Skip to content
Part 43 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Bai damu da kukan da take yi ba, ya shige toilet ya yi wanka hade da dauro alwalar magariba.

Da zai fita ne ya ce “Za ki iya komawa gidan bikin yanzu idan kina so.”

Ta san so yake ya kara mata haushi, kuma ta ji haushin sosai.

Har aka idar da sallahr magariba tana zaune a tsakiyar gadon tana marayan kukanta.

Ganin duhu ya fara shigowa dakin ne ta mike zuwa toilet ta yi wanka hade da dauro alwala.

Tana kabbara sallah ta ji kukan su Hassan, ta san kawo mata su aka yi, yaye su dai za ta yi ta huta, wannan komawar ba za ta koma dasu ba, da dai taso sai ta yi exam, amma yanzu kam ba za ta iya ba, azabar ta ishe ta haka.

Ta sallame sallahr hade da janyo Hussan don kuka yake yi sosai, lokaci daya kuma suna gaisawa da Ummi.

Ita ma Ummi alwala ta yo ta zo ta kabbara sallah.

Tana ba Hussaini nono Blessing ta shigo, sai yanzu Fatima ta kare mata kallo, sosai ta canja, ta yi haske hade da kara yar ƙiba mai ban sha’awa. Kamar mai karamin ciki, sai wani kishin sabo ya kamata.

Kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba tashin arewa ba ce, fatar lingif alamun hutu da kuma kuma lafiyayyun maya-mayai da subulai.

Kan kujerar ta zauna, hade da daukar Hassan da yake mayar da ajiyar zuciya tana fadin “My boy, who touch you?”

Ya zuba mata jikakkun idanunsa yana mata kallon rashin sani.

Cike da fara’a ta maido da hankalinta kan Fatima “Mom Ziyad ina wuni?”

Fatiman ta amsa ba yabo ba fallasa, hankalinta a kansu Hana da Ziyad da wasu yaran su Aunty Aisha da suka shigo.

Blessing ta bi su da kallon sha’awa yadda Fatiman ta basu attention kuma take fahimtar duk wata magana tasu, ko wane lokaci Blessing tana jin ina ma ita daya ce daga ƴaƴan Mama suna burge ta sosai.

Wayayyu, ga llmi, iya, dressing ga kuma son junansu.

A daidai lokacin Mustapha ya shigo.

Blessing ta yi mishi sannu da zuwa, Fatima ta yi kamar ba ta san ya shigo ba, shi da ya san dalili sai dariya ta kufce mishi.

Ya mika hannu ya dauki Hussaini da yake kan jikinta lokaci daya kuma yana zama kan kujera, shi ma hankalinsa a kan yaran. Sai Blessing ta zama hoto saboda har yanzu ba ta goge da hausar da za a rika hira da ita ba, don Fatima shigewa bedroom ta yi ta barsu a wurin.

Tana kan sallaya bayan ta idar sallahr isha’i Ummi ta shigo yi mata sallama.

Sai dai suka tattauna a kan hadakar kasuwancinsu, sannan Fatiman ta mike don yi wa Ummin rakiya.

Har zuwa lokacin Mustapha, Blessing da su Hana suna falon.

Ya kasa dauke idonsa a kanta, yadda take wani basarwa sai yake jin wani shauki.

Gab za ta wuce ta gaban shi ne ya ce “Yaran nan zasu kwana a nan ne?”

Cike da borin kunya ya yi maganar saboda daga Ummi har Blessing sun sanya mishi ido.

Ta juya hade da kallon yaran, kafin ta tabe baki, kamar ba ta son magana ta ce “oho musu.”

Ummi ce ta tasa keyar yaran, sai da suka je zaure Ummin ta ce “Ba za a hana yayana sakewa ba wlh, duk su tafi gidan Mama.”

Fatima ta daure fuska tamau “Yaushe muka fara wannan wasan da ke?” Ta ce tana kallon Ummin.

“Ba wasa ba ne, gaskiya na fada, wlh Ya Mustapha hankalinsa baya jikinsa, ke kuma sai wani sha mishi kamshi kike yi, Aunty Fatima laifin kam ba ya wuce ba?” A marairaice Ummi ta karasa maganar.

“Mtswww!” Fatima ta ja tsoki. Hade da juyawa ta koma ciki.

Tana fadin “Idan kin gama sharhin Allah Ya tashemu lafiya.”

A falon ta wuce su, ta shige bedroom ta yi kwanciyarta a bun ta.

Jin shirun ne ya sa Mustapha biyo bayanta.

Gefenta ya zauna sannan ya ce “Ya za ki bar bakuwa a falo.”

“Wacece bakuwar?”

Ta tambaya ba tare da ta kalle shi ba.

