Yau Juma'a wainar shinkafa take son don haka misalin karfe goma ta gama hada komai ta koma daki ta kwanta, wani irin bacci take ji, saboda yawan tashin dare da take yi, shi ya sa da rana ko safe sai ta dan taba bacci.
Tun su Hassan suna tsalle-tsalle a kanta har suma bacci ya daukesu.
Cikin baccin ta rika shakar kamshin turaren Mustapha.
Ta rika bude idonta kadan-kadan har ta bude su a kansa.
Sanye yake cikin suit coffee color masu sheki, sun dau guga, kafadarshi sagale da bakar jaka wacce za ta iya daukar kaya. . .