Skip to content
Part 45 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Take wuta ta dauke mata, yayin da wani kunci ya ziyarci zuciyarta. Ta zubawa strip din ido kamar wacce ke jiran ganin canji.

Can kuma ta ce “Ciki! Allah ka san abin da ke zuciyata, wani yana nema bai samu ba, ni kuma ka ba ni, amma a wannan lokacin Ya Allah ina bukatar hutu.” kamar mai koyon tafiya ta ja kafafunta zuwa kan katifa ta fadi yarab, hawaye masu dumi suka biyo bayan faduwar tata.

Tsawon mintuna talatin tana kukan, kafin daga bisani ta janyo wayarta, ta rubuta “Ciki gare ni, kuma ni cirewa zan yi.” ta tura sakon tare da yadda wayar kan katifa ta ci gaba da sharce wasu sabbin hawayen, “Ciki fa!” ta kuma fada a zahiri, sannan ta dora da “Cire shi zan yi, yaushe na gama da wahalar su Husaini, ban ko huta ba ace kuma ga ciki”

Karar wayarta ne ta katse mata maganar, ganin Mustapha ne sai ta ƙi dagawa, don ta san tatsuniyar gizo dai ba za ta wuce koki ba, kiran na yankewa sakonshi ya shigo “Kar ki cire cikin nan, rayuka zasu baci”

Ta zubawa sakon ido, kamar wacce ba ta gane me ya rubuta ba, kafin ta tantance ta gane ko ba ta gane ba, wani kiran ya kuma shigowa. Haka yay ta jera mata kira ba ta dagawa tare da text din gargadin kar ta cire mishi ciki.

Wayar ta kashe hade da kwantawa sosai kan katifar ta shiga sakawa da kwancewa, tana kallon kalubalen da ke gabanta idan ta bar cikin nan, a lissafinta haihuwar za ta iya kamawa a 200level first semester karshe, kenan ko ta gama exam ko tana cikin yi ko ba ta fara ba, duk a ciki bayan ta gama exam din ne kacal mai sauki, amma sauran duk akwai challenge.

Ta tuna wannan ta tuna wancan har baccin da ba ta yi niyya ba ya dauke ta.

A cikin baccin ta rika jin buga kofa, ido cike da bacci ta nufi kofar tana fadin “Waye?”

Jin muryar Aunty Lami da sauri ta bude, fuska dauke da mamakin ganin ta ta ce “Aunty lafiya?”

Harara ta fara dallara mata sannan ta wuce ta zuwa cikin dakin hade da zama kan katifa.

Fatima ta karaso har yanzu da mamaki a kan fuskarta ta kuma cewa “Aunty lafiya dai ko?”

“Ban sani ba”

“To!” Fatima ta ce hannu a kan haɓa tana kallon Aunty Lamin.

“Mustapha ya ce kin ce za ki cire ciki?” kai tsaye Aunty Lamin ta yi tambayar.

Ita ma kai tsaye ta ce “Eh.”

“saboda ba ki da hankali?”

Sai a lokacin Fatima ta nemi wurin zama tana fadin “Aunty duka yaushe na yaye ƴan biyu, yanzun kuma ciki, kuma kin san irin wahalar da na sha lokacin da na hada karatu tare da rainon yaran nan. Yanzu kuma in raini ciki sannan in koma rainon yaro ko yarinya fisabilillahi Aunty, ko tausayina ba kwa ji.”

Aunty Lami ta sassauta murya” To me ya sa tun farko ba ki dauki matakin hana shigar cikin ba?”

” Dama niyyata ina yaye su Hassan in yi planning. “

” To yanzu dai tun da wannan ya shiga ki yi hak’uri a kiyaye gaba. Mustapha ya hau sama sosai, ya ce zai fara daukar mataki a kan abubuwan da kike mishi. “

” To ni me nake yi mishi Aunty? idan ni ban yi korafi a kansa ba, bai kamata shi ya yi a kaina ba ai.”

” To ya ce a komai ba ba kya shawara da shi sai dai ya ga kina yi”

Tabe baki Fatima ta yi kafin ta ce “Maza kenan. Haka ya ce?

“To zan yi mishi karya ne?”

“a’a.” Fatima ta fada da sauri

” To kar dai ki sake ki cire cikin nan don Allah, don sosai ya dauki zahi, shi ne ma ya taso ni cikin ranar nan, irin yadda ya damu tamkar kin hwada mishi kin sha maganin cire cikin, kina jiran hitar cikin ne.”

“Hmmm!” Fatima ta kuma cewa lokacin da take gyara zamanta.
I
“Aunty a cikinsu ni ce abun tausayi fa, ƴar kauye ba kowan kowa ba, mai matakin secondary ilmin addinin ma ban yi nisa ba. Mustapha ya sauke, yana da haddar kusan hizif arba’in a kansa. Ga sauran littafan addini a kansa, yana da matakin digiri yana aiki kuma.

