanki?” cike da mamaki Aunty Hauwa ke maganar.
“To Aunty me zan yi?”
“Ba komai. Allah Ya kyauta.” ta yi maganar hade da yunkurawa ta tashi tsaye.
“Ni na tafi.”
Tsame hannun ta ta yi a cikin ruwan wankin ta bi bayan Aunty Hauwa.
Har kofar gida sai da ta danyi nisa sannan Fatima ta tura kofar zaure hade da manna bayan ta gini ta fashe da kuka.
Cikin muryar kuka take fadin “To Aunty ya zan yi? Me kike so in yi? In zo gida a yi min dariyar wanda ya dauki namiji uba maraya zai zama? Ina zan je Aunty! Ina zan je!! Yanzu lokacin Allah Ya kara ne, ni kuwa ba zan je ba, bare a yi min ita, a kara min haushi.” cikin kuka sosai take maganar, sai da ta ji kukan Hussaini sannan ta bar zauren cike da tausayin kanta, ita da kuka yake mata wahala, yau gashi ta kwana kuka da alama za ta wuni yin shi, Allah kadai ma ya san ranar tsayuwar hawayenta.
Tana ba Hussaini nono Ummi ta yi sallama, ta amsa ta cike da kulawa, har ta karaso kuma Fatiman ba ta dauke idonta a kanta ba.
Ba tare da ta zauna ba suka gaisa, sannan ta zame hijabinta ta dora kan igiya, ta nufi wankin da Fatima ke yi.
“Aunty Fatima don Allah kar ki sa damuwa a ranki, ko ki ce za ki bar gidan nan, ni ke na sani a matsayin uwa, idan kika tafi zan yi maraici” cewar Ummi cikin kuka hannayenta du biyun a cikin ruwan wanki.
Fatima ta yi shiru tana kallon kofar shigowa kamar mai jiran shigowar wani.
Ita tafiya gida ma bai zo kanta ba, shi din wani abun gori ne kuma a wajen ta, kullum Mama sai ta goronta mata, haka ma ƴan’awanta.
“Yayana bai kyauta ba, bai yi miki halasci ba, kin aure shi ba shi da komai, kika zauna da shi tsawon shekaru hudu cikin matsi, kika siyar da kayanki don magance matsalolin shi, kika rike mishi uwa kamar ta ki, kika rike mishi kanwa rikon ƴa da uwa. Kika rasa cika burinki kika cika mishi na shi, amma maimakon da ya samu dama ya cika miki na ki sai ya saka miki da kishiya, kuma wacce ta fi ki komai.”
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce” Zan cika burina da kaina Ummi. In sha Allah sai na cika burina Ummi. “
Ummi ta rika yi mata kallon ta wace hanya za ta cika shi.
Murmushi Fatima ta yi kafin ta ce” Za ki gani, in sha Allah zan cika burina, daga jiya na dora ɗanba, ke dai ki yi min addu’a. Sannan duk abin da zai faru ya zama tsakaninmu ne kawai. “
“In Sha Allah! Kuma ina yi miki fatan alkairi.”
“Na gode” cewar Fatima, lokaci daya kuma ta mike zuwa daki don kwantar da Hussaini saboda tuni ya yi bacci.