Skip to content
Part 37 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Yau Juma’a wainar shinkafa take son don haka misalin karfe goma ta gama hada komai ta koma daki ta kwanta, wani irin bacci take ji, saboda yawan tashin dare da take yi, shi ya sa da rana ko safe sai ta dan taba bacci.

Tun su Hassan suna tsalle-tsalle a kanta har suma bacci ya daukesu.

Cikin baccin ta rika shakar kamshin turaren Mustapha.

Ta rika bude idonta kadan-kadan har ta bude su a kansa.

Sanye yake cikin suit coffee color masu sheki, sun dau guga, kafadarshi sagale da bakar jaka wacce za ta iya daukar kaya kala biyu.

Ko wane lokaci Mustapha kara gogewa yake, kyanshi da kwarjininshi na kara fitowa.

Yanzu ma da yake gabanta sai take ganin kamar ba mijinta ba, irin ruwa ba sa’ar wandon nan ba.

Idan wayewa da gogewa ake nema kam, a yanzu Mustapha ba sa’arta ba ne. Wayewarshi da gogewar da ya yi cikin yan watanni babu mai kallon shi ma ya ce ya aje mata da yara hudu.

Ya mika hannu ya dago ta, ba tare da ya yi magana ko ya ba ta damar magana ba, janta yake yi a hankali har ya tura ta cikin dakin sannan ya mayar da kofar ya rufe.

Cikin salo da dabara ya raba ta da duk kayan jikinta har zuwa lokacin bai ba ta damar yin magana ba.

Sai da ya tabbatar ya gamsu sannan ya koma gefe hade da rungumeta tsam a jikinsa.

Cikin wata irin murya ya ce “Fatima I’m very sorry please, I’m sorry, please for give me”

Tana jin sa amma ba ta ce komai ba, kara matse ta ya yi a jikinsa”wlh ina sonki, har yanzu ina kaunarki, na kasa samun nutsuwa, da kaina nake jin ba ki cancanci wannan ba, amma babu yadda na iya ne don Allah ki yi hakuri Fatima I’m so sorry! “

So take ta daure ta kuma cije kada ta yi kuka amma kuma ta kasa yin hakan zuciyarta ta yi rauni, a hankali sautin kukan ya rika fita, daga jin kukan ka san cewa kuka ne da ake yin shi domin samun saukin zafin da ake ji a zuciya.

Sosai Mustapha ya kuma rikicewa ya shiga lallalashinta tare da furta mata maganganu masu dadi, alƙawura kam ta sha su.

Ita dai ba ta mar komai ba. Sai ma zare jikinta da ta yi ta wuce toilet.

Sai da ta kintsa jikinta sannan ta shige kitchen don aikin abinci rana. Yayin da Mustapha ke ta wasa da su Hassan a falo.

Misalin karfe daya ya fito cikin shirin masallaci, shadda ce wagambari fara tas, da aka yi wa dinkin gari, shi ma sai ya fito sosai kamar ba Dansadamu ba zuwa ya yi, kansa bakar dara ce da bakin takalmi cover na maza, kamshinsa mai dadi ya cika falon.

Fatima da ke zaune ta bi shi da kallo a lokacin da yake daura tsadadden agogonsa.

A zuciyarta take fadin ashe Mustapha mai kyau ne, hutu ne bai samu ba, lokaci daya ya canja, canjin da ke ba ta mamaki.

Ya kai hannu saitin idanunta ya karkarda, take ta dawo hankalinta

“What are you thinking?”

“Ba Komai” ta amsa a hankali.

Ya duka gabanta hade da dafa gwiwowinta

“I’m still love you Fatima, ƙi yarda wlh har abada babu kamar ki a wajena. Ke din mai daraja ce a wurina.”

Jin sa kawai take yi, amma idan jikinta duk kunne ne ba za ta yarda, zuwa yanzu kam ba ta san me Mustapha zai yi ya dawo kamar da a zuciyarta ba.

Ya kama hannunta hade da kissing din bayan hannu, ita dai kamar zane haka ta zame mishi, har ya fice daga falon bayan ya dauki sallaya. Ta bi bayan sa da kallo hade da sauke ajiyar zuciya.

Fitarsa ke da wuya, ta hadawa su Hussaini ruwan wanka, ta shirya su tsab cikin shadda golden kala, da takalmansu masu kyau brown color, duk ta aje su a kan keke bayan ta basu madararsu, sannan ta shiga wanka.
Ita ma ta shirya cikin shadda irin tasu dinkin doguwar riga, ta zuba sarka da yan kunne, sosai ta yi kyau, tana fesa turare ta ji shigowarsa ba ta fita ba, kuma ba ta fasa abin da take yi ba.

Tana jin sa yana yi wa su Hassan wasa suna kyalkyata dariya.