Matarshi yar gayu tashin cikin gari rainon gidan masu kudi, mai matakin digiri tana aiki. Wace kashin bayansu ba ni ba? In ta haifa mishi yara shi ne nawa aikin?”

” A’ ah! To wannan kam wa ya ja, ina ke ce, da tun hwarko kin yi karatunki, wa ya isa ya nuna miki yatsa yanzu?”

“To yanzu ba ga shi ina son gyara kuskurena ba Aunty. Tsakani ga Allah a zo a makala min wani ciki kuma.
Shi fa digiri na biyu ma zai wuce, ita kanta matar tashi wani karatun take yi a bangaren addini ni da da mai ido ce dai yar banzar su. “

“To wannan dai duk bai zama hujjar cire ciki ba, abin da Allah Ya sa za ka, zama za ka zama, ko min dadewa kuwa. Ke dai kar ki sare.”

“Dole in sare Aunty. Ya Mustapha ne ya kamata ya karfafa min gwiwa amma Sam bai taba yin hakan ba.”

Kafin Aunty Lami ta yi magana wayarta da ke cikin jaka ta yi 1 kara, ta lalubo ta tana fadin” Kin ga Mustaphan ne ma ke kira. “

Da yake a speaker Auntyn ta sa wayar Fatima na jin yadda Mustapha yake magana hankali a tashe cike da, gargadi akan kar a zubar mishi da ciki, har da rantsuwarshi wai idan har Fatima ta zubar da cikin wlh zai yi abin da kowa ba zai ji dadi ba.

Aunty Lamin ta yanke kiran bayan ta tabbatarwa da Mustapha babu abin da zai samu cikinsa.

Murmushin takaici Fatima ta yi lokaci daya kuma ta ce “Me ye abin da zai yi? Hala ya sake ni, wlh Aunty ban da kin sa baki, da na zubar da cikin nan in ga me Mustapha zai yi, ba dai saki ba ne kawai, to sai me?”

“Don Allah kar ki jagula abu, ke ba ki san faffaka irin ta namiji ba.”

Fatima ta share hawayen da suka zubo mata, wai yau Mustapha ne ke yi mata barazana da saki kai duniya ba tabbas gaskiya.

“To me ye kuma na kuka?” ” Aunty Lami ta fada cike da tausayin ƴar’uwar tata.

Wasu hawayen suka kuma zubo mata kafin ta ce” Aunty ban son auran nan yanzu wlh. Duk ya fita a kaina. ” yadda ta karasa maganar sai jikin Aunty Lami ya kuma mutuwa.

Cikin tattausar murya Aunty Lami ta ce “Haba me ye haka, kar ki kara furta irin wannan maganar, wannan shi ne auran ai, ina za ki je? yara hudu ga ciki, kika sani ko shi ma biyun ne.”

Cike da tsokana Aunty Lami ta yi maganar

“Ba ma biyun ba ne sha Allah” cikin sauri Fatima ta fada.

Sai da Aunty Lami ta murmusa sannan ta ce “Allah dai ya kawo masu albarka.”

Fatima ba ta amsa ba, illa ta ci gaba da share ragowar hawayenta.

“Gida zan tafi, na baro yara basu dawo islamiya ba, kar su dawo ban koma ba.” ta yi maganar hade da mikewa tsaye.

Fatima ma mikewar ta yi tana fadin “Har yanzu ban samu na je gidan Zainab ba”

“A kuwa ya kamata ki je.”

“Zan je sha Allah.”

Ita ma ta amsa lokacin da suke fita waje, a tsakar gidan ne aunty Lami ta ce “Wai haka gidan naku yake kamar ba students ba? Shiru kamar ana zaman makoki. Gaskiya ba ku da ɗabi’a.”

Sai da Fatima ta murmusa sannan ta ce “Tun ban saba ba, yanzu kam na saba, sai nake jin hakan ya fi dadi, tun da dai ba fada ake yi ba.”

“Duk da haka dai ya kamata ku canja wannan tsarin, ai ba za ku aje tarihi na rayuwa awuri daya ba, kowa gum kamar masu ciwon haƙori.”

Tabe baki ta yi “Umm! Kila nan gaba, amma yanzu kam sai gaisuwa sama-sama”

“To Allah Ya kyauta.”

“Amin.” cewar Fatima.

Sai da suka karasa gate Aunty Lami ta tsaya cikin alamun gargadi ta ce “Kar ki sake ki zubar mishi da ciki Fatima, ina kara gargadinki, idan kika zubar ko me Mustapha ya yi miki ke kika ja, don ya hi ki gaskiya.”

Fatima ba ta ce uffan ba, haka Aunty Lami tai ta buge mata warning har sai da ta samu mashin.

