Bai damu da kukan da take yi ba, ya shige toilet ya yi wanka hade da dauro alwalar magariba.
Da zai fita ne ya ce "Za ki iya komawa gidan bikin yanzu idan kina so."
Ta san so yake ya kara mata haushi, kuma ta ji haushin sosai.
Har aka idar da sallahr magariba tana zaune a tsakiyar gadon tana marayan kukanta.
Ganin duhu ya fara shigowa dakin ne ta mike zuwa toilet ta yi wanka hade da dauro alwala.
Tana kabbara sallah ta ji kukan su Hassan, ta san kawo mata su aka yi, yaye su dai za ta. . .