“Rahama. Ina nufin Blessing”

Yanzu kam ta Kalle shi, sannan ta tabe ba ki “To me ye kuma hadina da ita, na ga ba ta sanni ba, ni ma ban san ta ba, wurina ta zo? Idan biki ta zo ai gidan Hakimi za ta wurin Aunty Hauwa ba wurina ba.”

Tun da ta fara maganar yake kallon ta, sai da ta kai karshe ne ya ce”To wanda ya zo wurin Aunty Hauwa ai wurinki ya zo?”

“In ji wa? Wurin Aunty Hauwa dai ya zo. Me ye kuma hadin bakon Aunty Hauwa da ni? Ita kanta Aunty Hauwar me muka hada da ya iyayenmu daya.”

Ya kasa janye idanunsa a kanta, kafin ya ce,

“Please keep jokes aside. Bai kamata ki yi mata haka ba.”

“Ka ga! Ni fa ban tura mata da wasika ta zo ba, don haka ta yi harkarta ni ma in yi tawa yauwa. Shi ya sa ma da na zo na sauka gidan ubana, ban san takura. Sai ku yi ta damuna da wata mata can wai dole sai mun yi magana ne, da ban mata maganar ba me ye same ta. Ni fa gaskiya an dame ni. “

Fitowa ya yi daga dakin, ya samu Blessing kwance a kan kujera, karya ya yi mata da cewa Fatiman kanta ke ciwo, shi ya raka Blessing dakin Inna da suka gyara ya yi mata sai da safe bayan ya kwaso kayan cin bikin da ya dinko musu.

Kan gadon ya zube su, yana daga su daya bayan daya yana nunawa Fatima, lace ne blue black mai kananan hudoji, anko ne ita da Hana da kuma Blessing, sai shadda golden color, su dukkansu harda Ummi, akwai takalma da gyale masu kyau kalar ƴan gayu.

Ta yi masa godiya sosai hade da nuna jin dadinta abin da bai yi tsammani ba, ya dauka yadda take cika tana batsewar nan, shi da kayan ma basu ishe ta kallo ba.

Yanzu ma duk yadda ta rika rokonshi a kan ya kyale ta, bai ji rokon ba haka ta kwana fushi, shi ya sa karfe takwas na safe tabar gidan, ita dai a kayan da Mustapha ya siya mata ko dankunne ba ta dauka ba, ta dai dauki nasu Hana da Ziyad, sai kuma nasu Hassan.

Lokacin da Blessing ta zo su gaisa sai Mustapha kawai ta samu yana bacci.

Ba ta ji dadin abun ba, ya kamata sun kwana gida su gaisa, sannan ta sanar mata za ta fita.

Amma za ta yi mata uzuri har yanzu Fatiman yarinya ce don Blessing ta ba ta kyawawan shekaru a kalla biyar.

Ita ta gyare gidan tsab, sannan ta hada musu abun kari.

Fatima kam ana can an shiga hidimar daurin aure, shagali ake yi sosai, shi ya sa ya mantar da ita duk wani haushi da kishin Blessing da take ji a ranta.

Bayan an sakko masallaci juma’a aka daura auran Zainab, wanda ya samu halartar manya mutane daga waje da cikin Kasar nan, wannan ya kara tabbatarwa da Blessing Fatima suna da karfi sosai a garin.

Ba a bata lokaci misalin karfe uku anguna suka fara kwashe amarya da kawayenta.

Fatima na cikin mota, Mama ta kifo zane ta fito zuwa wurin motocin, tana lekawa daya bayan daya, har ko ta yi katari da motar da Fatiman take ciki.

“Ke! Fito a cikin motar nan.”

Mama ta yi maganar cikin bada umarni.

Cike da mamaki Fatima ta tambaya “In fito kuma, ikon Allah.”

“Eh. Fito na ce.”

Haka Fatima ta fito bayan ta bata rai.

Maman ta dora “Mu je gida tun da ke ba ki da hankali, mijin naki ya zo sai ki kama hanya ki tafi ki bar shi da wata. Ke ko kishi ma ba kya yi?”

“Kishi kuma?”

“eh shi.”

“Yanzu Mama don wannan ne za ki hana ni tafiya?”

“To bai isa dalilin a hana ki tafiyar ba.”

“Aiko to wlh jibi zan yi tafiya ta.”

“Ki tafi ma gobe, amma yau kam ba za ki je wannan Katsinar ba.”

Rai bace Fatima ta aje kujera ta zauna a tsakar gidan, ta so gudu ne saboda sosai tsoron ciki take ji, kuma ta ga alamar Mustapha abin da yake so kenan, don ta yi mishi complain din cewa lokacin da yake karatu, ta ba shi dukkan support, me zai sa ita ba zai yi hakan ba.

Sai cewa ya yi wai ciki nawa ya yi mata lokacin da yake karatun, har ƴan biyu ya bata.