Lokacin da ta dawo dakin alwala ta yi don gabatar da sallahr azhur.

Tana idarwa ta shiga kitchen yunwa take ji sosai, har tashin zuciya take ji.

Ruwan dahuwar indomie ta dora, sai dai kuma tana zuba indomie ta fara tafasa, ita ma ta fara amai.

Sosai ta jigata, dole ta sauke indomien ta shiga laluben abin da take son ci.

Haka ta shafe tsawon lokaci tana kawo kalolin abinci a zuciyarta, amma ba ta ji tana sha’awar komai ba.

Kuma yunwa take ji sosai. Empty tea ta sha, shi ne ya dan rike ta zuwa la’asar.

Sai da ta yi la’asar sannan ta watsa ruwa hade da sanya doguwar riga ta dora hijab.

Soson powder kawai ta goga a kan fuskarta, sannan ta shafa humra mai kamshi.

Tana kokarin rufe kofarta ne, kofar farar yarinyar nan ta bude, suka kalli juna a tare kuma suka hada baki wurin fadin “ina wuni”

Duk sai suka yi murmushi a tare.

“Are you going out side?” yarinyar ta fada lokacin da ta karaso inda Fatiman take.

“Eh. Zan dan fita ne” Fatiman ta ba ta amsa da Hausa.

“If Ba damuwa zan iya rage miki hanya ni ma zan fita ne”

“Amma ina kika yi ne?” ta yi saurin tambaya tun kafin Fatima ta amsa mata tambayarta ta farko.

“I don’t know, kawai zan fita ne, idan na samu wani abu in sawo.”

“Something like what”

“Ban sani ba fa.”

Tare suka yi murmushi, sannan ta ce “we can go, my name is Umaima”

“Ni kuma Fatima”

Kai ta jinjina lokacin ta take bude motar.

Cike da kwarewa ta haura kan titi.

Cike da sha’awa Fatima ke kallon ta, tare da fatan ita ma watarana ta gan ta a motar kanta. Tana son ta ga ta zama yar gayu, irin matan nan da basu jiran miji, komai suna wa kansu, kai me ya kai wannan dadi? Yau ki ga, kin taso hidima ba ki da fargabar ko namiji ya, sa miki hannu ko kar ya sa duk daya

“Ko yaushe ranar za ta zo?”
Ta tambayi kanta. Sai kuma ta fara kiyasto ga ta nan cikin kwalliyar tafiya wurin aiki, ta bude motorta ta yi mata key ta harba kan titi. Ga ta zaune tana karanto labaran duniya.

Sai murmushi ya kufce mata, dalilin da ya sanya Umaima fadin” Are alright? “

Kai ta jinjina alamun eh, har lokacin da murmushin a kan fuskarta.

” Ina twins, ba na kallon su yanzu? “

” Suna gida” Fatima ta ba ta amsa

“Kin yaye su?”

Kai ta daga alamar eh.

“And you’re pregnant now”

“How do you know?” cike da mamaki Fatima ta yi maganar.

“Saboda abin da nake karanta kenan” Umaima ta amsa ta cikin siririyar dariya.

Lokaci daya kuma tana shiga gidan abincin da ke gabansu.

Cike da kwarewa ta yi parking, kusan tare suka fito, tun da Allah Ya halitto Fatima yau ne rana ta farko da ta taba shiga gidan cin abinci.

Duk sai ta ji bambarakwai, ji take yi kamar idanu kowa a kanta suke.

Yayin da Umaima ke yin komai cikin kwarewa kai tsaye.

Ita kuma ji take yi kamar za a ce ta yi ba daidai ba.

Suna kan table zaune aka kawo musu abin da Umaima ta yi ticking

“I know you need this.” cewar Umaima lokacin da take tura ma Fatima plate a gaban ta

Sakwara ce ta miyar egusi, sai ganda kawai a ciki, babu wani kamshi sinadarin girki a miyar dangin su curry ko thyme.

Yadda ta ga Umaima tana cin shinkafa fried rice kanta tsaye Kamar tana a daki ita kadai sai abun ya ba ta mamaki.

Ita duk da ta ji tana son cin Sakwarar amma ta kasa, duk inda ta juya sai ta ga kamar ita kowa ke kallo.

Ganin tana neman yin kauyanci ne ya sa ta dan yagi Sakwarar kadan, ba don ta koshi ba ta ajiye, kafin ta dauki coke mai sanyi ta sha, sai ta ji duk wani bacin rai babu sosai, zuciyarta ta yi wasai, musamman yadda take ganin kowa yana walwalarshi, tamkar dai sun gama da matsololinsu.

Umaima ce ta kira ma’aikatan wurin suka kwashe plates din, bayan ta tambayi Fatima ta koshi. Sannan kuma ta ce a yo take away din wani abu guda biyu, wanda Fatima ba ta san me ye ba, a sunan dai ta ji an kira fish.