Lokacin da ya shigo dankwali take daurawa, dankwalin ya karbe tare da kwantowa a bayanta, fuskarsu ta hadu a cikin mirror, duk yadda ta so kin karbar sakonshi sai da jikinta ya bijirewa hakan.

Wata sabuwar soyayya ce Mustaphan ya zo mata da ita a wannan karon, kamar jiya aka kawo mishi ita.

Abinci ma tare suka ci, sai da aka kira la’asar sannan ta fita gidan.

Gidan Mama ya shiga bayan ya fito daga masallaci, abin da ya tsammani kuwa shi ya taras, Aunty Bilki, Aunty Sadiya da kuma Aunty Ayyo duk suna gidan

Cike da girmamawa suka gaisa sannan ya wuce dakin Mama.

Duk suka bi bayansa da kallo sai da ya shige dakin Mama.

Zaune take kan sallaya da alama sallah ta idar. Har kasa ya duka suka gaisa, ta yi masa sannu da zuwa sannan suka shiga hirar yau da kullum, koda wasa Mama ba ta yi mishi maganar biki ba, tamkar ma dai ba ta san da maganar ba, shi kuma nauyi da kunya sun hana shi yin maganar duk da ya yi shiru, alamun akwai magana a bakinshi.

Ganin shirun ya yi yawa ne ya mike cike da girmamawa ya yi mata sallama.

Gidan Aunty Hauwa ya yi niyyar zuwa sai kuma suka hadu a bakin kofa, ita za ta shigo shi zai fita, don haka a nan suka gaisa a takaice, sai dai ya fada mata zuwa gobe sha Allah zai bullo su tattauna.

Mama ta fito daga daki hade da yin masauki a kan dutsen da ke kusa da kofarta.

Tana sauraron gulmar da yaranta ke yi.

Aunty Ayyo ce ta ce “Ikon Allah! Allah Ya bamu kudi masu albarka. Don Allah ku kalli yadda Mustapha ya canja lokaci daya.”

Aunty Bilki ma ta ce “Wlh fa ya zama kamar wani Dan Ministern kudi.”

Suka dan yi dariya kafin Aunty Sadiya ta ce “Shi ya sa ya rakimo aure, maza haka suke, da sun ga canji sai ki ji aure kuma.”

“Ummm! Ko kun san har yanzu Fatima ba ta taba yi min zancen auran nan nashi ba.” Aunty Ayyo ta fada tana kallon sauran.

Dukkansu suka ce su ma ba ta yi musu ba.

Mama ta tsoma baki “Ai ni ma nan ba ta yi min ba, ke tun da aka tsira maganar auran ma ba ta zo gidan nan ba.”

Aunty a shigo gidan hade da sallama, suka amsa mata, ta shiga gaishe da Mama a lokacin da take zama.

Aunty Ayyo ta tare ta da maganar ko sun yi magana da Fatima ne game da auran Mustapha.

Tabe baki Aunty Hauwa ta yi sannan ta ce” Yadda dai na ba ku labari har yanzu haka abun yake, da alama auran ma mu ya dama ita bai dame ta ba.”

“Ai har yanzu ba ta yi hankali ba.” in ji Mama tana kallon Aunty Hauwa.

“Allah Ya kyauta” suka hada baki wajen fada.

Daga gidan Mama Mustapha gidan Ummi ya wuce, dama ya saba zuwa, duk lokacin da ya zo ya kan je gidan su gaisa, sosai hakan yake mata dadi, sai ta ji ta wata mai gata.

Lokacin da ya yi sallama Hana ce ta amsa hade da lekowa zauran, ganin Abbanta take rungume shi tana murna, kafin daga bisani ta sake shi, ta ruga zuwa cikin gida tana yi wa Ummi da Ziyad albishir.

Zuciyar Mustapha ta cika da farin ciki, yana son yaranshi sosai, musamman ya gansu fes cikin walwala.

Ba jimawa Ummi ta fito sanye da zundumemen Hijab hannunta rike da Ziyad yayin da Hana ke bin su a baya.

Har kasa ta duka ta gaishe shi cike da girmamawa, ya amsa cike da kulawa.

Sai da ya fara tambayarta ko akwai wata matsala ta amsa mishi da ba komai, ya juya batun sana’a, nan ma ta ce komai yana tafiya lafiya ƙalau.

Ya gyara tsayuwarsa yana kallon ta “Ummi kun yi wata magana da Auntynki ne?”

Tana dago kai tana kallon sa, yanayin fuskarta ta amsa mishi tambayar shi ma’ana dai basu yi wata magana ba.

Ya nisa a hankali kafin ya ce “Ba Ta fada miki zan yi aure ba?”

Ido ta fitar waje sosai alamun mamaki “Aure kuma Yaya?”

Ya sauke ajiyar zuciya hade da kallon inda su Hana suke suna game da wayar shi.

Kai ya jinjina alamun eh.

Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya ce “Na san kina jin Fatima tamkar mahaifiyarki, ba kya son abin da zai bata mata rai, ciki kuwa har da ni. Na san kina min kallon butulu, ciki mai manta kyautar jiya, ko wane kallo ma dai mutane zasu yi min Allah Ya san abin da ke cikin zuciyata. Sai dai daga ke har Fatima ina rokon yafiyarku. “

Ummi dai ba ta ce komai ba, kanta yana kasa.

Ya dora” Blessing mutuniyar kirki ce, ba sai na fada ba, kin san tarin alkairinta gare ni. Mahaifiyarta ta roke ni da in aure ta bayan ta muslunta, amma ban karbi tayin ba, shi ya sa ta sako Hakimi a ciki, kuma kin san waye Hakimi, shi ne ya shige gaba wajen karbar auran nan. Amma ban yi niyyar yin aure ba, don nunawa Fatima iyakarta ba. And idan har akwai wani kaso na lada da nake da shi a, auran Blessing da kuma musluntarta, na, sadaukarwa da Fatima da shi. Ki shaida. “

Cikin nauyin baki Ummi ta ce” Allah Ya tabbatar da alkairi. “

Ya amsa da amin, sannan suka shiga tattaunawa a kan wasu matsalolin, sai da ya tabbatar ya gamsar da Ummi maganar aure ba zabinshi ba ne sannan ya baro gidan.

Sai da ya yi sallahr isha’i sannan ya koma gida.

Wata irin soyayya Fatima ke gani daga gare shi, tamkar jiya aka kawo ta gidan, ta ma rasa yadda za ta fassara abun.

Bai tafi ranar Lahadi ba, kamar yadda ya saba, sai Monday, tamkar dai baya son komawar, abin da ya zo wa Fatima da mamaki.

Yana tafiya ta kira Zainab a waya, wacce ta iso a safiyar ranar.

Kamar mintuna 30 kuwa Zainab ta iso.

Fatima ta bi ta da, kallon sha’awa, kominta a waye fes da ita.

Ka rantse ita ta tsarawa kanta rayuwa, ta gama nursing school ga aiki ta samu a general hospital Katsina, ga miji mai ilmi wanda ya jiku da naira, to me ye kuma take nema.

Don matsalar dubu dari Zainab na magance ma kanta, yanzu haka ma Umra zasu da azumi.

Sai ta ji duk tausayin kanta ya kama ta.

Zainab ta katse mata tunani da fadin “Kin hada takardun?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Sai dai in hada yanzu.”

Zainab ta zauna a kan kujera lokaci daya kuma tana yi wa su Hassan wasa, “Aunty Fatee!”

Ba ta amsa ba, amma ta zubawa Zainab din idanunta.

“Kina ganin karatun nan zai yiwu a wannan lokacin. Yara hudu, ga aure sannan ba ke kadai ba ce, dame za ki ji? Kokarin janyo hankalin miji kanki, tarbiyar yara ko karatun?”

Fatima ta nisa kadan kafin ta ce “Zainab zama ba karatun ma wani kalubalen ne, don Allah kar ki sace min gwiwa ki karfafa min ita.”

Duk suka yi shiru na ƴan sakanni sannan Zainab ta ce “To me ye fa’idar boyewa kowa kina neman admission?”

Sai da ta dauki Hussain da yake kananun kuka sannan ta ce “Saboda babu wani zai ba ni kwarin gwiwa, kowa zai ce karatu ba nawa ba ne yanzu, saboda na tara yara. Amma kuma gemu ai baya hana ilmi”

Kai Zainab ta jijjiga hade da fadin “Shi kenan Allah Ya shige mana gaba.”

“Amin” In ji Fatima cikin sanyin jiki

“Amma me ya sa kika canza daga malamar makaranta ko ta jinya kika koma bangaren aikin gidan radio.”

Sai da Fatima ta murmusa ta ce “ina son in rika gaishe da Mama kullum”

Tare suka yi dariya, Zainab ta ce “Gaskiya kam, irin soyayyar Mama da radio ya kamata ta, samu wanda zai rika gaishe ta kullum.”

“You see” cewar Fatima a lokacin da ta mike zuwa bedroom don hadowa Zainab takardunta.

Sai da Zainab ta hada duk wani abu da ta san ana bukata har da hotunan Fatima, sannan ta tafi.

Kamar yadda Fatima ta ce Zainab ta rike mata sirrin neman admission dinta, Zainab din kam ta yi kokarin rikewa, don basu taba maganar da kowa ba.

Har zuwa lokacin da aka fara sakin admission din, cikin ikon Allah sunan Fatima na sahun gaba.

Samun wannan labari ba karamin faranta mata ya yi ba, har azumi ta tashi da shi, yanzu kuma fatan ta bai wuce hanyar samun kudin registration ba.

Burinta shi ne har ta gama school din nan kar ta roki kowa komai, ciki kuwa har da Mustapha.

Matar J ✍🏻

<< Daga Karshe 36Daga Karshe 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.