Ta ja siririn tsoki a bayyane, lokaci daya kuma tana kallon Blessing da ta shigo hannunta rike da na Ziyad, shar suke cikin ankon shaddar da Mustapha ya yi musu, ba karya Blessing ta iya kwalliya, ai wayewa ma ba daya ba.

Sai da ta gaishe da mutanen gidan, sannan ta ja tabarmar da ke kusa da Fatima ta zauna, a zuciya Fatima ke cewa “Allah ya hada ni da ƴar jaraba, wannan bakin naci sai ka ce talauci haba.”

“Dazu na shiga, sai na ga har kin fita.”

“Eh. Na san ba ki tashi ba, shi ya sa ban shiga ba.”

Sai Blessing ta dan ji dadi kadan, duk kuwa da Fatiman karya ta shirga mata, don ko ta kanta ba ta bi ba.

“To Allah Ya sanya alkairi an daura aure.”

“Amin.” Fatima ta amsa hade da ture Ziyad, wanda tun da ya shigo ya yi masauki a jikinta.

“Dama na ce yau me za a yi da dare, zan je in girka, tun da na san ba yanzu za ki koma gidan ba.”

Karon farko da Fatima ta yi dariya, dariyar da ita kanta ba ta san dalilin yin ta ba, amma kawai tana kallon karfin halin Blessing din ne, na son shiga sabgarta.

Cikin siririyar dariya ta ce” ku girka komai, ni ba ma lallai in dawo gidan ba. “

Cike da mamaki Blessing ke kallonta, duk Hausawa ne haka basu wani damu da lamarin miji ba, kodai Fatiman ce haka, tana mamakin irin son da Mustapha ke yi mata, bayan ita ko a jikinta, ko da wane makami ta yi amfani wajen rike zuciyarsa oho, tun da suka iso ko sau daya bai ci abincin Fatiman ba, kamar yadda ba ta ga inda ta jefe shi da wani murmushi mai nuna alamar soyayya ba.

Ko magana ma sai ta ga dama take yin ta, amma sonta yake yi sosai. Su Hausawa Allah ya yi musu wannan baiwar. mazajensu na kokarin wajen ganin basu yi kukan komai ba. Abun mamaki wai yanzu ma ba lallai ta kwana a gidan ba.

“To a ina za ta kwana?” ta tambayi kanta.

Saboda ta ji ƴan’awanta na tsegumin Mama ta hana ta tafiya Katsina.

A daidai lokacin Jamil ya shigo, da hannu ya yi mata alamar ta zo.

“Ina zuwa.” Fatima ta fadawa Blessing lokacin da take mikewa ta bi bayan shi.

Bangaren Alhaji suka shiga, kan plastic chair suka zauna suna fuskantar juna.

“Muna fada ne har yanzu?” ya fara tambayarta

Sai da sautin dariyarta ya dan fita, kafin ta girgiza kai, alamar a’a.

“Atoh!” ya fada sannan ya dora da “Yanzu mun girma ai.”

Wannan karon ma murmushi ta yi.

“Ya school?”

“Alhamdulillahi” sai yanzu ta bude baki ta yi magana.

“Hope babu wata matsala?”

Kan ta kuma girzawa tare da fadin “Alhamdulillahi ba komai gaskiya.”

“Kenan kina jin dadin karatun?”

Kai ta gyaɗa alamar eh.

“Na yi farin ciki sosai da jin kin koma makaranta, shi karatu ba a tsufa da shi idan ka sanya kanka za ka yi, kawai za ka yi.”

Kai ta shiga jinjinawa alamar gamsuwa.

“And Fatima I’m your brother, and I love you as my sister, ban taba kin ki ba, don Allah ki dauke ni dan’uwa kuma abokin shawara da za ki iya tattauna komai da shi”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Ni ma ban taba kinka ba Ya Jamil, wlh ina sonka tamkar dai yadda nake son su Ya Bashir. Abubuwan da suka faru a baya kuma don Allah ka yi hak’uri. Sannan ina matukar godiya da dukkan taimakonka gare ni. Allah Ya saka ma da mafificin alkairi.

Ya zuba mata ido cike da mamakin maganganunta, kullum kara hankali take yi da nutsuwa.

“No stop thanking me, you deserve more than that, you’re my little sister.”

“An ce kin bude account?” ya katse dan shirun da ya ratsa tsakaninsu.

“Eh.” ta amsa hade da jijjiga kai.

“Rubuta mun” ya yi maganar hade da mika mata wayarsa.

Sun jima suna tattauna maganganu wacce ke kara musu fahimtar juna, har sai da aka leko kiran Fatima wai ƴan biyunta na kuka.

Sannan ta bar wurin tare da alkawarin sha Allah za ta rika sanar da shi duk abin da ya kamata ya sani.

Kuma shi ma ya yi mata alkawarin biyan kudin registration din ta har ta gama.

Matar J✍🏻

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 42Daga Karshe 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×