Tana zaune aka kawo, kafin Umaima ta zaro kudin da suka tasarwa 5k ta biya.

Abun da ya fi ba Fatima mamaki kenan, wannan yar gullisuwar Sakwarar da ruwa, sai Coke daya , sai kuma shinkafar da Umaima ta ci da nama da hadin coslow shi ne har suka ci 5k.

“Kai na zaune bai ga gari ba” ta fada a zuciyarta.

Ita kam ba za ta iya wannan zaman karyar ba, wai danfulani ya shiga birni bai ga rumbu ba, ya ce ana zaman karya a nan.

“Zan je gidan Auntyna ne, ko za mu je?” Umaima ta tambaya lokacin da suke ficewa daga gidan abinci.

Kai ta jinjina alamar eh, don ba ta da wani zabi, haka kuwa Umaima ta rika ratsa unguwanni, har zuwa lokacin da ta shiga unguwar Dutsen safe lowcost,

A gaban wani katafaren gida ta tsaya hade da yin horn, maigadi ya bude musu gate, Umaima ta danna kan motar ciki hade da yin parking.

Fatima na shiga manyan gidaje, amma wannan gidan tsarinshi daban ne, ba ta kwari kanta ba, ta rika baza dan’uwanta lungu da sako tana kallon gidan.

Musamman da Umaima ta bar ta a tangamemen falon mai dauke da kayan alatun da wasu ma ba ta san ko menene ba ita kuma ta haye sama.
Tambayata
Ta ci gaba da wurga idanunta ko wace kusurwa tana ba ido abincinshi.

Sai da ta ji karar takunsu suna sakkowa daga stairs din da ya ratsa falon ne ta daidaita nutsuwarta.

“I’m sorry for keeping you waiting” cewar Umaima cikin murmushi. Ita ma Fatima murmushin ta mayar mata.

“Aunty meet my friend…” ta tsaya tana kallon Fatima hade da murmushi.

“Fatima M. Lawan Sandamu” cewer Fatima cikin I murmushi.

“Ehen!” Umaima ta cafe, sannan ta ce “And Momy twins meet my Goggo Dr and Halima Dikko”

Sai a lokacin Fatima ta kuma dora idon ta a kan Dr Halima, kyakkyawar mace yar gayu, kallo daya za ka yi mata ka fahimci tana da gogewa a ilimin zamani.

“Ina wuni?”Fatima ta fada hade da dan, I zamo wa.

Goggo Halima ta kara fadada murmushinta, suka gaisa cike da mutuntawa.

Amma Kafin suka ci gaba da tattaunawa da Umaima, da alama wani karin haske Umaiman ke nema a kan wata lecture da suka yi, sai ta ji sun burge ta.

Ko yaushe ne ita ma za ta fara irin wannan rayuwar? A kallo daya mutane su shaida ita din babbar mace ce, tana son ta zama yar gayu komai kwas-kwas.

Har jikin motar Goggo Halima ta rakosu, har zuwa lokacin kuwa sharhi take tayi wa Umaima a kan abin da ta tambaya.

Wannan karon Umaima gudu take, kila baya rasa nasaba da ganin magariba ta gabato, suna kuwa isa gate din gidansu ana kiran sallahr magariba.

A hanzarce Umaima ta mikawa Fatima ledar take away daya tana fadin “We talk later, it’s time for prayer now.”

Cike da godiya Fatima ta amsa, ta so ta tambaye ta nawa za ta bayar, amma ganin yadda Umaima ke sauri sai ta kyale ta, da alama tana muhimmantar da lokacin sallah.

Sai da ta yi sallahr magariba, sannan ta, warware kunshin da Umaima ta ba ta

” Raɓashe!” ta fada a bayyane, hade yago kifin kadan ta hada da Irish ta tura baki, lokaci daya kuma ta lumshe ido. Dadin ya rika ratsa sassan jikin ta.

“Gaskiya ni yar kauye ce, ban taba sanin akwai wannan ba, ikon Allah.” ta ci gaba da fada a lokacin da take cin kifin.

“Yi ina cin wannan ko sau daya ne a sati na je Sandamu waye zai gane ni.” Ta kai karshen maganar tata hade kallon jikin ta.

“To ko nawa ake siyarwa oho?”

“Dole in kara komawa wurin can.” ” ta kuma fada bayan dan shirun da ta yi.

Duk irin cin ta ba ta cinye kifin ba, shi dole ta aje shi yadda ba zai lalace ba.

Daga lokacin da suka fita zuwa yanzu ranta wasai yake, shi ya sa ma ta, janyo wayarta hade da kunnawa.

Kamar jira kiran Mustapha ya shigo.

Matar J

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 44Daga Karshe 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×